CHAPTER 12

8 0 0
                                    

YASMEENAH

Khadeejah Bint Ismail ( Deejasmah)

Mikiya Writers Association ( MWA)

Dedicated to Asma'u Abubakar Musa ( Jasmine)

With love to Radeeyah Ismail ( Uomm Ajmal)

09042522373

TOP TEN

CHAPTER 12

Zaro idanu tayi jin abinda ya fad'i d'in, tabbas shi ne sai dai kuma ita tunaninta bai tab'a zuwa ko kusa da wurin ba. Wasu tambayoyi ta sake masa a kan matsalar a take taji kanta ya washe, ajiye maganar sukayi suka tattauna akan abinda ya kawo shi office d'in in the first place.

Fita yayi bayan gamawarsu. yayinda ita kuma ta koma kan maganar da sukayi, dogon research tayi a kai and everything da ya shafi case d'in kafin ta tattara kayanta zuwa gida cike da k'warin guiwa.

9:00 dai-dai ya zauna a gabanta yana mai tsura mata idanu, da ma tun dawowarta yake takalinta da maganar amma ta k'i ba shi damar hakan sai ayyukan gida da take tayi. Kallonta yayi yana mai cewa " jan ran yayi yawa madam, ki fiddani a haske".

Ajiyar zuciya ta sauke kana tace " Hubby ba fa wani abu bane, zargi ne sai anyi test za a tabbatar ".

"Me za ai wa test d'in?". Ya tambaya cikeda rashin fahimtar in da maganar nata ya dosa, murmushi tayi tana cewa " ni dai gobe ka kai ni in d'ebi jininta or rather ka bamu ita muyi mata a clinic d'in mu in dai har abinda muke zargi ya tabbata toh, but before that muna son ayi mata DNA test ne to confirm if she's the same person sai ayi comparing result d'in da test d'in da sukayi na aure ".

"Yanzu dai kina nufin ba za aji komai ba kenan sai bayan fitowar result d'in?" Ya tambaya yana mamakin lamarin, kai ta gyad'a masa kana ta cigaba da cewa " yin test d'in shi zai tabbatar da kasantuwarta Yasmeenah or somebody else in kuma ita d'in ce then there's need ayi dogon bincike akan cause na juyawarta sai ayi treating abun, now dai we only need to confirm if it's her ".

Ajiyar rai ya sauke yana cewa " can't we just go there now?". Girgiza kai tayi tana cewa " mu dai bari zuwa goben please, so that by Monday the result will be ready". Ok ya furta yana mai kallon file d'in gabanshi.

Washe gari bisa azazzalawarshi 8 suka tafi station, cell ta buk'aci a kai ta. ACP ko cewa yayi a kawota office kawai, girgiza kai tayi tana mai cewa " let me see her alone please, i want her to be free and comfortable with me so let me be". Ok yace kafin suka rankaya zuwa cell d'in, Asabe ta bud'e a nan ta dakatar da su ita d'aya ta shiga wurin Yasmeenah.

A duk'unk'une da ta saba zama take, duk da taji shigowar mutum d'akin amma bata d'ago ba sai ma sake sunne kai da tayi a gwuiwarta. Cike da tausayi take bin d'akin da kallo, tun daga kan kwalin k'asa ceiling da ma toilet kafin ta dire ganinta akanta.

Sallama tayi mata cikin sanyin murya, da sauri ta amsa tana d'ago da kanta. Rintse idanu tayi a sanda tayi arba da fuskar ashe pic ya rage abun sosai ( wannan fa pic d'in ranar farko ne ita ko Yasmeenah kullum yanayinta sake sauyawa yake yi). Yawu ta had'iye ta bud'e idanun tana mata murmushi, da idanu ta bita kawai tana mamakin shigowarta wurin

Kamar almara taga matar ta zauna a gabanta, hannu ta d'aura a gwuiwarta tana mai cewa " kar ki tsorata my dear I'm here to help you, duhun da ya mamaye tarihinki nake son yayewa hope I'm welcome?".

Gyad'a kai tayi kafin a hankali tace " you are welcome Aunty but ke kin yarda da ni ne?". Yes tayi assuring d'inta ta d'aura da fad'in " hakanan na aminta dake and I have a strong feeling that you are the one you are claiming to be, Yasmeenah right?".

YASMEENAHWhere stories live. Discover now