Hankalin Sultan yakai kololuwa wajen tashi, yasan in Badiyya ta fara kukannan to fah babu sauran zaman lafiya, sai yanzu yake dana sanin aikata abunda yayi, yayi maganar har ya gaji akan tayi shiru amma taki, gashi har gari ya fara haske, ganin zata bata mashi lokaci, gashi ko wanka batayi ba balle maganar sallah.
Matsowa yayi kusa da ita ya sureta, sai bala'i take murya can kasa amma yaki kulata, gashi babu karfin yin cizo da shure shure da tayi, suna shiga toilet din ya ajeya ajeta cikin bath tub kafin ya kunna ruwan ruwan zafi ya sirka ta zauna a ciki, ihu ta tsala ta rike hannunshi gam, shi kuwa sai sannu yake mata, amma Badiyya yau ba baka sai ido kawai dake zubda hawaye.
Ganin ruwan ya salafce yasa ya tsiyayar da ruwan kafin ya hada mata na wanka "Debbo am, kiyi wankan tsarki da wanka kizo kiyi sallah," yana fadar haka bai jira amsarta ba, ganin wani mugun kallo data bishi da rinannun idanunta da tayi, fita yayi yana kara gode ma Allah da kuma rokon kar Allah yasa ta kara fushi dashi yanzu.
Badiyya a hankali hawaye nabin idanunta tayi wankan tsarki kafin ta dora da Alwalla, tana gamawa ta lura babu abun daurawa, wani shafin kukan ta kara budewa, towel ta hango anyi hanging dinshi, dauka tayi ta daura kafin a hankali tayi trudging out of the bathroom.
Tana fita taga new set of gown, ga underwears an aje mata akan gado, bedsheet din gadan ma an chanza shi, grimacing tayi kafin ta karasa ta zura kayan tahau kan sallayar ta tada sallah.
Tana gamawa taji ya shigo da tray din abinci a hannunshi, probably order yayi a hotel din, kauda fuskarta tayi ta cigaba da laziminta. Sultan rabowa yayi kusa da ita ya ajiye tray din, sannan ya zauna yana fuskantarta. "Debbo am, I'm sorry dan Allah, kici abinci, daga baya sai kimin duk hukuncin da zakiyi," ya fada yana marairaice fuska, hade da kura mata ido yana kallonta bako kiftawa.
Badiyya kauda kai gefe tayi wasu hawayen na zubo mata, tunowa da lokacin da take mashi magiyar yayi hakuri amma yaki, kallon fuskarshi kadai yanzu wani kululon bakin ciki yake tado mata.
Sultan yayi maganar har ya gaji, ita kuma Badiyya a cewarta tunda har tayita rokonshi yaki ji to bazata kara mashi magana ba. Sultan ganin sun bata lokaci a haka amma Badiyya taki kulashi, gashi an fara kiranshi a station din da aka kai Nabil akan suna nemanshi.
"Badiyya, ya kikeso nayi? Saboda na karbi hakkina kike fushi dani? To naji nayi laifi... dan Allah kiyi hakuri kici abincin, idan muka koma gida sai na baki magani kisha," Sultan ya fada a raunane, gaba daya komai ya jagule mashi, ya tsani shariyar da Badiyya ke mashi.
Yanzu ma banza ta mashi, ganin da gaske fah fushin take, "Yanzu Badiyya saboda abunda ya faru zaki halaka kanki da yunwa? kuma ko ki fadamin inda ke maki ciwo ko? Shikenan Badiyya, ko nima so kike na miki kukan sai kiyi hakuri?" Ya tambaya kamar zai kuka, Badiyya kara share hawayenta tayi kuma bata kulashi ba.
Sultan mikewa tsaye yayi "Badiyya indan abunda ya faru ne zaki halakamin kanki da yunwa ko? To Allah ya baki hakuri, zanje na auro wadda zata bani hakkina, kuma ta bari na kula da ita," yana fadin haka yayi hanyar fita, can kasan makoshi yaji Badiyya tayi magana "Zanci," ta furta. Hakan yasa wani murmushin jin dadi ya bayyana akan labban Sultan, dan yasan weak point din Badiyya to kishiya ne.
Dawowa yayi ya zauna ya fara bata abincin, a hakan ba kallonshi take ba, tura abincin kawai takeyi, dan tsananin kishinta yasa ma takecin abincin.
Tana gama cin abinci yace ta tashi su tafi gida ta huta, mikewa tayi tana dingishi, kokarin taimaka mata yayi amma ta buge hannunshi ta cigaba da tafiya a hankali har ta kai inda sukayi parking. Bude mata motar yayi ta shiga, sannan shima ya zagaya ya shiga tukun suka fita.
Suna isa gida a hankali ta shiga gidan, direct dakinta ta wuce bata jira shigowarshi ba, dan wani mugun bacci ne ke dibarta kamar wadda tayi shaye2, tana zuwa ta fada kan gado sai bacci.
Sultan shigowa yayi yaga ta kwanta, kofar yaja mata kafin ya rufe gidan ya tafi Sabon Gari police station, yana zuwa yaga wani Uncle din Nabil yazo akan zaiyi bailing dinshi, kuma iyayenshi sunyi waya zaa turashi Portharcout a yau din, dan har an mishi bookimg flight. Nan aka bada bailing shi tare da kashedin idan wani abu ya sami Badiyya to lallai shi zasu tuhuma.
