CHAPTER 13

24 0 0
                                    

YASMEENAH

Khadeejah Bint Ismail ( Deejasmah)

Mikiya Writers Association ( MWA)

Dedicated to Asma'u Abubakar Musa ( Jasmine)

With love to Radeeyah Ismail ( Uomm Ajmal)

09042522373

TOP TEN

CHAPTER 13

Almustapha Jalige this chapter is for you indeed your love for Yasmeenah is a top notch. Thanks for the love and support enjoy and be happy.

Lumshe idanunshi yayi kawai yana yin abinda zuciyarshi take ayyana masa, ji yakeyi kamar hanya d'aya da yake da ita kenan da zai iya expressing how sorry he is ya kuma tabbatar mata da cewa har abada yana son ta a duk yanda take.

Cizo ta gartsa masa a harshenshi ya ko had'a har da lip d'in shi na k'asa, da sauri ya janye bakinshi yana dafe shi cikeda razana don cizon ya shige shi ba k'arya. Hawayen idanunta ta share tana mai kawar da idanunta daga kan shi, hannu ya kai ya na kamo nata cikeda tausayi DDA so mai k'arfi.

Ba ta waigo ba kuma hawayen idanunta basu tsaya da gudu ba, bata hanasu ba barinsu tayi suna sharafinsu yadda suke so don tun farkon lamarin ba ta samu damar hakan ba sai yau. A hankali cikin narkakkar murya yace " I'm sorry!!". Juya idanunta tayi tana mai kallonshi, murmushi tayi mai ciwo tana cije already swollen lips d'in ta tace " sorry? For?".

"Everything, the pain, the cries and......" Katseshi tayi da cewa " and for not keeping your promises?, for breeching my trust and leaving me stranded? Sarham ka na tunanin your sorry is enough for all that you've done huh?". Ta k'arashe da kuka mai k'arfi, hannu ya kai zai tab'ata ta janye tana mai cigaba da kukanta kallonta yake yi da tsantsar tausayi yayinda kalaman bakinshi suka k'afe ya rasa ta ina zai fara ga kuma kukanta dake ci masa tuwo a k'warya.

Yace " na sani it ain't not enough, amma wallahi I've done everything for your love I was worried and devastated that time na rasa ta ina zan fara ne a tunanina an shigo ne an cutar dake ba laifina bane ke ma kin san hakan anybody in my shoe will do same ". Gyad'a kai tayi tana cewa " love indeed! Shi soyayyar ne ya rufe maka idanu har ka kasa reasoning? Ko da wani ne ya shigo gidan nan ba zaka iya resolving issuen da natsuwa ba har sai yayi resulting to duka? Dukan ma har da murder attempt ai ban tab'a sanin I married a monster for a husband ba, bayan nan ka had'a ni da police baka tab'a waiwayowa ba balle ka san halin da nake ciki ba..." Kasa k'arasawa tayi saboda kuka, Allah ne kad'ai ya san yanda take ji a zuciyarta a kan abinda ya faru. Ta kuma fi jin zafin abinda ya aikata mata fiyeda wanda y'an gidansu sukayi mata, a tunaninta ko fin haka ta canja zai natsu ya saurari bayananta ba wai bugunta ba. Tana da yak'inin in shi ne yake cikin makamancin halinda take ciki zata zauna da shi har izuwa randa Allah zai yaye komai.

Kasa jure kukanta yayi ya janyota jikinshi da kyau yana mai rungumeta tsam a k'irjinshi, patting bayanta yake yi a hankali yana jero kalaman rarrashi a gareta har sai da ta d'an tsagaita da kukan kafin ta fara k'ok'arin zame jikinta. Hanata damar hakan yayi sai janta da yayi zuwa bakin gado suka zauna, a gefenta ya zauna ya fara magana cikeda natsuwa da son kwantar mata da hankali.

"Na shiga matsananciyar damuwa akan abinda ya faru, ko ranar da abun ya faru a asibiti na kwana infact kwanana uku a asibiti ko da aka sallameni ba wai don na warke bane Aa matsa musu nayi saboda hankalina yana gareki. Burina in nemeki a koina ne possible, duk wani bincike munyi a tsakiyar hakan ne Allah ya jeho mana da Malam shi ne kuma ya warware sark'ak'iyar da ta faru yanzu dai burinmu bai wuce Allah ya baki sauk'i ba and I won't rest har sai na binciko wanda yayi sanadiyyar jefa ki cikin wannan yanayin '' Ya k'arashe bitterly.

"Yaushe ka fara yarda da Malami kuma ban sani ba, wato in da Malam d'in bai fad'i hakan ba da har yanzu ina cikin wancan d'akin kenan ko?". Ta furta itama tana jin d'acin zuciyarta yana dawowa sabo fil, kai ya girgiza yana mai cewa " Aa ko babu Malam a shirye muke da shirin tsananta bincike a kanmu tunda it's our last option and ba wai mun baiwa Malam yardar mu ne over everything ba sai don kasancewarshi mai tsayawa a kan gaskiya da kiyaye dokokin ubangiji".

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jan 19 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

YASMEENAHWhere stories live. Discover now