BAYAN SHEKARA BIYU DA WATANNI
Zuwa yanzu Badiyya ta gama level 3 dinta as a law student, result suke jira, wanda a hakan ne aka tura su wani two weeks experience, wanda Badiyya sunanta ya fada a jerin list din yan Lagos.
Tana zaune ta tasa littafinta a gaba tana dubawa, Hilal ne ya rugo da gudu ya fada jikinta "Mum, kinga Dad da Heela sunata dukana ko? Kuma nayi ihu nayi kuka amma duk kika shareni Mum," ya fada yana rushewa da kukan shawaba. It has always been like that, Badiyya would be always backing him, shi kuma Sultan Heela is his fave.
A lokacin data ji ya fado jikinta tayi niyyar zare mishi ido saboda karatunta da yayi halting, amma yanzu jin hakan tasan Sultan rigimarta kawai yake nema, dan ya tabbatar suka fara wannan fadan to dole taje ta shiga, inba haka ba babu sauran zaman lafia.
"Ahhh my little hero, abunda Dad din ya maka kenan? Bari muje, ita kuma twin sis munyi fada da ita," Badiyya ta fada tana tattare littatafan dake yashe a gabanta kafin ta mike.
"Yauwa Mum dina, that's why I always love you," Hilal ya fada da gwari-gwarin maganarshi yana kama hannunta enthusiastically kafin suka fito daga dakinta.
Suna shiga playroom din taga Sultan a baje yana hadama Heela puzzle, alama tama Hilal da hannu alamun suyi shiru, kafin sukaje inda balls din wasansu kanana suke suka dauko. Gaba daya suka juye kwandon kananin balls din jikin Sultan da Heela.
A take suka kwatsa karar jin tsoro, inda Badiyya da Hilal suka kwashe da dariya hade dayin thumbs up. "Yes! Aren't you the best Mum on earth?! And you twin sis, kaima Dad, ga brave Mum dina nan sai kuyi abunda zakuyi," Ya fada yana daka tsalle hade da nuna dan karamin damtsen hannunshi.
Wawuro su Sultan yayi amma Hilal ya kwafce, sai dai ya kamo Badiyya ta fado jikinshi, duka yaran suka fashe suna dariya. Hilal ya mika ma Heela hannu suka tafa yace "Dad ya kama Mum, the war will soon start," a tare suka fashe da wata dariyar.
Badiyya kallon mamaki tabishi dashi, lallaima yaronnan, abunda zaice kenan ma? Wato twin sis dinshi ta fita kenan. "Kai Hilal, haka mukayi dakai? Zoka taimaka min joor, see this boy," ta fada tana kokarin kwatar kanta daga rikon Sultan.
Hilal side hugging Heela yayi "Noo Mum, bakiga Dad yafini karfi ba? I won't embroil myself in this, yana iya markada mu," ya fada yana dariya.
Karfi ta saka zata kwace kanta amma Sultan ya murde hannun cikeda mugunta yana dariya, kara ta saki da biyu dan ta basu tsoro, aikuwa nan Heela ta fizge daga jikin Hilal ta rugo wajen, damtsen hannun Sultan ta rike ta fara ja "Dad, ka saketa mana! Nayi hakuri fah. You're hurting her please," ita bil haqqi janye Sultan take daga rikon dayayi ma Badiyya.
Dariya Sultan ya kwashe da ita "Heela? We're no more on the same team kenan? Oya! Hilal janyeta agun, karka barta tazo nan harsai Mum dinku tayi kuka," ya fada yana kara rike Badiyya, wadda was doing all her might taga ta yakicema rikonshi.
Nanfa abu ya tashi, sai Heela tazo zata gartsama Sultan cizo sai Hilal ya tashi. "Mum, be strong ok? Don't cry, we have to show them how brave we are! Dad Allah ka saketa," ta fada da karfi tanata kokowa da Hilal wanda shima ya mata mugun riko.
"I won't my baby, barni dashi. Kai kuma you should let her go, inba haka ba Hilal nazo nan zaka sani," Badiyya ta fada tanata maida numfashi, ita mamaki take yadda take gaba daya Sultan ya sakar mata karfinshi dan mugunta.
"Kai Hilal, don't even lose the hold balle maganar saki, they have to cry before we can let them go," Sultan ya fada yanata dariya, Badiyya thought she might take advantage of him; hakan yasa takai bakinta daidai wuyanshi, saurin janye kanshi yayi.
"Ohh baby, if that's what you want, we can call the game off," ya rada mata a kunne hade dayi mata wink. Harara ta balla mashi tana kallon wajen su Hilal, nan Heela ta samu ta bigeshi ta rugo.
YOU ARE READING
RAYUWAR BADIYYA ✅
General Fiction"Tun ina yarinya kike zagin mahaifiyata, tun bansan menene maanar kalmomin wulakanci da muzgunawa ba nakejin kina fadarsu ga mahaifiyata, ina cikin wannan halin wani azzalumi yaje ya kashe min mahaifiya, a gaban idona kika hana a tafi dani inda zanj...