YASMEENAH
Khadeejah Bint Ismail ( Deejasmah)
Mikiya Writers Association ( MWA)
Dedicated to Asma'u Abubakar Musa ( Jasmine)
With love to Radeeyah Ismail ( Uomm Ajmal)
Wattpad @deejasmah15
Arewabooks @deejasmah
Bakandamiya @deejasmah09042522373
TOP TEN
CHAPTER 6
Da idanu suka bishi har ya k'ule ajiyar zuciya ta sauke, tana mai jin kamar bata kyauta ba. Anya hak'ki ba zai bita ba kuwa? Yana sonta ita kanta shaida ne and what he did was out of love, and she loves him too. Tunda har tana son shi then meyasa ta amince da wanin shi? Meyasa bata kore shi yanda take koran 'yan baya ba? Meyasa ba zata iya jiran shi har zuwa sanda zai samu aikin ba?. Tambayoyi ne da take buk'atar natsuwa da sharafin amsa su wa kanta sai dai ta san ba zata iya amsawa ba don bata dasu a yanzu haka.
Yana lure da ita da tunanin da ta tafi don tun fitowarshi ta d'auke wuta, karon farko da baiji haushi ko ya ga laifin ta ba sai ma tausayi da yaji mai k'arfi ba nata kad'ai ba dukan su sun bashi tausayi ainun. Don it isn't easy rabuwa da wanda ka sawa burin aure, sai dai he's so self-centered when it comes to her. Yana sonta ba kuma zai iya bawa waninshi damar mallakarta ba, sai dai in bai da rayuwa kuma wannan ne baida iko a kai.
Cewa yayi " you haven't done anything wrong Babe, you were just not meant to be". Kallon shi tayi tana mai cewa " I wish I can feel same way but na kasa, ji nake kamar na cutar dashi ". Girgiza kai kawai yayi amma bai iya magana ba, itama sauke idanunta tayi don bata iya jure kallon shi ko kad'an.
Sai da ya nisa kafin yace " kar ki bari damuwa tayi miki yawa, just pray may it be the best for us all". Ameen kawai ta furta tana wasa da hannunta cewa yayi " Babe ya maganar zuwa clinic d'in?" Girgiza kai tayi tana cewa " I'm okay Noorie na sha pain relieve". Narke idanun shi yayi a kanta kafin yace " are you sure?". Yea ta amsa in affirmation.
Sun d'an jima a tsaye amma ba wata hirar azo a gani bane, don mind d'inta bai wani tare da shi. Ganin haka ya sa shi cewa " ki shiga ciki babe we will talk". A hankali tace " Toh Babe, love you" Ya amsa da love you too, shigewa tayi ciki yana tsaye har ta shige kafin ya ja motar shi ya wuce.
A y'an tsukin tunanin Nazeem da halinda yake ciki ya hana mata sukuni, yanda ta fad'i gani takeyi kamar Allah ba zai bar ta ba don tamkar ta yaudare shi take ji. Hatta Mama sai da ta lura da rashin walwalarta ko da ta tambayi bahasi, ai sai Zuu tace " wai tunanin wancan banzan fuk'ara'un takeyi".
Tsaki Mama tayi tana cewa " amma ke dai anyi sakarai wacce bata san inda yake mata ciwo ba, in ba rashin rabo ba meye a Nazeem da har kika mak'ale mashi Allah ya kawo miki arzik'i har gida kina son yiwa kanki sagegeduwa toh wallahi da wasa kika bari na k'ara jin wannan maganar sai na b'ata miki rai Banza mara kishin kai". Ta inda take shiga ba tanan take fita ba, Zuu tana ta zuga ta sai da suka gaji don kan su sukayi shiru ita dai ko cikanku bata ce ba.
Fad'an da suka yi mata ya sanya ta saki ranta har Sarham ya gane hakan, abun yayi masa dad'i don dama a cikin damuwa yake ainun da rashin walwalarta. A ranar da yamma ko sai ga shi, sakin jiki tayi suka sha soyayya kamar ba abinda ya faru.
Gefe guda tuni su Baba sun amshi bak'unci iyayen Sarham, inda aka tsayar da rana due to suggestion d'in Mama 4 months dai dai. Ba haka yaso ba don bai son sa dogon biki amma ta rok'i alfarma saboda shirye-shiryen da take yi.
Kaya na gani na fad'a aka kawo kamar ba a san ciwon kud'in ba, ko kayan sa rana kamar wacce suke shirin bud'e shago da sauran kayayyaki . Yawan kayan sai da Baba yayi fad'a itako da fariya da gadara take nuna kayan, har gayya take yi na musamman in anzo ta bazo k'amshi ta zauna tsakiya tana maida yanda akayi tana cewa " ai samun mace mai goshin Yasmeen a unguwar nan sai an tona" y'ar korarta Mama rahama na daga gefe tana cewa " ai Meenah ta dangwalo arziki".
YOU ARE READING
YASMEENAH
Science FictionYASMEENAH Da mamakance nake kallon kaina, ni ce amma bani bace! Bani bace wacce ke tsaye a gabana. Toh wacece ni ina kuma na tafi?, tambayoyi ne da ban da amsarsu don ko zaa shaƙe ni ba zan iya amsawa ba. A dai-dai lokacin bugun ƙofar shi ya tsanant...