YASMEENAH
Khadeejah Bint Ismail ( Deejasmah)
Mikiya Writers Association ( MWA)
Dedicated to Asma'u Abubakar Musa ( Jasmine)
With love to Radeeyah Ismail ( Uomm Ajmal)
09042522373
TOP TEN
CHAPTER 10
Look who is back🌚
Na san kunyi kewata ni ma haka amma ba da son raina ba ne dole ce ta sanya amma kowani second masoya Yasmeenah suna raina burina in kammala jarabawa in dawo gareku, toh gamu mun dawo kuma in shaa Allah zamu d'aura daga inda muka tsaya wannan Karon babu tsaye-tsaye in samu in kammala don mutanen Nisfu suna buk'ata ta ainun.
Na ga adduoinku kuma tabbas na gode Allah ya saka da khairan ya sa mu ga alkhairi baki d'aya.
Moh Sabeer, Aysha Alkaseem and Meenah this chapter is wholely yours, thanks for the love and care Yasmeenah tana gaisuwa daga ohishin kwalawa😂.
Da sauri ya mik'e don all this while sai yanzu Zeem ya fad'o masa a rai bai kuma san me yasa ba, ACP ne ya dube shi yana cewa " kar ka damu, mu da kanmu zamu nemo shi har da ma ita matar taka in shaa Allah". A d'an hasale yace " har zuwa yaushe kenan officer?, Nazeem is really dangerous I have no idea what he can do to my wife ".
"Bai isa ya tsere ba no matter how cunning and naive he's, da kaina zanyi leading operation d'in I assure you that it'll in shaa Allah yeild a positive result".
Har zai bud'e baki yayi magana Baba ya tare da cewa " ka kwantar da hankalinka tunda har shi ya amsa ragamar aikin toh mu basu dama su yi k'ok'arinsu".
"Yes man!" Toh kawai ya iya furtawa, su kayi sallama da IM Mahdi suka nufi waje. Sun dad'e suna zantawa da sake jajantawa juna kafin su rabu da Baba kowa ya kama hanyarsa.
Bai da k'warin jikin da zai iya driving ko d'aya haka ya sa ya shiga motar Jaheed ya lafe yana mai kishingid'a a motar yana jin zazzab'i na shirin rufe shi. Kallonshi yayi yana shirin magana wayarshi tayi ringing.
"Wai Sarham barci ka sake komawa ne bayan ka san jiranku akeyi ne?" Shi ne tambayar da ta watso masa a dai-dai sanda ya d'aga wayar, ajiyar zuciya ya sauke yana cewa " A'a Mamie yanzu haka ma ba ma gidan".
"Kuna hanya?"
"Muna police station matsala ce gagaruma ta tunkaro mu".
"Innalillahi wace kalar matsala kuma ni Fatima?". Ta tambaya da bayyanannen tashen hankali a harshenta, sama-sama ya shaida mata abinda ya faru. A rikice ta sanya salati tana cewa " tabbas muna cikin jarabawa amma ba abinda yafi k'arfin addua yanzu ya ake ciki?".
Ta buk'ata, duk da cewa yanzu ya gama mata hakan bai sa ya gaji ba sabon bayani yayi mata yana jin kamar ya had'iye rai ya mutu kawai. A hankali tace " Allah ya bayyana ta yanzu kai ina zaka?".
"Muna tare da Jaheed zan tsaya wurinsa kawai".
"Yawwa bashi wayar" bai iya amsawa ba sai umarnin da ta bayar ya aiwatar, bai san mai suka tattauna ba don shi Jaheed d'in da toh yake ta amsawa.
Daga haka yaja motar zuwa gidansu don can Sardaunan police sun rufe saboda yana under investigation ne hakan yasa aka zagaye wurin har mai gadi an tafi dashi .
Koda suka shiga samun wuri yayi kawai ya zauna yana tunanin abinda ya faru kamar almara ko mafarki, har d'aci-d'aci yake ji a mak'ogwaronsa na damuwa in da yana da saurin kuka da sai yayi mai'shi ko zai samu sukuni amma sai na zuci da yake yi yana jin zubar hawayen kamar zubar ruwan dalma a zuciyarsa hakan yasa idanuwanshi suka kad'a sukayi jazur ba kyan gani.
YOU ARE READING
YASMEENAH
Science FictionYASMEENAH Da mamakance nake kallon kaina, ni ce amma bani bace! Bani bace wacce ke tsaye a gabana. Toh wacece ni ina kuma na tafi?, tambayoyi ne da ban da amsarsu don ko zaa shaƙe ni ba zan iya amsawa ba. A dai-dai lokacin bugun ƙofar shi ya tsanant...