PROLOGUE (THRILLER)

63 5 2
                                    

YASMEENAH

Khadeejah Bint Ismail ( Deejasmah)

MIKIYA WRITERS ASSOCIATION ( MWA)

Wattpad @deejasmah15
Arewabooks @deejasmah
Bakandamiya @deejasmah

09042522373

PROLOUGE (THRILLER)

Rungumeta ya yi ta baya yana lumshe idanunsa da sukai masa laushi, a hankali bugun zuciyarsa ke sauyawa yana doka masa da ƙarfi kamar zata ratso tsakiyar ƙirjinsa ta fito.  Ƙamshin turaren nata; ya ƙara taimakawa wajan sakar masa da gaɓɓan jiki, wasu gasusuwa na mimmiƙewa a saman fatarshi, ya ɗan riƙota da kyau yana kusanta ta da jikinsa cike da nutsastsan yanayi na so. Shagwaɓe fuska ta yi ƙyakƙyawan murmushi shimfiɗe a fuskarta ta ce

"Good morning Noorie" “Morning" Ya amsa yana juyo da ita. A mugun tsorace ya sake ta yana mai cewa " who are you?".

Da mamakance ta kalleshi tace " Noorie!!",  jifanta da wani mugun kallon da ya sanya hanjinta hautsinewa yana mai cewa " don't call me that!, where's my wife?". Baki ta bud'e zata bashi amsa sai kuma taji harshen ya rik'e , bai bi ta kan ta ba ya  juya da mugun gudu yana k'wala kiran " Hayatii!", on top of his voice wannan wace halitta ce ta shigo masa gida da sanyin safiyar nan shin wace irin masifa ya farka ita ne?


Bayan shi ta biyo da sauri bayan ta kashe gas electric d'in dama a kai ta d'aura kasancewar ba a had'a gas d'in ba .  Mamaki k'aramin abu ne akan abunda takeji, shin me yake faru ne? ya zaayi gashi a gabanta amma kuma yana nemanta?. Turus ta tsaya ganin yanda ya fara nemanta a haukace yana yi yana kiran Sunanta kamar wani zararre a lungu da sak'on gidan sai dai babu ita.

Dawowa yayi gabanta tamkar namijin zaki yana huci mai zafi, sai kuma kamar wasa taji ya shak'eta cikin fitar hayyaci yace " where's my wifeeee? what have you done to her?".    Rik'e hannunshi tayi tana mai k'ok'arin k'watar kanta, sai dai ina ko giyar wake ta sha baa zata iya kw'acewa ba abunku da k'arfi ba d'aya ba ya shak'eta gam.


Kakari ta fara tana kallonshi da fararen idanunta da suka rine zuwa ja saboda tsabar azaba da wuya, juyawa idanuwanta suka farayi tana shirin shid'ewa sa'annan ya sake ta jifa da ita yayi kamar ya yarda kayan wanki.

Yaraf ta fad'a kan sofa tana nishi shafa wuyanta takeyi don ta tabbata yanda take farar nan sai shaidan hannunsa yai mata tambari, kallonta yayi cikin fushi yace " before I do anything stupid, where's my wife? And what have you done to her?".    Cikin muryanta da bai fita saboda shak'a don numfashinta har yanzu bai dawo dai-dai ba tace " Babeee!.......", kafar shi da yasa yai ball da ita ne ya katse maganar da take shirin yi cewa yake " where's my wife?, or do you think I'm a fool or blind da zan kasa bambance Mata ta?,,,,,now tell me where's my wife before I kill you".

Runtse idanu tayi cikeda azabar muguntar da yake mata, don k'afarshi ya d'aura a cikinta yana matsewa lumshe idanu tayi ta sadak'ar mutuwar tace tazo kuma tabbas aljanu sunyi wa mijinta mugun rik'o in ba haka ba ya zai dinga bugunta kamar ya samu jaka?.

Ta san yanada anger issues but she never know that he can be this dangerous to ko dai mahaukaci ne bata sani ba?. In ba mahaukaci ba toh tabbas yana shaye-shaye, rufe su akayi baa gaya musu ba. Don in ba mashayi ba ya za'ayi daga kawota gidan shi jiya da dare, yau ta farka da duka?. Ita kuma tata jarabawar kenan?, toh wallahi bata tsayawa Mama zata kira azo a d'auketa daga gidan wannan mahaukacin kafin ya kashe musu 'ya.

Kallonta ya tsaya yi har lokacin ka'farshi yana cikinta sai kuma kamar an tsikare shi yace " I'll call the cops right away since you don't want to talk, you'll definitely talk in the station".

Shafa aljihunshi yayi babu waya hakan yasa ya tuna da cewa wayar tana d'aki, k'ofa ya nufa yai locking tareda zare key sannan ya koma ya rufo kitchen d'in da suka baro shima ya sake locking da kyau don kar ta gudu kafin ya nufi d'akin don d'aukar waya. Tana a yashe a k'asa kumallo yana fitowa daga bakinta saboda haurin da yayi mata a cikin da bai ga abinci ba, jan jiki ta fara yi zuwa toilet d'in parlorn da k'yar ta iya tsayuwa a ciki.

Wash hand basin ta isa tana kunna ruwa, ta d'ibo ruwan zata kai fuska ne ta lura da sauyin da hannunta yayi. Da sauri ta zubar da ruwan tana jujjuya hannunta cikeda taajjubi, kallon madubin dake gabanta tayi a take ta sanya ihu tana mai rirrik'e fuskarta cikeda tsoro, damuwa, mamaki da ta'ajjubi ta furta " this ain't no me!, who is thissss?!". A take ta sulale k'asa cikin rashin k'arfi don yanzu ta yarda ko waye zai iya dukanta abunda yafi duka ma sef, don ko ita kanta tana tantamar waye a gabanta a yanzu haka shafa jikinta ta fara yi ta na fashewa da kuka cikeda damuwa tace " ya lateef what's happening to me......?!!"




Me ya sameta?.
Meye matsalar?.
Shin da gasken canja ta akayi?.
Ko dai ita ce?.

Salon na dabanne, haka ma matsalar ta dabanne I bet baku tab'a jin salo irin wannan ba ku biyoni muje zuwa kar ku yarda a baku labariiiii......

#like
#vote
#share
#comment
#follow

Deejasmah✍🦋❤

YASMEENAHWhere stories live. Discover now