Badiyya harta fara zuwa makaranta, har sun gama first semester. Kullum tare suke fita indai tanada lectures din safe, in kuma bata dashi saidai su fita tare ya ajeta office kafin lokacin, yanzu haka dai Badiyya an fara koyon mota, danshi yace bazai yarda wani katon banza ya dunga tuka matarshi ba.
Tana zaune bayan tayi lunch, Sultan yana wajen aiki sai missing dinshi take, ga wani tukukin bakin ciki data keji yana yawan taso mata? Hakanan ana zaman lafiya sai ta farajin haushi. Tana zaune tana kallo taji sallamarshi, dagowa tayi tana kallonshi hade da murmushi, har yazo ya zauna kusa da ita, lura da yanayinta yasa yayi magana "Debbo am, baki lafiya ne? Naga kinyi wani iri, kuma ko tarbata yau bakiyi ba," ya fada yana riko hannunta.
Kawai fashe mashi da kuka tayi, ita tama rasa haushin datake ji, kawai dai tasan ranta yana yawan baci, lallashinta yayi kafin ta fara magana, "Ni ko Sultan am, kaga dama tun tuni na fada maka cikina yana man tauri kamar dutse, amma sai kace babu komai, yanzu kuma ni hakanan sai naita jin haushi, kuma gashi naga cikina sai wani girma yake min, kuma fa har motsi nakeji Sultan am," kuka ta fashe dashi, rungume ta yayi, a ranshi kuwa ayyanawa yake karyarshi ta kare, dan tun ba yanzu yasan tanada ciki ba, amma gudun bala'inta yasa take shiru, kullim tazo mashi da maganar cikinta na mata wani abu sai ya bata magannin pregnancy care, amma yanzu karya ta kare.
Can tayi kukanta ta gaji amma Sultan baice mata komai ba, dago da kanta tayi idanunta sunyi jajir "Sultan am, kodai aljanu ne? Kaga yadda cikin ke juya min kuwa? Allah da gaske nake, kuma kaga sai kumburi yake man, kila kashe ni zasuyi, wayyo Sultan am bazan kara ganinka ba kenan?" Kankameshi tayi tana kuka haikan, Sultan dariya ya kusan yi mata, amma tuna bala'in dazai shiga idan ta gano cikin yasa ya danne dariyarshi, dan gara ya lallabata ko shima ta mashi da sauki.
Ganin dai da gaske kukan take taki tsayawa yasa Sultan ya fara magan "Badiyya, dan Allah kiyi shiru kinji? Ki daina kuka hakanan, maganar kumburin ciki da motsi ni ai likitane ko? Kuma ina baki magani, may be dai bakya shan maganin yadda ya kamata sai yasa har yanzu bai daina ba, kuma babu wasu aljanun da suka kamaki balle su kashe ki, ina tare dake, kuma kullun zaki rika ganini, kinji Debbo am?" Ya fada placatingly, yana goge mata hawayenta, Badiyya nodding kanta tayi kafin ta kara kwabe fuska.
Magana ta fara cikeda shawaga, tana saka hannayenta tana irga "Kaga ko Sultan am, Allah duk sadda ka bani magana sai nasha, kuma fa ni ba cikina kadai bane ba, ko ina na jiki ya kara kumburi, kuma na kusan 4 months banga period dina ba, nidai ma shiga ukku, kila shanye mani jin zasu farayi kafin su kasheni, shikenan nan bazanga auran Baby Moha ba (Muhammad kanin Sultan)" tukura Badiyya take kuka, ganin da gaske take yasa Sultan dauko wasu pregnancy pills din, ya mata addua cikin ruwa kafin ya bata, tanasha ne hankalinta ya kwanta, anan yaci lunch dinshi itama ta karaci, tana ta mashi complain yanzu tana yawan cin abinci ga kuma kwadayi dayake damunta, shidai Sultan babu baka sai ido.
