YASMEENAH
Khadeejah Bint Ismail ( Deejasmah)
Mikiya Writers Association ( MWA)
Dedicated to Asma'u Abubakar Musa ( Jasmine)
With love to Radeeyah Ismail ( Uomm Ajmal)
Wattpad @deejasmah15
Arewabooks @deejasmah
Bakandamiya @deejasmah09042522373
TOP TEN
CHAPTER 3
Cikin k'unar rai yake driving lallai ma Meenah yana mata kallon mai hankali ashe irin wainnan yaran take kulawa? har da wani ce mata taje gida, dukan steering wheel d'in yayi yana tuna kamota da ya kusa yi. Lallai a yau zata san shi waye, don ta kiyaye ko don gaba. Tsaki ya sake a karo na ba adadi, cikin ikon Allah ya kawo gida.
A bakin wani had'add'en gida yayi horn, tun daga waje zaka iya shaida tsari da haduwar gidan. Balle kuma sanda security guard ya bud'e gate, tsayawa labarin gidan b'ata baki ne ainun amma ka kwatanta had'uwa da kyan gida irin na y'an gayu. Though ba wata k'awa akayi wa gidan ba tsabar tsari da yanayin tsarin ginin da yafi kama da gine-ginen Turkiya shi zai ja hankalinka.
Shigar da motar yayi yana mai parking a inda aka ajiye takwarorinta, lumshe idanu yayi ba zai iya shiga wurin Mamie a yanda yake ba. Don tabbas zata tambaye shi abinda ya b'ata masa rai, and he's not ready to discuss that with anyone don haka ya nufi part d'in shi cikeda b'acin rai.
Yanda ya b'ule shi da hayak'i ba k'aramin sake hargitsa shi yayi ba, wato shi zasu wulak'anta su tafi su bar shi kamar mahaukaci. Bakin shi ya ciza yana mai ciro wayarshi numb Meenah da yayi saving as "LOML" da emojin heart da lock ya fara dialing. Har ta katse bata d'aga ba, sake kira ya kuma shi ma same thing a na ukun ma sai yaji switch off.
Wani k'ululun bak'in ciki ne ya sake zuwa mai k'irji, k'arasawa yayi jikin gate ya fara knocking a d'an zafafe kamar zai b'alla. Ai ko nan take yara suka d'an fara zagaye wurin suna masu kallon shi, a take aka bud'e gidan Zuu ce cikin kallon k'ask'anci tace " lafiya Malam kake shirin b'alla mana k'ofa, bashinka muka ci ne halan?".
Kallon tsana yayi mata don duk da kasancewarta 'yaruwar Meenah amma yayi masifar tsanarta yadda baka tsammani, yace " Dallah ba wurin ki nazo ba, kin zo kin tsareni da wata kod'ad'diyar fuskar ki sai ki koma ai". Ware idanunta tayi a kan shi jin yadda ya kira fuskarta da kod'ad'diya, kafin cikin dariyar rainin hankali tace " ohhh haka ne fa ba wurina kazo ba, amma ina son ka sani ita wacce kazo wurin nata ba zata fito ba zaka iya jan tsumman k'afafunka ka tafi ko in sa yara suyi maka watsin kasa?".
Ya san kanun rashin mutuncin ta ya kuma san wannan k'arami ne daga abunda zata iya, da ko yara suyi masa watsin k'asa da ihu gwara ya wuce. Wulak'ancin da akayi masa ma ya ishe shi ba sai an k'ara masa da wani ba, sai ji yayi tace " auuu, ba zaka tafi ba?, kaiii Shamwilu kuzo in saku aiki...." Kafin ta k'arasa yaran suka iso yuuuu kamar dama abinda suke jira kenan.
Murmushin nasara tayi tana kallon shi, shima kallonta yayi dead in the eyes yana cewa " ai shiyasa har yanzu kika rasa mashinshini, toh wani sakaran ne zai d'auki mai mugun hali irinki ai sai dai kara da kiyashi ' d'aukar marar sani' zan tafi ba wai don ina tsoro ko shakkar abinda kike k'ok'arin sawa a min ba Aa sai don saboda ba zan iya zama muna shak'ar iska d'aya da worthless piece like you ba. Shegiya mai bak'in jini kawai".
Yana gama fad'in haka ya juya, yana mai jin dad'in rage fushin shi a kanta. Ita ko tsayawa tayi k'ik'am tana mai jin d'aci a ranta, lallai ma Nazeem har shi zai mata gorin samari. Toh ai da saurayi irin shi gwara ace bata da kowa, sai dai kuma abun ya mata dukan da baka yi zata ba. A take ta runtse idanunta hawaye suna gangarowa, juyawa tayi ta koma tana mai banging gate d'in har ta manta da yaran jama'a da ta tattaro. Tana tura gate d'in ta duk'a a k'asa tana mai sanya kuka mara sauti, ta d'an dad'e a wajen sai da taji d'an sukuni a zuciyarta kafin ta nufi parlor.
YOU ARE READING
YASMEENAH
Ciencia FicciónYASMEENAH Da mamakance nake kallon kaina, ni ce amma bani bace! Bani bace wacce ke tsaye a gabana. Toh wacece ni ina kuma na tafi?, tambayoyi ne da ban da amsarsu don ko zaa shaƙe ni ba zan iya amsawa ba. A dai-dai lokacin bugun ƙofar shi ya tsanant...