CHAPTER ONE

34 3 0
                                    

YASMEENAH

Khadeejah Bint Ismail ( Deejasmah)

Mikiya Writers Association ( MWA)

Dedicated to Asma'u Abubakar Musa ( Jasmine)

With love to Radeeyah Ismail ( Uomm Ajmal)

Wattpad @deejasmah15
Arewabooks @deejasmah
Bakandamiya @deejasmah

09042522373

TOP TEN🔥

CHAPTER ONE

"Ai ke baki da matsalar rashin saurayi sai dai mu mu koka" wata matashiyar budurwa wacce ba zata kimanin 21-23 ba, wankan tarwad'a ce haka tana da kyau dai-dai gwargwado  ta furta hakan tana zama a gefenta. Kallonta tayi da narkakkun idanuwanta masu hazo-hazo a cikinsu, fara ce amma ba shar ba irin farin nan mai ja a cikin shi. Tana da kyau ainun wanda ganin farko zaka shaida haka, sannan tana da d'an tsayo da jiki irin matan da ake kira full option wato komai ya ji.

Murmushin maganarta tayi tana cewa " kin fiye zolaya Zuu", ware idanu tayi tana cewa " ai kema kin san gaskiya na fad'i, kina da samarin ki wanda ko yau aka ce ki fito da miji zaki iya fito da d'aya daga ciki ni fa?....ai sai dai zare idanu don banda takamaiman wanda zan tsayar" ta k'arashe maganar da d'an d'aci a harshenta. Dafa ta tayi cike da tausayi tace " amma Zuu ai saurayi ba shi ne miji ba, sai ki ga ke da baki da kowa kin fara shiga daga ciki kin bar ni a nan".

Dariya ta kwashe da shi tace " imagination of the century!,,, wannan abu ne da baa zai tab'a faruwa ba ke dai ki godewa Allah kawai Yasmeenah". Ta'be baki tayi tace " baki san ikon Allah bane, yanzu dai tunda dai Baban bai motsa ba ai sai mu cigaba da addua Allah ya fito mana da nagari ko?".

Kafin ta kai ga cewa komai aka bud'e k'ofar aka shigo, doguwar mace ce mai jiki da tsayi duk maganar da sukayi a kunnenta suka yi shi. Sai dai ko a fuskarta bata nuna ba cewa tayi " amma kun manta da aikar da akayi muku ne halan?, kun shige d'aki kun k'ule ko mai kuke tattaunawa ne da kullum baku gajiya oho ".


A tare suka mik'e suna cewa " yanzu zamu tafi Mama", hijab Yasmeenah ta zara yayinda ita kuma Zubaidah ta yafa gyale akan doguwar rigarta sak'on suka amsa, kafin sukayi wa Maman sallama. Da idanu ta rakasu ta na mai cewa a dawo lafiya.

Dake gidan a nan unguwar su yake haka yasa suka tafi a k'afa cike da natsuwa, suna cigaba da hirar da basu gajiya da ita, yanda ka san ba gida d'aya zasu koma ba. Gidan Mama Ramatu suka shiga da sallama, da fara'a ta amsa tana cewa " Aah 'yan biyun Mama ne da ranar nan?, sannunku da zuwa ". Yauwa suka ce suna duk'awa, gaisheta sukayi ta amsa da fara'a tana tambayar su jamaar gida kowa lafiya suka bata amsa kafin suka k'arasa cikin parlorn.

Ruwa ta ajiye musu da abun motsa baki, sake gaisawa sukayi kafin ta zauna. Sak'on suka ajiye mata a gabanta, dubawa tayi sukayi mata bayanin sak'on. Amsa tayi tana bata nata sak'on da zasu kaiwa Maman, basu jima ba suka kamo hanyar tafiya gida.

Honk ake ta musu babu ko k'ak'kautawa, hakan ne ya sanya suka matsa daga kan titin don akan titi suke sosai. D'an wuce su motar tayi kad'an kafin akayi parking, na cikin motar bai fito ba sun d'an wuce kad'an aka bud'e k'ofar gaban motar. Sallama akayi musu cikin wata murya mai cikeda karsashi da aji, tsayawa sukayi ba tare da sun juyo ba suka amsa a hankali. "Nace ba...?", ya furta da ya sanya suka waigo duka a tare " Meenah bari inje, it might be my lucky day" ta furta in a whisper cikin tone d'in da tayi mata magana itama tace " all the best".

Wurin shi ta k'arasa cikin yanga, matsawa Meenahn tayi izuwa k'ofar wani gida. Ko 2 mins ba a rufa ba ta dawo fuskarta da d'an murmushi. "White blood cells ke fa yake kira", ta furta cike da tsokana. Wara idanunta tayi cikeda mamakin jin sunan da ta kirata dashi, cewa tayi " wai white blood cells, ke dai Zuu baki rabo da tsokana". Murmushi tayi tace " Ai gaskiya ne, je ki yana jiranki", ok tace tana nufar wurinshi cikeda natsuwa da aji kamar kullum.

YASMEENAHWhere stories live. Discover now