***
Wajen karfe tara Badiyya tace ma Sultan tanajin bacci, cewa yayi su tafi daki, wanka ta shiga tayi sai kara nacin maganar take, shidai yayi nata shiru, dan duk adduar dazaiyi sai yasata a ciki Allah ya sauketa lafiya, salloli yasa sukayi kafin suka tafi suka kwanta, yunwa tace mashi tanaji, sai yaje ya dafo mata indomie.
Sun kwanta Badiyya ta dora kanta a chest dinshi tana wasa da hannunta, can dai tayi magana "Sultan am, Ina sanka wallahi, idan na mutu kafin Ikhlas tayi aure sai ka aureta kaji? Nasan ita kadai zata kula dakai sosai," ta fada murya can kasa, wani mugun kallo Sultan ya watsa mata, wanda hakan ya tilasta mata rufe idanunta, dan tasan fada zatasha.
"Badiyya menene haka, ba nace maki banasan maganar ba? Kuma babu mutuwar da zakiyi, lafiya lau zaki haifi babynki, ku rayu...." sai yau saurin gumtse bakinshi, dar dar yake Allah yasa bata gane me yake nufi ba.
Badiyya jin haihuwa da rayuwa yasa ta mike zaune, shima ya biyota "Sultan am, naji kace haihuwa da baby? Me kake nufi? Ciki gareni?" Ta tambaya tana kare mashi kallo, saurin girgiza mata kai yayi tare da hugging dinta.
"It was a mistake, ba ina nufin ciki ba, nine babynki mana, ko bakyaso ki rayu tare dani?" Ya tambaya yana kashe mata ido. Sauke numfashi tayi alamar relief, kafin ta kalleshi da murmushi kan fuskarta "Zan rayu dakai mana Sultan am. I was afraid ne, I thought ciki gareni, da rightaway zamuje a zubda shi, dan gara tun kafin yazo duniyar ya barta, bazan bari yazo duniya yasha azabar rayuwa ba, yanzu ma da aljanu kesan kasheni," ta karasa maganarta da alamun tausayi, shi kuwa Sultan kwata kwata komai tsaya mashi yayi, wat bala'i zata tada a zubda cikin ko me?
"Badiyya zubarwa kuma?" Ya tambaya haltingly, not very sure of his words. Daga mashi kai Badiyya tayi "Eh mana Sultan am, ko bazaka yarda ba? Kaga dana kawoshi duniya na barshi cikinta cikin bakin ciki ai gara in rabashi da ita cikin kwanciyar hankali," ta fada tana riko hannunshi alamar he should reason with her.
Jinjina kai Sultan yayi, yana mai hango riginar dake gabansa, dan ko giyar wake yasha bazai bari Badiyya ta zubda cikin ba, saidai ayita bala'i. Can kasan makoshi ya furta "Ai kuwa akwai rigima." Badiyya kallonshi tayi tace "Sultan am, ne kace?" Girgiza mata kai yayi alamar babu komai kafin ya jawota suka koma kan gadon, ta bude baki zatayi magana yayi saurin riganta "Badiyya, aljanu basasan ana hirar dare, kiyi shiru lets sleep," jin maganar aljanu yasa Badiyya saurin kulle idanunta, hankalinta kwance bacci yayi awon gaba da ita.
Sultan kuwa kasa runtsawa yayi, yana kwance amma barci ya kaurece ma idanshi, tunani yake duk ranar da Badiyya zata gane tanada ciki ba karamar masifa zaayi ba, dan kuwa saidai suyi sama su fado amma bazai taba barin ta kashe mashi yaro ko yarinya ba.
Ba'afi minti biyar da bacci ya kwashi Sultan ba yaji kakarin amai a falo, dafe kanshi yayi a hankali ya furta "Dakyar inba abunda nake gudu bane zai faru," cikin hanzari ya karasa toilet din ya tayata ta wanke bakinta kafin ya gyara wajen suka fito.
