YASMEENAH
Khadeejah Bint Ismail ( Deejasmah)
Mikiya Writers Association ( MWA)
Dedicated to Asma'u Abubakar Musa ( Jasmine)
With love to Radeeyah Ismail ( Uomm Ajmal)
09042522373
TOP TEN
CHAPTER 8
YASMEENAH
Asabar da misalin 11am dubban al'umma suka shaida d'aurin auren Asma'u Abubakar Hunkuyi da angonta Sarham Ali Yakub akan sadaki mafi albarka. D'aurin aure ne da ya samu halattar manyan mutane kama daga hasfosin sojoji, y'an sanda, y'an kasuwa da k'usoshin gwamnati kasancewar Alhj Ali Yakub Marafa shi ne tsohon controllern custom dukda ya rasu yana da alfarma a k'asar balle kuma yanzu da Sarham d'in kan shi babban jami'i ne.
Sanda aka d'aura auren suna zaune a gidan mak'wafciyar su Uomm Amrah, inda take sanye cikin bridal gown seam foam color na wani tsadadden material. Ya zauna a jikin ta tsaf kamar a jikinta aka d'inka shi, wai a hakan ma an bud'e kenan amma har yanzu dai ya kamata though not that wanda zai yi ba kyan nan.
Makeup d'in da akai mata yau yafi na jiya kyau ga yanayin d'aurin da ya dace da kwalliyan, sai tayi using silver costumes masu ado da diamond a ciki. Tayi kyau ainun kamar ka saceta ka gudu, gefenta friends ne sai videos suke yi.
Dai-dai lokacin wayarta yayi ringing Zuu dake gefenta ta kalli wayar ta sanya gud'a, nan hankalin y'anmatan ya dawo kanta nan suka maida wayoyin su kanta suna mata wak'ar " an d'aura an d'aura ta zama matar Sarham Allah tagode ma". Zuu tace " Aah matar Noorie dai". Ai ko suka juya wak'ar suka koma cewa matar Noorien, ita dai murmushi kawai take yi tana lumshe idonta yayinda wayar yaci gaba da ringing don mai kiran bai tsagaita ba.
D'an rausayar da idanun tayi tana kallonsu, tana son ta d'aga wayar amma hayaniyarsu tayi yawa. Tsam ta mik'e ta nufi hanyar shiga bedroom d'in su Amrahn da take cikin masu yi mata tsiyar. Biyota sukayi a baya aiko tana shiga ta rufe don ta gane mai suke shirin yi, so suke su d'auketa tana waya da shi ita ko ba da ita zaai wannan trend d'in ba.
Zama tayi a bakin gado tana shirin kiranshi sai gashi ya kirawo ta, kara wayar tayi a kunneta tana shirin yin sallama yace " it's official,,,,you are mine" cikin wata kasalalliyar murya yayi maganar. Sai da tsigar jikinta ta mik'e jin yanda yayi maganar ta kasa cewa komai sai lumshe idanu tayi, sake cewa yayi " my very own!!!" A hankali tace " uhmmm!".
Ajiyar zuciya ya sauke yana cewa " zama ki bud'e baki ne yarinya, kina ina?". Cewa tayi " neighbor kai fa?" Lumshe idanun shi yayi yana kallon Jaheed da ya saki tuk'in da yake yi ya zura masa idanu, yace " daga wurin d'aurin aure and I'm coming right away to see you". Sassauta murya yayi yace " I want to come and hug you baby, na dad'e ina burin haka I wanna feel you in my body".
Rufe idanu tayi tana cewa " kai Noorie". Murmushi yayi he can imagine her doing so yace " ba wani kai, ai yanzu ke mallakina ce so I'm definitely doing that just get ready I love you Mrs. SA Yakub Marafa" . Daga haka ya katse kiran, lumshe idanu tayi taji sunan har k'asan ranta and she loves yanda yake yawan katse kira a lokutan da ya furta mata kalmar so it's more romantic than anything.
Bud'e d'akin tayi tuno yace yana hanya, tana fitowa sukayo mata caa akai. Ita dai bata tanka ba sai waje da ta samu ta zauna tana mai wasa da wayarta.
Sanda suka iso k'ofar gidan a cike yake da motocin y'an uwan Baba da suka dawo daga d'aurin aure suka yo nan, kallonshi Jaheed yayi yana cewa " uban y'an zumud'i kabi ka matsa muzo kalli yanda gidan yake cikeda jamaa haka zamu shiga?". Cewa yayi " har ma mun shiga mun fito malam, bari ma ka gani".
YOU ARE READING
YASMEENAH
FantascienzaYASMEENAH Da mamakance nake kallon kaina, ni ce amma bani bace! Bani bace wacce ke tsaye a gabana. Toh wacece ni ina kuma na tafi?, tambayoyi ne da ban da amsarsu don ko zaa shaƙe ni ba zan iya amsawa ba. A dai-dai lokacin bugun ƙofar shi ya tsanant...