YASMEENAH
Khadeejah Bint Ismail ( Deejasmah)
Mikiya Writers Association ( MWA)
Dedicated to Asma'u Abubakar Musa ( Jasmine)
With love to Radeeyah Ismail ( Uomm Ajmal)
Wattpad @deejasmah15
Arewabooks @deejasmah
Bakandamiya @deejasmah09042522373
TOP TEN
CHAPTER 7
Biki wan shagali wai kowa ya raina ba nasa bane, tabbas haka yake don duka b'angare biyun sun kacame da shiri. Su Mama ana ta shirin kece raini while gidan su Sarham suke shirin fita kunya, bana alfahari ba. Duk da dai ko fariyar zaa yi toh da akwai.
A gefen Sarham kam hidindimun sun cakud'e ga gyaran gida ga aiki, ga sauran abubuwa don ma bai d'auko ta yanzu daga school duk da sun koma don dama break d'in 2 weeks ne.
Ta b'angare Meenah kam kamar ba amarya ba as people dey talk, don babu irin ramar nan da amare kan yi sai k'iba take mulkawa kamar wacce ake hurawa. Dama she's kinda thick but yanzu ta sake mulmulewa, sai d'an karen haske da take k'arawa shi ma kamar tana bleaching. Bakin mutane ya sa ta koma sa nik'ab da socks, don duk inda tabi sai an tanka hakan ko ba k'aramin dad'i yayiwa Sarham ba.
A baje suke a tsakar d'aki kaya ne a gabansu, suke bud'ewa yanzu suka dawo daga wurin tailor. Bridal gowns d'in sun had'u har sun gaji da had'uwa, Zuu ta kalleta tana cewa " ki tashi ki gwada kayan nan, mek I see yanda zasu yi miki ".
Numfashi ta sauke tana sake bajewa a kan carpet, bata san meyasa a kwanakin nan take yawan gajiya ba. Abu kad'an za tayi taji ta gaji kamar tayi aikin azo a gani, cewa tayi " wai sai an gwada?, measurements d'ina ne fa". Ta kalleta da kyau tana cewa " ke fa na lura dake kwanakin nan raki kawai kika iya,kuma tsabar shagwab'a ce tayi miki yawa in zaki mik'e ma tun wuri tohm don wuya zaki sha ".
Tura baki tayi tana zama kafin tace " ke kuma kin cika masifa wallahi, ni ba wata rakin da nakeyi tsabar wahalar da ake bani ne a kwanakin nan daga wannan sai wannan". Cewa tayi " eh lallai, saboda bamu je mun fito da asoebi mun yi yawon rabon su da kuma IV bane ya sa kike fad'in haka". Zare idanu tayi tana cewa " da ba zan ganu ba kenan, Allah yana sona shiyasa". Dariya ta sanya ganin reaction d'in ta tana mai cewa " ni dai ki tashi ki sa kayan nan".
Sanin in bata tashi ba ba zata tab'a barinta ta huta bane ya sanya ta tashi zaune, kayan ta d'aga da duka fitted gowns sai ball gown gud'a d'aya ne ta zuge zip. Towel ta nemo ta d'aura kafin ta cire na jikinta, zurawa ta fara k'okarin yi sai dai yak'i shiga sai a wurin cikin da har y'ar tumbi tayi hips d'in ya tsaya.
Da mamaki take kallon kayan don dai measurements d'in ta ne, to ko dai bai sa dai-dai bane yayi amfani da na Zuu tunda dama ta fita k'iba?. Bata da mai bata amsa sai ta d'aga kai tana kallon Zuun da itama kallonta takeyi da mamaki, tace " lallai amaren zamani, ana rama kina k'iba da alamu in aka kaiki gidan SarMeen ba zamu ganeki ba".
Tale baki tayi tana cewa " ke ta wannan kike ma, ni yanzu ina ake son in bi in ga haske 10 days to biki kayan biki sun k'i shiga?". Cewa tayi "kaiwa zaa yi ya d'an bud'e su dama ai dole suyi fitting, in an bud'e zai bi koina though ba haka aka so ba kaya in aka bud'e basu wani kyau".
Cewa tayi " yanzu naji batu, wannan kuma in ya zauna ba matsala not everyone will notice wai an tab'a su" a hankali tace " hakane kuma amma the styles are madd! Zamu bada kala ranar". Cire kayan tayi ta maida nata ba tare da ta tanka mata ba, don ta lura ita bata da damuwa yoh in ba rashin damuwa ba ana zancen zaman kaya ita ta style take".
YOU ARE READING
YASMEENAH
Fiksi IlmiahYASMEENAH Da mamakance nake kallon kaina, ni ce amma bani bace! Bani bace wacce ke tsaye a gabana. Toh wacece ni ina kuma na tafi?, tambayoyi ne da ban da amsarsu don ko zaa shaƙe ni ba zan iya amsawa ba. A dai-dai lokacin bugun ƙofar shi ya tsanant...