Kafin Sultan ya dawo azahar tayi, takeaway ya musu kafin ya wuce gida, yana shigowa dakin Badiyya ya wuce, ganinta yayi kan sallaya ta kwanta, alamun bata da lafiya, karasa wajenta yayi ya dagota, zare jikinta da yayi rau saboda zazzabi tayi ta wuce ta hau kan gado hade da lullubewa da blanket.
Baice mata komai ba ya dauko takeaway din ya juye abincin cikin plate, ajewa yayi kan bed side drawer kafin ya zauna da niyar bata. Girgiza mashi kai tayi ta dauki abincin ta fara ci, har ta gama kallonta kawai yake, saida tasha ruwa ta koma kafin ya fara magana "Badiyya, dan Allah kiyi hakuri, ki fadaman inda yake maki ciwo, sai na baki magani, please mana Badiyya," muryarshi a raunane, maganarshi a hankali yayi yana kallonta.
Runtse idonta tayi alamar bacci kafin ta girgiza mashi kai alamar Aa, dan tayi alkawarin bazai ji muryarta ba, duk abunda yace tayi zatayi, amma bazai tabajin muryarta ba, tunda baiji muryar lokacin da take rokonshi ba.
Magana yayi tayi amma tayi shiru alamun bacci ya dauketa, ganin babu wanda zai taimaka mashi yasa ya dauki wayarta ya kira Ikhlas yace tazo Badiyya bata lafiya.
Matsowa yayi ya mata peck a goshi kafin ya fita dakin a hankali, Badiyya najin karar rufe kofa wasu hawaye suka silalo mata saman fuska, "Why Sultan am? I wasn't ready for that," a hankali ta cigaba da sobbing har bacci ya dauketa.
***
Gwaggo ce zaune tsakiyar falonta, ga karar wuta tanaji a makwabta amma gidanta babu,yan NEPA sun yanke, ruwa ma yan ruwa sun yanke gidanta, gashi yanzu tsabar shinkafa kadai ta rage mata, tunda Ahmad ya tafi bayan bikin Badiyya bai kara kulata ba, washe garin ranar daya tafi ma data kirashi sai cewa yayi da ita aka hada baki Badiyya ta auri Sultan.
Daga ranar ko ta kirashi baya dauka, tayi text din har ta gaji, yanzu kuma komai na gidan ya kare, gashi bata da kudi balle hanyar samunsu, awakanta ne kuma Badiyya ta sake su sun tafi. Yauma kamar kullun haka ta zauna bayan ta gama cin shinkafa da yaji zalla, sai dan mai, maggi ma ba kowane lokaci take samunshi ba, dan yanzu shine kadai abincinta.
Zama tayi a falo jugum, sai can kamar an tsikareta ta tashi ta shiga daki, wayarta da raban dataga kati har ta manta, wani yaro ta samu ya ciyo mata bashin MTN na dari biyu, shine take cincinawa tana kiran Ahmad amma baya dauka.
Dawowa tayi falon ta zauna, kafin tayi dailing numbershi, saida tayi kira kusan na biyar, har ta kusa katsewa sannan taji an daga, wani murmushin data dade batayi bane ya bayyana kan fuskarta "Hello Ahmad, yanzu dan nan ka kyauta kenan? Ka tafi ka barni kuma ina kira baka dauka? Baka damu kaji halin danake ciki ba ko Ahmad?" Muryarta har ta fara karewa, saboda tsananin bakin ciki.
Wani wawan tsaki taji anja "Dayake shi Ahmad din bawan kine, ko kuma kudinshi naki ne, ai dan iyalinshi yake nemo kudin badan ya kawo ma wata can ba, dan Allah malama tunda kinga kinata kira baa daukaba baki gajiya? Ko tsabar san cin kudin banzar ne? To shima yanzu Allah ya bashi iyali masu kishinshi da guminshi. Yanzu ma dauka nayi na maki warning akan karki kara kiranshi, tunda bake kika haifeshi ba," Adama na kaiwa nan ta kashe wayar tana jan wani tsakin takaici.
Gwaggo sakake tayi da wayar a hannu, tunani take anya wannan Adama ce kuwa? Amma kuma ai muryarta taji, kuma yadda take maganar inba matar mutum ba babu wanda zaiyi irin haka.
Kara dailing number tayi amma wannan matar me maganar kudi ta katse mata jin dadi😂 dole ta hakura ta sauke wayar a take ta saki wata uwar kara "Ni Binta na hado ma kaina bala'i."
Dan Allah ku rika voting da comment. Sannan kuma ku fadawa friends dinku su karanta, suma su fadawa friends dinsu. Nagode.
YOU ARE READING
RAYUWAR BADIYYA ✅
Fiction générale"Tun ina yarinya kike zagin mahaifiyata, tun bansan menene maanar kalmomin wulakanci da muzgunawa ba nakejin kina fadarsu ga mahaifiyata, ina cikin wannan halin wani azzalumi yaje ya kashe min mahaifiya, a gaban idona kika hana a tafi dani inda zanj...