kallon kallo aka fara tsakanin Sultan da Badiyya, shi yana tsoron abunda Baba Baraka ta furta zatayi, dan yasan tabbas maganar da tayi babu chanji, indai ba wani iko daga Allah ba. Ita kuwa Badiyya mutuwar tsaye tayi, dukda bata taba ganin Baba Baraka baKallon amma yanayin fuskarta ya nuna mata babu sauki a tattare da ita, gaba daya wata irin fargaba da tashin hankali ne ya lullube ta. Sultan ta kalla shima ya kalleta, kafin a hankali ya bude baki ya fara magana "Baba baraka sannu da zuwa, maganar da kikaji wasa ne ba da gaske take ba, kinyi misunderstanding maganarmu ne, ko Debbo am?" Ya fada yana kallon Badiyya, alama ya mata da ido akan ta amsa mashi.
Rausaya kai tayi alamar tausayi, kafin ta kakaro yaken dole "Baba baraka sannu da zuwa, cikin wasa mukayi maganar, ku zauna Khadija bari na kawo maku abinci," tana fadin haka tayi sauri tayi hanyar kitchen, dan tsabar tsoro ji take kamar ta fadi kasa.
Fizgo hannunta dataji anyi yasa ta juya, yan cikinta ne suka kada, ganin fuskar Baba baraka murtuk, tana jefa mata wani mugun kallo da take jefa masu itada Sultan. Rike hannunta tayi tana jujjuyawa, kafin ta fara magana "yanzu kai Aliyu dan ka raina mani hankali, ka kalli wannan yarinyar kace batada juna biyu? Kuma daga jin yarda kuke maganar da gaske kukeyinta, kuma yadda naga idan yarinyar nan taurin kai ne da ita," ta fada tana wurga ma Sultan wani irin mugun kallo. Sakake sukayi shida Badiyya, dan sunsan karshen rashin gaskiya sun kaita.
Ya bude baki zaiyi magana Baba baraka ta tsayar dashi ta hanyar daga hannunta, "gobe kazo gidan ka sameni, zan kira yan uwan babanka naji wanda baima yaranshi miji ba cikinsu, sakaran banza kawai," tana fadin haka taja hannun Khadija wadda hawaye sun cika mata idanu sukayi waje, fal ran Khadija cike da damuwa yake, dan tasan halin Baba baraka, irin dangin mijin nanne masu muguwar akida.
Har sun fita falon Badiyya da Sultan suka biyosu "Baba baraka ku tsaya ko ruwa kusha dan Allah," Badiyya ta fada murya a dardare, dan gaba daya tsoron matar ne ya darsu a ranta.
Wani irin mugun kallo Baba baraka ta wurgo mata gamida tsaki, "da can da nike ai naga baki bani ruwan ba saiyasa nazo nan insha, wanda baisan dan cikinshi inaga wani dangin miji," ta fada cikeda gatse hade da kama hanya.
Sultan bayansu yabi jiki a sanyaye "Baba baraka to ku tsaya na fiddo mota na maidaku gida dan Allah," ya fada yana jifarta da kallon roko.
Tsaki tayi "kai dalla rufe man baki shashasha, kaida mace kesan mulkawa zaka wani zo haikan haikan kace zaka kaini gida? Wallahi ka fita idona, sakarai kawai," tana fadar haka ta fita, dama driver Kamal ya saka ya kawosu, rai a bace ta wuce gidansu su Sultan, a ranta tana ayyana irin balain da zata shuka gameda maganar nan.
Yana shigowa falon yaga Badiyya bata nan, dakinta ya shiga ya ganta zaune ta juya baya, daga gani wani abu take kallo, ga hawaye dake bin kuncinta sai shasheka takeyi.
Jiki a sanyaye ya isa inda take, kusa da ita ya zauna kafin yakai hannu ya karbi abunda take kallo, camerarta ce yagani tana kallon picture din da sukayi ita da Firdausi, a ranar da zata rasu, wani irin tausayinta yaji ya bala'in kamashi, dan kuwa yasan babu wanda take bukata fiye da mahaifiyarta a lokacinnan. Hannu yakai ya rungumota ta gefe, tanajinta kan jikinshi ta saki wani irin kuka mai kona zuciya, baice mata koma ba, dukda shima heart dinshi tana burning beyond expectation, saida ta gaji dan kanta kafin ta fara magana.
"Sultan am, dama ashe haka Momy takeji duk lokacin da Gwaggo ta mata ko kallon banza ne? Ashe haka zuciyarta ke kuna aduk lokacin da Gwaggo ta jefeta da mugayen kalamai? Sultan am ashe haka take shiga cikin hali na damuwa da bakin ciki aduk lokacin da wani abu ya hadata da Gwaggo? Inkau hakane Momy ta dade tana kunsar bakin ciki, ta dade tana rayuwa cikin kunar rai, ta dade tana kuka wanda batada mai lallashinta. Lokacin da naji zan auri Nabil I was afraid akan wane irin mutane ne danginshi? Would they accept me? ko kuma zasu kyamace ni ne? I was happy lokacin dana gane cewar kaine mijina, saboda nasanka nasan danginka, inasansu suna sona, ashe I was wrong, life isn't always a bed of roses, Sultam am," kuka ta fashe dashi kamar zuciyarta ta fito, hugging dinshi tayi jikinta yana kyarma, shi kuwa kasa ce mata koda tayi hakuri ne, dan shima da zaa barshi yayi kukan dayaji dadi, saboda bayau yasan Baba baraka bata chanza magana ba.
