CHAPTER 9

8 1 0
                                    

YASMEENAH

Khadeejah Bint Ismail ( Deejasmah)

Mikiya Writers Association ( MWA)

Dedicated to Asma'u Abubakar Musa ( Jasmine)

With love to Radeeyah Ismail ( Uomm Ajmal)

09042522373

TOP TEN

CHAPTER 9

Jiya nace zanyi update sai kuma rashin charge ya hanani typing sai yau na samu dama, fatan za a yi min ahuwa😩?

Ummu Abulgais wannan shafin naki ne ke d'aya k'wallin k'wal saboda soyayyarki ga Yasmeenah❤🥀. Allah ya raya Abulgais bisa tafarki ya bar soyayya a tsakaninki da Abbanshi😌. Deejasmah tana godiya rabbi ya bar zumunci.

Tsaye tayi kanta a k'asa tana kallon k'afafunta da sauyin da sukayi, ba wai kumbura sukayi ba a'a girma suka sauya da tudu sai dai babu tsawo. D'ago kanta ta sakeyi tana kallon mirror, komai na fuskarta ya canja. Hancinta da yake siriri madaidaici a tsayi ne yayi wani irin girma da tudu, har ya ninka nata sau biyar ko fi. Haka lips d'in ta that is not thin nor thick but it is full and luscious, shima yayi girma sosai ya kumbura. Sai idanunta da suka rage girma da ma ba girman arziki suke da shi ba, gaban goshinta kuma wrinkles ne ya bayyana ga wasu mula-mulan k'uraje da suka mamaye fuskar sai kumatu cus kamar an cusa fulawa. Hannunta shima ba kumbura bane amma muscles d'in ne suka k'ara girma, tundaga tafi har zuwa wuyan hannun. Hijabin ta cire don zafin da wuyanta yake mata ya nuna ba k'aramar shak'a yayi mata ba, da sauri ta runtse idanu don mak'ok'o ne mai matuk'ar girma da fad'i ya mamaye duka wuyanta hakan kuma ya taimaka wurin sake kumbura fuskarta. Ta saman k'irjinta ma wani nama ne ya taso a dai-dai wurin k'ashin wuyarta " ya salaam!!!".

Mamaki takeyi da alajabin sauyin da tayi a dare d'aya, abune da yafi kama da almara ko tatsuniya irin wanda bata tab'a jinsu ba a duniya yayinda gefe guda take mamakin rashin lura da sauyin sai yanzu. A dai-dai lokacin ne aka sake buga k'ofar toilet d'in cikin wata authoritative voice aka ce " open this door, right now!!". A razane ta kalli k'ofar ta tabbatar police ne, maida hijabinta tayi ta murd'a k'ofar.

Fita tayi ta tsaya tana k'are musu kallo suma ita suke kallo cikeda tsoro don basu tab'a ganin mutum mai kama da ita ba, officern dake wajen ne ya kalli matan yana cewa " ku sa mata handcuffs". Helplessly ta mik'a hannayenta, sark'afa mata sukayi suka ja ta zuwa waje. Kallonshi yayi yana cewa " don't worry yourself sir, we'll do everything in our power to bring back your wife yanzu zaka biyo mu station don d'aukar statement d'inku".

Bai ko iya amsawa ba ya rakosu a baya yana jin bugun zuciyarshi na tsananta, damuwa da k'unci suna ziyartarshi ga kuma fargaba. Ta ina zai fara sanar da iyayenta da b'acewarta? ba ma wannan ba ina take a halin yanzu me ya fitar da ita kuma wani hali take? Ita kuma wannan halittar wacece?. Tambayoyine da bai da amsar su, hakan yasa yayi kasak'e yana bin bayansu a motarshi da mugun gudu kamar zai tashi sama. Hakan ne ma ya sa ya wucesu, don su ba gudu suke sosai ba kun san tafiyar motar y'an sanda musamman in non-emergency situations.

Kusan tare suka isa office d'in da Jaheed da ya fito a firgice don bai san me ya sanya shi cewa su had'u a station ba, yanda ya ganshi ba k'aramin tsorata shi yayi ba rungumeshi yayi k'am yana sauke ajiyar rai kamar yayi gudu. Zareshi daga jikinshi yayi cikin damuwa don bai tab'a ganinshi a kwatankwacin yanayin nan ba, cewa yayi " me yake faruwa Dude?". Kasa magana yayi sai ajiyan zuciya da yake saukewa akai-akai, dafa kafad'arshi yayi yana cewa " kabi komai a sannu guy, amma me ya fito da kai yau da sanyin safiyar nan daga gida ka bar Meenahn?".

Sai yanzu ya iya magana cikin hard'ewar harshe " ban san inda take ba, I just woke up today and she's nowhere to be found!!". Da sauri ya sakeshi yana mai zare idanu a mamakance yace " ban gane nowhere to be found ba, ina taje allurace da zata b'ace ko me?". A hankali yace " I left her in her room da naje masallaci na dawo na tarda room d'in locked, so sai na wuce room d'ina nayi bacci a can tashin da nayi ne na ga wata bak'uwar halitta a kitchen pretending to be her".

YASMEENAHWhere stories live. Discover now