Sultan bai jira wani karin bayani ba yasha round about suka koma inda Ahmad yake kallo, zufa ta ko'ina sai keto mashi taki. Suna zuwa ko jira ya ida samun wajen parking Ahmad baiyi ba ya balle marfin motar ya fice daga, gudu gud sauri sauri haka yake har ya karasa wajen matan dake zaune, sun zagaye wata guda daya wadda take fitar da numfashi a wahalce.
Bubbuge su yayi, kafin yana zuwa ya dago fuskarta, saida ya tabbatar ita dinta kafin ya fashe da wani kuka mai tsuma zuciya, "Mai ya sameki haka? Ashe rayuwa bani kadai ta wujijjiga ba? Meke faruwa damu ne?" Tambayar da yake ma kanshi kenan, yana tallabo Gwaggo daga kwancen da take cikin kasa.
Daya daga cikin matan gurin ce ta fara magana cikeda masifa "Malam lafiyarka kuwa? Hakanan daga zuwa ka riko matar da ba taka ba, kanata kuka. Ko dai daga asibitin mahaukata ka fito?" Tana fadin haka ta fara janye Gwaggo daga Rikon Ahmad.
Kafin Ahmad yayi magana, Badiyya da Sultan sun karaso. Badiyya ce tayi saurin karasawa wajen "Dady lafiyarka kuwa? Ji fa inda ka zauna, kuma ka rike wannan matar. Ka santa ne?" Ta tambaya tana kokarin yakice Gwaggo daga rikon Ahmad din.
Dagowa yayi hawaye na zuba a idanunshi "Yaya ce fah Badiyya, Yaya ce, a mother material to me," ya fada, sai a lokacin ma ya lura da idanun Gwaggo da suka kakkafe, alamar kila ganinshi ne ya samata cikin wannan halin. Dama ya lafiyar giwa.
"Sultan! Kawo mota mu tafi asibiti," abunda ya fada kenan da tsananin kara. A rude Sultan ya janyo motar zuwa kuwa dasu, da taimakon Sultan Ahmad ya saka Gwaggo a bayan motar, inda twins da Nana suke mata kallon mamaki. Itadai Nana gani take kamar tasan matar, dan kuwa akwai ta da rikon fuska.
Basu zarce ko ina ba sai General hospital, dan kuwa a yanayinta da Sultan ya gani yasan general ne kawai zasu samu specialized doctors cikin gaggawa. Suna shiga kuwa aka karbeta, emergency room suka shiga da ita.
Ganin an kusa awa daya doctors din basu fito ba, ga twins da Nana duk sun wani ya kwane alamar yunwa, sai yasa Sultan kiran Khalil akan yazo ya kaisu gida, idan sun gama zasu biyo su daukesu.
Khalil na zuwa ya hango Nana rabe jilin Ahmad, kallon tsoro takema kowa, gaba daya jikin ya mata sanyi, gani take kamar wani abu zai faru. Sai da suka gaisa dasu Ahmad da Badiyya kafin yaja hannun twins sukayi hanyar fita, har zasu wuce ya juyo ya kalli Sultan "Yaya, ita waccan banda ita ne?" Ya tambaya yana kallon Nana. Yarinyar gata da kyau, amma yadda tayi shiru sai ta bashi tausayi.
"Tashi ku tafi kinji Nana? Yanzu zamu zo muma," Ahmad ya fada yana mikar da ita tsaye. Babu musu ta mike tana kallon Ahmad, hawaye sun taru a idanunta "Dady, tun ranar da Mama ta ajiyeka a irin wannan wajen ban kara ganinta ba, kuma inaso na ganta," tana furta hakan bata jira amsarshi ba tayi gaba. Dan kuwa ta saba dajin amsar dazai bata.
Koda suka shiga mota shiru tayi tana share hawayenta, kallonta kawai Khalil yakeyi, amma gaba daya yarinyar ta bashi tausayi. Can dai ya mika mata handkerchief dinshi "Karbi ki goge hawayenki, beautiful girls basa kuka, unless idan kinaso ki zama ugly," ya fada hankalinshi yana kan tukin dan yakeyi.
Karbam handkerchief din tayi, tana mishi wani puzzled look, da alama maganarshi ta shige ta "Da gaske kake? Dady once said I'm a beautiful girl, I'll marry a handsome guy. To yanzu tunda nayi kuka I won't marry him kenan?" Ta tambaya tana turbune fuska, dan ita har ga Allah ta dauki maganar da gaske.
Saida yasa roundabout kafin ya juyo ya kalleta, a small smile creeping out of his lips. "Ai a yanzu haka you're beautiful, just don't cry anymore, if not; handsome guys like me wouldn't marry you," ya fada hana daga girarshi, alamar da gaske yake, ganin irin kallon tsoron data mishi.
"You're a nice person ai, sai ka aureni even if na zama ugly girl, infact bazan kara kuka ba," tana fadin haka ta goge sauran hawayenta, forcing a smile on her face.
YOU ARE READING
RAYUWAR BADIYYA ✅
General Fiction"Tun ina yarinya kike zagin mahaifiyata, tun bansan menene maanar kalmomin wulakanci da muzgunawa ba nakejin kina fadarsu ga mahaifiyata, ina cikin wannan halin wani azzalumi yaje ya kashe min mahaifiya, a gaban idona kika hana a tafi dani inda zanj...