Saida kukan ya tsagaita ne ya samu ya fara magana a hankali "Badiyya, dan Allah kiyi shiru kiyi hakuri, it wasn't her fault, she wasn't that rude, abunda tajine yayi hyping dinta up, we should just keep on praying, and you should also stop crying Badiyya, it's not good for the baby," ya fada yana patting bayanta, danshi a tunaninshi yanzu ta hakura tana nadama ne.
Dakyar ya samu taci indomie kafin suka kwanta, still tana ajiyar zuciya, lokaci zuwa lokaci tana kiran 'Momy', tayi mugun bawa Sultan tausayi, dan yasan ji take mutuwar ta dawo mata sabuwa.
***
Washe gari sama sama suka gaisa hade dayin breakfast, Sultan ya tafi wajen aiki, ya fada mata akan zai biya wajen kiran Baba baraka, dan yasan idan baije ba wani balain ne, dan Baba baraka batada sauki kona zaman minti daya, ga bakar mita kamar shedan. Dakyar tai mashi Allah ya kiyaye ta dawo falon ta zauna tai jugum, abun duniya ya taru ya mata yawa.
Bayan laasar tayi sallah ta dawo falon tana kallo, dan kuwa ganin sakama rai damuwa babu abunda zai mata banda janyo wani balain, tana zaune tana kallo amma zuciyarta gaba daya tana kan Sultan, dan tasan ya tashi aiki by now, probably yana wajen Baba baraka, Allah kadai yasan abunda take kitsa mashi.
Sallamar da taji ne ya katse mata tunani, a hankali ta mike taje ta bude, ganin wata mata tayi tsaye, wadda tana ganinta hawaye ya taru cikin idanunta, sai kawai ta rungume Badiyya, itadai Badiyya bata ganeta ba, amma tasan tabbas akwai inda tasan matar, dagowa natar tayi tana kallonta, kuka take sosai "Badiyya baki gane ni ba ko? Anty Kausar ce (Kanwar Firdausi) Badiyya, kiyi hakuri, munsan mun kyaleki, saidai ba laifinmu bane, wannan matar ce," Anty Kausar ta fada tana rushewa da kuka, Badiyya kuwa ganin dangin nata yadda kasan tsohuwar rijiya na ambaliya haka ta barke da kuka.
A haka suka tafi falo, kuka suke sosai, inda Anty Kausar keta bawa Badiyya hakuri akan kyaletan da sukayi, ita kuwa Badiyya ta kasa magana sai rungumeta da tayi tana kuka, dan kuwa gani take kamar taga mamanta, saida sukayi kafin Badiyya ta kawo mata abun motsa baki, inda Anty Kausar ke fada mata cewar kowannen su hankalinshi baya kwanciya, ga mafarkin Firdausi da suketa yi, hakan yasa Musaddiq wanda yake kasar waje yace Kausar tazo ta dubata, daga baya sunzo, tunda tafi kusa da Katsina. Nan Badiyya ke fada mata ai tayi aure, ita kuma ta fada mata da taje akace Gwaggo ta tashi, shine ta shiga gidansu Ikhlas akasa driver ya kawota gidannan.
Nanfa Badiyya ta fara bata labarin rayuwarta, kuka suke kamar ransu ya fita, Kausar ji tayi tabbas basuyi ma yaruwarsu adalci ba, ace suna raye amma diyarta tayi irin wannan wahalar. Suna zaune Sultan ya shigo fuskarshi zallar damuwa, tsayawa yayi suka gaisa da Anty Kausar cikeda girmamawa kafin ya wuce dakinshi, dan yadda yakejin zuciyarshi kamar anyi gobara cikinta.
A tare da Kausar suka dafa abincin dare, dan kin barin Badiyya ta dafa ita kadai tayi, kasantuwar lura da yaron cikin jikinta da tayi, cikeda farin ciki da soyayya suka gama girkinsu, ta dauka takai ma Sultan nashi, dan shi kunyar Kausar din yakeji, bayan bakin cikin da danginshi suka kunsa ma Badiyya, but yasan bata fada mata ba.
Sun shiga dakin Badiyya kafin su kwanta, inda Kausar ke shaida mata akan gobe zata koma Kano, zata fadawa sauran yan uwanta, idan sun shirya zasuzo su duka, korata dakin Sultan tayi ganin da gaske anan zata kwana.
Badiyya taso hakan, dan dama akwai maganar da takeso suyi da Sultan din, tana shiga ta ganshi ya kwanta fuskarshi na kallon ceiling, zama tayi gefen gado, hakan yasa Sultan tambayarta ko lafiya, saidai amsar data bashi itace least abunda yayi expecting daga bakin Badiyya.
Kauda fuskarta gefe tayi, dan bataso tana kallonshi, hakan zai hanata aiwata abunda tayi niyya a cikin ranta. Dakyar kamar me tsoron magana ta fara magana "Sultan am, wallahi ina sanka, kuma karka dauki abunda zan fada maka da wani abu, dan Allah ka barni na tafi gida wajen Anty Kausar, kuma karka sake ka nemeni, danka ko yarka idan na haifa zan maido maka kamar yadda ka bukata."
YOU ARE READING
RAYUWAR BADIYYA ✅
General Fiction"Tun ina yarinya kike zagin mahaifiyata, tun bansan menene maanar kalmomin wulakanci da muzgunawa ba nakejin kina fadarsu ga mahaifiyata, ina cikin wannan halin wani azzalumi yaje ya kashe min mahaifiya, a gaban idona kika hana a tafi dani inda zanj...