CHAPTER 4

7 0 0
                                    

YASMEENAH

Khadeejah Bint Ismail ( Deejasmah)

Mikiya Writers Association ( MWA)

Dedicated to Asma'u Abubakar Musa ( Jasmine)

With love to Radeeyah Ismail ( Uomm Ajmal)

Wattpad @deejasmah15
Arewabooks @deejasmah
Bakandamiya @deejasmah

09042522373

TOP TEN

CHAPTER 4

A y'an kwanakin soyayya suke bugawa ita da Sarham, inda ta fuskanci halayyan shi da dama yana da zafi sosai don har yafi Nazeem. Shi Zeem dama zafin kai ne ta mai zaman banza tayi mai yawa while shi yake da authority da son girma, hakaza bai son musu ko gardama. Duk abinda ya tsaida toh ya zauna, a sati guda sun yi fad'a fin uku duk laifin bai wuce tace Aa.

A gefe guda kuma ya dage akan lallai sai ta bashi dama ya tura, wanda take ta dojewa hakan. Dan tana tsoron masifar shi ba kuma ta gama shawara da zuciyarta akan zab'in shi ai mijin aure ba, sai dai data nemi shawarar Mama cewa tayi " mazan ba tukwane bane ai Meenah, kowa da nashi kalar halin gwara mai fad'an sau da dama akan wasu halayen in dai kika iya zama dasu da kaucewa duk abinda zai sa ran shi b'aci shikenan amma mashayi ko mazinaci fa?, ko wanda zai lullub'e halin shi kayi tunanin mutumin kirkine sai kin shiga kiga ba haka bane kiyi istikhara first in dai kin yaba da halayen shi bai da wani aibu bayan fad'an kin ga shikenan sai mu sha biki".

Dariya tayi tana mai rufe idanunta cikeda kunya tana cewa " kai Mama!", itama dariyar tayi tana cewa " y'ar nema, toh mai za a jira daku? in dai har kin samu miji ai aurar dake za muyi sai addua da fatan Allah kawo na y'an baya" Ameen ta furta k'asan ranta amma a fili murmushi kawai tayi tana barin d'akin, girgiza kai Maman tayi tana binta da kallo ta na son natsuwarta sam bata da kwarafniya ga hankali.



San da suka je kwanciya ne take shaidawa Zuu yanda sukayi da Mama itama tayi caraf tana cewa " ai gaskiyar Mama ne, mai za a jira tunda a shiryen shi yake?", tura baki tayi tace " tab'din sai in yi aure Yayata bata yi ba?" Juya idanu tayi tana cewa " and so? kowace mace ai da lokacinta in nawa yana da nisa naki yana kusa sai ayi ta delaying naki har sai mazan sun tafi just saboda ni nawa bai zo ba? Wannan duk tunanin da ne my love, yanzu zamani ya canja da zaran mace ta samu miji aurar da ita akeyi so babu laifi ko d'aya let's just keep praying for the best".

Ta furta har ranta sai dai kuma tana d'an jin babu dad'i amma kuma ta san auran Yasmeenahn ne kwanciyar hankalinta, don tana da yak'inin idan tayi aure toh itama zata fi samun masoya. Gani take ita ta dasashe haskenta a wurin manemanta, so aurenta shine mafita ga nata matsalar.


Cikeda tausayi take kallonta, in da so samu ne tafi son su samu miji rana d'aya amma kuma kana naka ne Allah na nashi, duk kuma abunda yayi toh mai kyau ne. A hankali ta lumshe idanu tana cewa " toh Ameen, Allah ma ya fito miki da wani duk a had'a mu tare". Dariya tayi har ranta taji dad'in adduar don haka tace " Ameen" bakinta ya kasa rufuwa, sai kuma tace " but Zuu ya zanyi da Nazeem". D'an tsaki ta ja tana mai cewa " you dey mind dat werey?".



Had'e rai tayi jin sunan da ta kirashi sai dai bata tanka ba. Lura da canjin fuskar ne yasa tace " oops ashe Masoyi ne, my bad" uhmm kawai tace don taji zafi, bata damu ba ta cigaba da magana " kar ki biye ta Nazeem don irin wainnan kin san ba alkhairi a lamarin su, ki kama dahir kafin lokaci ya k'ure" ajiyar zuciya ta sauke kafin tace " amma kin san zaa yi k'ura da shi ko?". Cewa tayi " toshe kunne zakiyi da duk wani haukan da zaiyi, in ya ga ba ci dole ya hak'ura" jujjuya maganar tayi ta yi sai dai Zuu bata bari tunanin yayi nisa ba ta kawo wata hira, hakan yasa ta ajiye ta shi tana bata amsa, sun dad'e suna hirar su har barci ya kwashe su.


YASMEENAHWhere stories live. Discover now