CHAPTER 5

9 0 0
                                    

YASMEENAH

Khadeejah Bint Ismail ( Deejasmah)

Mikiya Writers Association ( MWA)

Dedicated to Asma'u Abubakar Musa ( Jasmine)

With love to Radeeyah Ismail ( Uomm Ajmal)

Wattpad @deejasmah15
Arewabooks @deejasmah
Bakandamiya @deejasmah

09042522373

TOP TEN

CHAPTER 5

Tunda suka zo neman izinin nan hankalinta yak'i kwanciya, yayinda tunani ya bi ya cika mata k'wak'walwa gani take kamar burinta ne ya kusa cika. Amma yanayin Baba bai nuna ko kusa yana son cikar burin nata ba, tayi nazarin mafita ta kuma samu. Sai dai kuma bata ga alamun shima zai b'ulle ba, anya ba lokacin murza kambunta bane yayi?.

Don da alamu babu kaiwa gaci da b'ullewa a lamarin, da ko ta zauna wankin hula ya kaita ga dare gwara ta bazama tun yanzu. Hakan ne yasa tunanin nata karkata ga dogon burinta, sai dai shi ma akwai tawaya don bata san ta inda zata fara ba. Bata son sa malamai a lamarin gudun kwab'ewar lamarin, da kuma sha'anin koma kan mashek'iya da k'aik'ayi kan yi a lokuta marasa adadi so malamai ba option bane zata fara da neman shawara daga aminiyarta don tasan kaf shawararta babu na yar wa.

Duk fad'i tashinta Baba na hankalce da ita, ya rasa gane kan ta a kwanakin ga matsin da take yawan masa akan Sarham. Ya san tana da san kud'i sosai don ko shi dalilin da ya sanya ta manne masa kenan, amma ba wai don tana son shi can-can ba. Duk da dai ba wani abu yake dashi ba face rufin asiri a lokacin har ma yanzu, amma ya d'ara kaf manemanta da komai.

Duk ko son kud'inta bai isa ya sanya shi kai 'yar shi inda zata wahala ko ba a san darajarta ba, yana son yaranshi irin so mai k'arfi kuma ba su da na biyu bayan iyayen shi da yanzu babu su a doron k'asa. Kuma kaf cikin yaran daga Tamam sai Yasmeenah a darajar so a zuciyar shi, itama ta shaida hakan kuma tana kwatanta soyayyar su don ma shi Tamam d'in sai a hankali tunda ya shilla ya bar k'asan har yanzu bai nufo inda suke ba though suna waya.

Fitowar shi daga wanka kenan yana shafa mai a jikin shi, gidan tsit babu kowa duk yaran sun tafi makaranta sai Zuu da ita d'aya ce bata tafi ba saboda bata da morning lectures. Maman ce ta shigo hannunta d'auke da trayn da aka jera kayan karin kumallo, ajiyewa tayi ta na mai nufar kayan da ta ciro mai. Bud'e su tayi tana feshe su da turaren shi na Shaykus-shuyuk mai sanyin k'amshi sannan ta taimaka masa ya sanya kayan, kafin ya zauna a carpet gaban kayan karin.

Itama zama tayi serving d'in shi tayi sannan ta koma gefe tana mai kallon shi, d'agowa yayi ya kalleta jin tunda suka tashi ba abinda ya shiga tsakanin su sai gaisuwa. Y'ar hirar da ta saba masa ma yau babu, cewa yayi " Maman yara lafiya kuwa?", d'an girgiza kai tayi tana mai cewa " lafiya lau, me ka gani?".

Aje kofin hannunshi yayi yana cewa " ya zaki ce lafiya bayan kin yi sukuku babu annuri a fuskar ki". D'an ajiyar zuciya ta sauke kafin tace " Baban Khalifa damuwa ce tayi min yawa, akan lamarin yaran mu ni kuma na ga kamar kai baka damu ba". Yace " wani abun ya faru ne wanda ban da masaniya?" Girgiza kanta ta sake tace " abubuwa da yawa ma kuma duk ka san dasu amma kayi biris da lamarin kamar baka san da wanzuwar su ba, wanda ni ba zan iya zuba musu idanu ba".



Girgiza kai yayi yana mai jinjina darunta, amma kuma bari ya bita a yanda tazo yace " in ko haka ne toh tabbas na sarayar da nauyi na, menene ya faru?". Tace " maganar Yasmeenah da yaron nan mana! Kana sane da shi yake dawo da ita daga makaranta ga kuma uwar siyayyar da yake narkowa ya kawo gidan nan amma baka maida hankali ba, Baban Khalifa har fa mutane sun fara yada magana akan mu ko don gudun bakunan su ba za a yi abun nan a wuce wurin ba?".


YASMEENAHWhere stories live. Discover now