YASMEENAH
Khadeejah Bint Ismail ( Deejasmah)
Mikiya Writers Association ( MWA)
Dedicated to Asma'u Abubakar Musa ( Jasmine)
With love to Radeeyah Ismail ( Uomm Ajmal)
Wattpad @deejasmah15
Arewabooks @deejasmah
Bakandamiya @deejasmah09042522373
TOP TEN ✍
CHAPTER TWO
Da idanuwa ta rakata tana mai mamakin halayyar y'aruwarta kamar wata mai juju, kuna zaman lafiya zata juye tayi ta bala'i wani lokacin kuma bata son ko kusa a rab'eta. Duk k'wak'war ka baka isa sanin me take ciki ba, inda sabo ai ta saba da ganin wainnan abubuwan. Amma kuma har yanzu ta kasa sabawa don baa haka take ba, and bata da wadda ta fita a duniya duk ko da tarin k'awayen da take da su. Ajiyar zuciya ta sauke jin ana kiran sallah, tashi tayi zaune ta na mai kallon k'ofar.
Tada sallah a masallaci yayi dai-dai da fitowar ta daga toilet, bata tanka mata ba haka itama bayin da ta fito itama ta shiga. Tsarki tayi ta chanja pad d'in jikinta kafin ta d'auro alwala ta fito, dadduma ta shimfid'a ta sanya hijabinta gabas ta fuskanta tana zama cikeda nutsuwa carbi take ja. ( Yake 'yaruwata a irin lokutan da baki da tsarki baki da halin ibada, ba zama zakiyi da najasa ba a duk lokutan sallah ki dinga k'ok'arta yin tsarki da alwala ki zauna a dadduma kina azkaran da zaki iya- tsari ne sosai ga dukkan abin k'i. Ba wai ki zauna kina hira ko chatting mara amfani ba Alwala kanta kariya ce mai k'arfi ga d'umbin lada Allah ya sa mu dace).
Tana zaune a wurin har aka kira isha'i, sai da aka idar ne tayi adduointa ta shafa kafin ta tashi maida komai wajen shi tayi. Tana shirin fita sai ga kira ya shigo wayarta, d'auka tayi duk da bak'uwar number ne tafi bada Sarham ne ya kira. Karawa tayi a kunnenta ta na mai lumshe idanu a d'an kamewar murya yace "I'm outside".
Ajiye wayar tayi tana jin bugun k'irjinta yana mai matuk'ar tsananta, dafe k'irjinta tayi tana mai karanta " laiha illa anta subhanka inni kuntu minaz zalimiin". Sai da tayi kusan k'afa 20 kafin taji d'an dama, wani hijabi ta nemo white color mai d'an tsayi don ya wuce gwuiwarta da hannayen shi. Sanyawa tayi tana sa turare kad'an da lip gloss kafin ta fito parlor.
Duka suna zaune ana ta hada-hadar cin abincin dare, d'an gaban Mama ta k'arasa tana shaida mata da tayi bak'o. A dawo lafiya tayi mata, k'ofa ta nufa cikin tafiyar da ta nuna sanyin da gwuiwowinta sukayi da harara ta rakata tana mai jan tsaki k'asa-k'asa.
A tsaye ta same shi yana jingine da gate d'in, kan shi da yake sakaye da face cap bak'a a sunkuye take. Maana yana mai kallon k'asa, cikin sassanyar muryarta tayi masa sallama. Amsawa yayi yana d'ago kyawawan idanun shi, wani irin kallo yake mata mai cike da ma'anoni fuskar shi babu walwala ko ta sisi.
A take ta runtse idanu don bata son ya gane a firgice take, balle har yayi tunanin tana mugun tsoron shi ne. " Ba zaki bar zuciyata ta huta ba ko?", sune kalaman da ya fito daga bakin shi yana mai k'ureta da maganan shi. D'an dagowa tayi tana mai dubanshi da kyau, saurayi ne d'an matashi haka mai kyau da aji. Fari ne tas don har ya d'ara ta a haske haka za kyau, kana ganin shi kaga Fulani cikakke babu mix har a maganar shi ma kuwa.
A d'an shagwab'e tace " ko gaisawa bamu yi ba zaka fara complain ko?" Girgiza kan shi yayi yana mai cewa " ba k'orafi nake ba Meenah, kema kin san abinda kika aikata who is he?". Shiru tayi ta tabbatar munafukan unguwa sun shaida masa da tsayuwar ta da wani, ta kuma san tsananin kishi irin na Nazeem abinda ma ya sata firgicewa tun da ya kirata kenan.
"Shirun ki yana nufin abubuwa da yawa Meenah, yana da kud'i ko? ". Kallon shi tayi yanzu kam da kyau cewa tayi " ai da yake ni mayyar kud'i ce dole ka tambaye ni hakan". A d'an hasale yace " it's just a question, na san yana da kud'i since he's even riding a sport car".
YOU ARE READING
YASMEENAH
Science FictionYASMEENAH Da mamakance nake kallon kaina, ni ce amma bani bace! Bani bace wacce ke tsaye a gabana. Toh wacece ni ina kuma na tafi?, tambayoyi ne da ban da amsarsu don ko zaa shaƙe ni ba zan iya amsawa ba. A dai-dai lokacin bugun ƙofar shi ya tsanant...