CHAPTER 11

7 1 0
                                    

YASMEENAH

Khadeejah Bint Ismail ( Deejasmah)

Mikiya Writers Association ( MWA)

Dedicated to Asma'u Abubakar Musa ( Jasmine)

With love to Radeeyah Ismail ( Uomm Ajmal)

09042522373

TOP TEN

CHAPTER 11

Jama'ar annabi ya mukaji da gajiyar biki, toh duka dai Allah ya sanya alkhairi ya bada zaman lafiya, ya had'a kawunansu ya dawwamar dasu cikin soyayya da aminci matabbaci.

This chapter is wholely dedicated to Aunty Salmah ( Mom Afnan) your love for this book is absolutely great, I know that a chapter won't describe how much you mean in the course of writing this book but know that I also gift it out of love enjoy and be safe😍❤.

Tsawon kwana 5 babu wanda ya lek'o ko yazo inda suke, both ita da Nazeem sun galabaita sun fita kamanninsu musamman ma shi da ba lafiya ya cika ba. 'Yan gidansu basu samu zuwa ba saboda rashin sanin station d'in da aka kai shi, duk sun zagaye na kusa sai dai babu wani bayani.

Mamani ce ta kawo shawarar suje gidan Alhaji Abubakar ( Baba) a da kamar kar ya je sai kuma da ta isheshi da mita ga damuwa ya sa yaje, sanda.yaje bayanan yana kasuwa sallahu ya bada ya koma.


10 pm ya sake dawowa gaisawa sukayi da Baba cikin mutunci, don dukansu sun san juna a unguwa kawai dai ba za a ce akwai kusanci a tsakaninsu ba kawai dai in an had'u ayi sallama.

Nan Babudin ya shaidawa Baba abinda yake tafe dashi kan batun Nazeem, shi ma Baban a take ya bashi labarin da ya sani sun farkon fara soyayyarsu da Meenah har zuwa yau da kwana uku kenan da b'acewarta jikinshi yayi sanyi don ko shi ne shi zai kama. Sai dai ya san waye Nazeem ciki da bai kurarin banza ne da kafiya ba wai don yace in ta kuskura ta auri wani zai kasheta ba yake nufin zai iya d'in ba, Allah ya kyauta kawai ya iya furtawa tareda tambayarshi ko zai iya ganinshi nan Baba yace sai dai gobe da safe tunda shi ma zai koma kan case d'in shi da Tamam kasancewar Sarham jikinshi sai sake rikicewa yake though yau da sauk'i adduar Allah ya bashi lafiya yayi sukayi sallama kowa ya shige gida.

Ko da ya koma ya labartawa Mamani abinda ya faru tab'e baki tayi tana cewa " in shaa Allahu ai ba zasu ganta ba, yanda ta wahal min da d'a itama ta wahala shegu dangin tsiya". Tsayawa yayi yana mai kallonta ya lura fa ita ba abinda zai sa ta saduda, girgiza kanshi kawai yayi yana wucewa d'aki.

Gidan Baba ma basu da natsuwa daga yaran har manya, a da basu sanar da Tamam ba sai dai ganin damuwar tana dad'uwa ba kuma alamun bayyanarta ya sanya da kanshi ya kira ya sanar masa. A ranar ko ya tattaro komatsanshi ya baro Lagos dama clearing kaya yaje yi, a ranar da ya dawo ne Babudi yazo hakan ya sa suka shirya washe gari zasu koma su sake jin yanda ake ciki duk da ACP IM Mahdi yana updating d'insu akai.

Bangaren Sarham kuwa damuwa ce tayi masa yawa inda dole ta sanya likitoci sedating d'in shi, don maganarshi a barshi ya fita neman Yasmeenah. Ta gefe guda kuma Jaheed yana ta fad'i tashi daga hospital zuwa station har external investigators ya sanya amma magana d'aya ita ce ba wanda ya ga san da aka fitar da Yasmeenah daga gidan, a take zuciyarshi ta fara masa rawa akan ko dai da gaske take yi to in itace me ya sameta ne har haka?.

Bai dai yi maganar da kowa ba har yau da jikin Sarham d'in yayi kyau, hakan ya sa likitoci suka sallamesu bayan an gargad'e su akan duk abinda zai d'aga masa hankali. Shi ko dama lambo yayi don ya gaji da alluran da suke ta tsikara masa ba gaira ba sabar, ga damuwar Yasmeenah da har a halin gushewar tunani bai kau daga kanshi ba ko na second guda ne.

Suna dawowa washe gari da sassafe shi da Jaheed suka nufi station, direct Zeem ya buk'aci gani aka bashi mintoci kad'an. A waiting room ya tsaya yana jiran isowarsu, after like 2 minutes sai gashi nan an kawo shi sanye da singlet da wando bak'i duk yayi biji-biji duk da basu dukeshi ba.

YASMEENAHWhere stories live. Discover now