Firdausi dakyar ta bude idonta, tana budewa taga gari ya fara haske. "Innalillahi." Ta fada, hade da daukar wayarta ta duba taga karfe shida da rabi na safe. Da hanzari ta tashi taje tayo alwalla tazo ta kabbara sallar Asuba, tana gamawa ta tashi tayi hanyar kitchen. A kan hanya ta hadu da Ahmad ya dawo daga masallaci, dabi'ar shi ce baya dawowa sai haske ya fara fitowa. Indai kan sallah ne, to sai kace Ahmad yafi kowa imani.
Da sauri ta dauke idonta daga kan fuskarshi, sai taga ya kara mata kyau. Tunda take bata taba jin soyayyar Ahnad a ranta ba irin ta yau, ya kara mata kyau da kwarjini. "Lafiya ta kuwa? Wannan irin so ne haka tunda asubar fari?" Ta tambayi kanta, a yayinda take shiga kitchen.
Tana cikin kitchen taji fitowar Badiyya, domin ta saba dukda weekends ne bata wani barcin kirki.
"Momy ina kwana?" Badiyya ta fada tana me rungume Mahaifiyarta.
"Lafiya lau, My Bady, bari in hada maku coffee keda Dady ko?" Ta fadi hade da ajiye doyar da take ferawa ta dauko coffee maker.
Shan coffee ya zamanma Ahmad da Badiyya jiki, dama shi ya koya mata. Bacin Firdausi tai masu da gaske da sun zama addicted to it, amma yanzu duk weekends sai sunsha.
Badiyya nanan tsaye har ta gama ta miko mata. "Kibi a hankali, karki kone." Ta fada mata, hade da mika mata cups din. Badiyya a hankali tai prowling zuwa parlour, inda ta iske Ahmad ya kunna TV yana kallon Morning News.
Sai data ajiye cups din a center table tukun ta dago fuskarta cike da murmushi. "Dady ina kwana?" Ta fada hade da miko mashi coffee shi. "Ga coffee musha, kaga jiya dama bamu sha ba." Ta fada hade da yar dariyarta, domin ta tuna yadda sai sunyita rokon Firdausi tukun take hada masu.
Yar dariya yayi, shima moments din suna dawo mashi cikin kai, haka suka zauna suna kallo sunashan coffee su.
Sai wajen bakwai da rabi na safe tukun Firdausi ta gama. Ladi me aiki bata nan taje gida, diyar kanwarta ta haihu.
Saida Firdausi ta gama jere kwanukan a saman carpet, yau a kasa zasuci abincin. Kamar yadda suka saba yi lokacinda rayuwarsu tana daidai.
"Ku sauko muci." Ta fadi tana murmushi, har cikin ranta yau takejin soyayyar Ahmad, ta rasa miye dalilin hakan. Shima yau ba laifi ya saki fuskarshi, ba kamar jiya ba.
Basu ce komai ba suka sauko kasa sukaci abinci, bayan sun gama breakfast Ahmad ya nufi hanyar dakinshi da niyar yin wanka. Badiyya ta mike hade da fadin, "Momy bari naje nayi wanka." Tana me nufar hanyar dakinta. Firdausi daga mata kai kawai tayi, ta nufi hanyar dakin Ahmad.
Tana shiga taganshi bakin gado yana waya yana murmushi, wani bakin ciki ne taji yazo mata a wuya, dukda bata da tabbas din dawa yake magana. Bata ce komai ba, tayi hanyar toilet ta hada mashi ruwan wanka ta dawo bakin gadon ta zauna.
Baice mata kala ba ya tashi ya shiga ya watsa ruwan, yana fitowa yaga ta fiddo mashi da kayanshi. Ya saka kayanshi yai hanyar fita, Firdausi tabi bayashi har yazo bakin kofa baice mata komai ba.
"Dady, dan Allah inaso na kara zuwa gidan gaisuwa." Ta fada a dardare.
"Na hanaki zuwa ne?" Ya fada, yana mata wata irin harara.
"Aa." Ta fada, kanta na kallan kasa.
"Karki dauki maganar dana gaya maki jiya a matsayin wasa, inhar baki bani ba.... hmmm." Ya furta hade da yimata wani kallo, sannan ya fita ya barta tsaya kamar gawa. Ita wallahi ta rasa ya zatayi.
Firdausi ta shiga dakin, ta fada ma Badiyya ta fito su tafi; domin tanaso taje gidan Yaya. Yaya itace kadai Yayar Ahmad, wajenta ya taso bayan iyayensu sun rasu.
Badiyya cikin hanzari ta shirya, domin tanasan gara ganin Sultan am, tasan koba komai zata debe mashi kewa.
***
YOU ARE READING
RAYUWAR BADIYYA ✅
General Fiction"Tun ina yarinya kike zagin mahaifiyata, tun bansan menene maanar kalmomin wulakanci da muzgunawa ba nakejin kina fadarsu ga mahaifiyata, ina cikin wannan halin wani azzalumi yaje ya kashe min mahaifiya, a gaban idona kika hana a tafi dani inda zanj...