Ruwa ya debo mata ya bata, dakyar kamar tana saka guba taka tasha ruwan kadan, kallonshi tayi hawaye nabin idanunta "Sultan am, kuli nakesan ci kura kura, sai gyada soyayya da aya mai sugar, kuma ina san cin tuwo miyar alayyahu," ta fada tana tsareshi da idanunta cikeda hawaye.
Sultan kamar ya dora hannu saman kai, yanzu ina zai samu dukkan wadannan abubuwan? Gara gara ma tuwon zai iya girka mata, amma sauran fah? Tukuru. "Yanzu Badiyya dan Allah..." bai ida maganar ba ta tashi da gudu ta ruga toilet, binta yayi, nanma amai tayi kamar hanjinta zasu fita, gashi babu komai cikinta banda ruwa, karshen tausayi ta bashi shi.
Tana fitowa ta zube kan gadon "Sultan am, mu tafi asibiti, wannan aljanun kila so suke su kasheni, kaga idan mukaje akace babu abunda yake damuna sai in nemi duk abunda nakesan ci naci, kila kwadayi ne yake damunsu sukazo suka takura mani," ta fada tana mikewa tsaye dakyar.
Sultan saurin dakatar da ita yayi, "Badiyya, kinga nima ai likita, ki bari na diba ki please," ya fada yana marairaice fuska, kuka kawai ta fashe mashi dashi "Dama Sultan am nasan ba so na kake ba, ba ka dade kana bani magani ba amma ban warke ba? Kuma ko zaka duba ni ai baka da equipments din a gida, muje asibitin nidai, inba dama so kake na mutu," ta fada tana bubbuga kafarta ga kuka tanayi.
Sultan babu yadda ya iya haka ya dauki car key dinshi ya fita, ya kira lambar Dr. Aysha amma batayi picking ba, gashi ita keda duty yau, yasan dakyar in tafi gida yanzu, yau kam dole asirinshi ya tonu. Addu'ar Allah ya kawo mashi abun da sauki yake yi har suka isa asibitin, Badiyya babu abunda takeyi banda kuka.
Suna shiga taga Dr. Aysha, kasancewar sun saba kawai tayi gaba taje suka gaisa, office dinta suka shiga, anan take fada mata abubuwan har cikinta ta nuna mata, tambayoyi ta kara mata, ita kuma Badiyya ta saki baki sai bada amsa take, fatanta daya Allah yasa ba aljanu bane.
Dr. Aysha dariya tayi kafin ta kalli Sultan wanda duk ya gama tsurewa waje daya "Yanzu kai Dr ace matarka nada juna biyu amma baka lura ba? A matsayinka na gyneacolist? Anyway, may be soyayya ce ta rufe idon," ta fada tana yar dariya, sai kuma ta maida dubanta kan Badiyya, wacce tayi mutuwar zaune, indai ba kurunta kesan kamata ba to tabbas taji ance juna biyu, kuma juna biyu ai yana nufin ciki ko?
Kallon Badiyya Dr. Aysha tayi fuskarta a sake "Congratulations amarya, kina dauki da ciki almost za'ace wata biyar, dan gane da amsoshin da kika bani, but ki dawo ranar monday saboda a duba exact watan yar Dady ko dan Dady," ta fada cikeda zolaya, muryar nurses sukaji suna kiran sunan Dr. Aysha alamun an kawo emergency, da hanzari tabar office din bata jira amsar Badiyya ba balle Sultan.
Sultan dafa kafadarta yayi, tayi saurin juyowa da bloodshot eyes dinta wanda sun kafe, hawayenma basa fitowa, hannun taki kan cikinta "Na tabbata kasan da zaman cikinnan, amma ka sani, ina kan bakata, abunda na fada maka dazu tabbas shi zan aiwatar!"
YOU ARE READING
RAYUWAR BADIYYA ✅
Ficción General"Tun ina yarinya kike zagin mahaifiyata, tun bansan menene maanar kalmomin wulakanci da muzgunawa ba nakejin kina fadarsu ga mahaifiyata, ina cikin wannan halin wani azzalumi yaje ya kashe min mahaifiya, a gaban idona kika hana a tafi dani inda zanj...