A daren Badiyya fir taki bacci, wai ita sai ta kaita taga Anty Maimuna. Firdausi abun duniya yai mata yawa; batasan ko sunga Ahmad dinba, shin waya kashe Anty Maimuna? Tambayar datafi tsaya mata a rai kenan. Ashe dama Ahmad yana gari har yake zuwa wani waje cin abinci, amma bazezo gida ba? Kodan Badiyya.
Dakyar ta samu ta lallaba Badiyya tayi bacci, ita kuma bacci ya kauracewa idonta. Wai meke shirin faruwa da rayuwarsu? Ahmad ya tafi yayi sati bai dawo ba, Amma kuma Kamal yace tare suka ci abincin rana, Sannan kuma an samu gawar Anty Maimuna.
Haka ta tashi taje ta dauro Alwalla tazo ta tada sallah, tanayi tana kuka; domin Allah ya karkato da hankalin Ahmad ya dawo gida. Ko badan ita ba, kodan Badiyya.
Bayan ta gama sallah, ta karanta Al-Qurani; har zata rufe maganganun Badiyya suka dawo mata a kwakwalwa. Ta bude ta karanta Suratul Mulk, hade dayi ma Baba, Anty Maimuna da Mama addu'ar samun rahamar Ubangiji.
Bayan ta gama karatun Al-Qurani, ta zauna tana pouring heart dinta ma Allah, dukda bata furta kalma ko daya ba, Amma taji dadin yin shirun da tayi. Koba komai wani bangare na zuciyarta ya mata sanyi.
A hankali ta tashi taje ta kwanta kan gadon ta, ta janyo Badiyya wadda taji tanata shesshekar kuka, ta rungume ta; tana rufe idonta cikin yanayin damuwa.
***
Da safe Badiyya, ta farka bata ce kala ba; a sanyaye tayi wanka taje sukai breakfast.
Itama Firdausi mutuwar ta tsaya mata a rai, gashi tanaso taje amma wayar Ahmad bata shiga balle ta fada mashi.
Bayan sun gama breakfast, a hankali Badiyya ta tashi ta shiga dakinta. "Momy, ki karba ki saka mu tafi." Ta fada a raunane, tana mika ma Firdausi Hijab dinta. Itama ta saka tata tai mata tsaye bisa kai.
Firdausi a hankali ta karbi hijab din, tai tsaye tana kallon Badiyya, domin batasan da wane baki zata fada ma Badiyya bata iya fita sai Ahmad ya yarda. Dan tasan kota fada mata ba yadda zatai ba.
Dakyar ta bude baki kamar bataso. "Kinga ko, Badiyya matar aure bata fita saita tambayi mijinta." Ta fadi tana janyota ta zauna kusa da ita. "To kinga Dady be dauka ba, ki bari sai wayarshi tayi." Ta fadi tana kallanta, burinta Allah yasa Badiyya ta fahimci me take fadi.
Badiyya ta dade tana kallon mahaifiyarta, alamun bata gane ba, sai da kyar ta iya bude bakinta. "To Momy, yanzu bazamuje bane?" Ta tambaya, hawaye na fara zuba daga idonta.
"Aa Badiyya, bari in kara trying number shi in gani." Firdausi ta fada hade da dauko wayarta.
Tana kira taji ta shiga, murmushin farin ciki tai ma Badiyya. Har saida ta kira sau uku tukun Ahmad ya dauka. "Hello." Ya fada a dakile, dagajin muryarshi yana cikin damuwa.
"Ina wuni." Ta fada, a dardare.
"Meya faru?" Ya tambaya, alamun baida lokacin gaishe gaishe.
"Dama jiya ne, Kamal yake fada man wai an kashe Maimuna." Ta fada hade da nuna damuwarta.
"Sai kuma aka ce maki ban sani ba." Ya katseta, cikin kosawa.
"Kayi hakuri. Dama so nake naje, in masu gaisuwa." Ta fada a dardare.
"Na hanaki zuwa ne?"
"Aa kayi hakuri." Kamin ta sake cewa wani abu ya kashe wayar.
Tai smiling lopsidedly. "Badiyya, dauko man car keys dina mu tafi." Firdausi ta fada hade da saka hijab dinta, tana mikewa tsaye.
Badiyya ta mike a hankali ta wuce zuwa dakin Momynta, tana mai jin dadin atleast zataje taga Sultan.
Bayan ta fito ta mika mata, suka fita. Suna tafiya ba wanda yace ma wani komai, a haka suka karasa Layout.
YOU ARE READING
RAYUWAR BADIYYA ✅
General Fiction"Tun ina yarinya kike zagin mahaifiyata, tun bansan menene maanar kalmomin wulakanci da muzgunawa ba nakejin kina fadarsu ga mahaifiyata, ina cikin wannan halin wani azzalumi yaje ya kashe min mahaifiya, a gaban idona kika hana a tafi dani inda zanj...