Rayuwace me aminci cikeda girmamawa hade da soyayya Badiyya da Sultan ke shimfidawa cikeda soyayya mai karfi. Yau ta kama lahadi, Badiyya ta tashi da safe, duk tayi wani fresh tayi kyau da ita, kallon gefenta tayi taga Sultan na shakar baccinsa hankali kwance, tunowa da muguntar daya mata jiya yasa tayi kwafa hade da murmushin mugunta itama.
Saitin kunnenshi takai bakinta, can kuma ta kurma wata uwar kara, a firgice Sultan ya farka, tana ganin ya bude ido itama tayi karar hade da wuntsilawa ta fita dakin da gudu harda haki, dan tasan idan Sultan ya riketa abun bazai mata kyau ba.
Sultan kuwa abunma dariya ya bashi, da ya bude ido da niyyar yi mata bala'i, amma ganin yarda ta zabura ta fita da uban gudu sai abun ya bashi dariya. Kwafa yayi ya furta "Yarinya zaki gane kurenki," yana fadin haka ya shiga toilet danyin wanka.
Badiyya kuwa tana fita ta shiga dakinta hada kullewa, toilet ta fada tayi wanka sharp sharp, kafin ta fito domin hada masu breakfast, dan yau so take suyi aikin gidannan, dan rabonshi da general cleaning an dade.
Tana fitowa cikin sanda ta fada kitchen, aikinta ta fara cikeda farin ciki, amma kasan ranta tsoro ne fal, dan tasan sarai Sultan ba kyaleta zaiyi ba, dan ya tsani a bashi tsoro.
Sultan yana fitowa yaga tana aiki, kana ganinta kasan a tsorace take, lallabawa yayi shima, saidai kawai taji an rike mata hannu gam "Kin gama gudun?" Ya tambaya yana tsareta da idanunshi, Badiyya ganin babu digon wasa idonshi yasa jikinta ya fara rawa.
"Sultan am dan Allah kayi hakuri, wallahi wasa nake maka, please," duk ta rude, she knew not to act obnoxious in har yayi making irin wannan fuskar, babu wasa a tattare dashi.
Kara shawabe fuska tayi "Sultan am mana, dan Allah fa nace," amma Sultan kallonta kawai ya tsaya yanayi, shi ganin yadda ta rude ma sai yaso bashi dariya, amma a hakan ya fuske.
Badiyya ganin babu abunda zaisa ya saketa, sai yasa kawai ta kankame shi, dan tasan hakan ne kawai weak point dinshi, shi kuwa Sultan jin tayi hugging dinshi yasa ya saki hannunta, yana shirin hugging dinta tayi saurin janye jikinta ta ruga da gudu tana kyalkyacewa da dariya, shima biye mata yayi.
"Nayi ma Sultam am wayau, mmmmm," ta fada cikeda jin dadi hada mashi gwalo, harda yar rawarta.
Sultan saida yayi dariya kafin daga baya ya gimtse, amma dukda haka fuskarshi cikeda take da dariya. "Debbo am, kizo nan Allah, kinsa man rai, kuma baki isa ba," ya fada yana fitowa daga kitchen, iske ta yayi tsaye ta kasa saisaituwa, dariya ma ta bashi amma ya gumtse.
"Ki wuce ki idasa abunda kikeyi," ya fada with stern face, kamar yace ar aikuwa Badiyya ta zura da gudu, sai dakinta ta rufe. "Sultan am, kasan Allah bazan fitoba, mugunta zaka mani, kaje kar abincin ya kone," batayi auni ba taji Sultan daidai kofarta yana bugawa. "Badiyya kinsan Allah ki fito, if not yau zakiyi bayani."
Badiyya najin haka ta kurma ihu, "Wayyo sultan am, girkina ya kone! Kaje ka dibo sai kazo ka kirani," Sultan najin haka ya wuce kitchen din, dariya kawai yake, dan wani lokacin drama Badiyya tana bashi mamaki.
Kitchen din yaje ya kashe gas din ya shirya dining kafin yaje dakinshi ya dauko extra key, yana zuwa ya bude sai ya ganta zaune bakin gado tana shan ruwa, kallonta ya maze "Ki fito toh,"yana fadar yayi gefe alamun tazo ta wuce.
Badiyya ganin yadda yayi da fuska yasa tayi hanyar kofar sum sum, tana zuwa kusa dashi ta zura da guda, dariya kawai yayi ya bita, yana fita falon ya ganta tana serving dinsu, zama yayi suka faraci. Suna gamawa Badiyya ta kwashe kayan ta tafi kitchen, sai ta kwala mashi kira "Sultan am, kazo muyi wanke wanke, kuma zamu gyara gidan duka," tana fadar haka ta cigaba da abunda take.
Sultan kuwa shigowa yayi kitchen din hannunshi cikin aljihu yana kare mata kallo, saida yazo kusa da ita ya tsaya yayi gyaran murya, Badiyya ta juyo a tsorace sai kuma ta maze.
"Ka taho ka fara aikin mana, ji Sultan am fa," ta wani hade rai kamar da gaske, tana nuna mashi kwanunkan.
Juyo da ita yayi tana fuskantarshi kafin yayi magana "Ai baki isa ba, bari inyi aikina kafin na tayaki," bai jira amsarta ba ya hade lips dinsu waje daya, saida yaga Badiyya tana karbar sako babu kamu hannun yaro kafin ya saketa cikeda mugunta, juyawa tayi ta cigaba da aikinta tana bata fuska, dan tasan da gayya yayi.
Shi kuma dariya yayi a haka suka gama wanke wanken suka gyara kitchen din, suna gamawa yaje falo ya zaune, zuwa tayi ta tsaya mashi tsakar kai, kallon lafiya ya mata, ita kuwa harda rike kugu, "Ka tashi gidan zamu gyara ko, ji Sultan am dinnan, ni bance nagaji ba saike, ga arzikin mugunta ga laziness," ta fada cikeda tsiwa, dan kuwa taji haushin abunda ya mata dazu.
Sultan dariya yayi "Indai kinaso na tayaki aiki to sai kinman abu," ya fada yana kanne mata ido.
"Fada naji menene, sharp sharp Sultan am, rana nayi fah, in mukayi baki fah," ta fada tana wani karkada kafa alamar sauri take. Mikewa tsaye Sultan yayi, "I want a kiss a nan," ya fada yana nuna labbanshi.
Da har ta tsaya tana kallonshi sai kuma tayi dariya kasa kasa, "Yanzu Sultan am saboda tsabar rashin kunya ga rana gatse gatse kake maganar iskanci? Allah ya shirya ka," sai kuma ta fashe da dariya, shima dariyar yayi, "bari dai na taimaka ma poor soul dinka," tana fadin haka tayi leaning in ta fara kissing dinshi, saida ta lura ya saki jiki sosai ta dage ta gantsara mashi cizo, kafin ta ari na kare.
Tana dariya ta ruga da gudu, "Haka kamin dazu, nima na rama, kuma Allah kazo muyi sharar nan," tana fadin haka tayi wajen daukar tsintsiya.
Sultan smirkimg yayi "zakiyi bayani anjima Allah, sai kinyi kuka," a haka yaje suka fara aikin, da taga yazo kusa da ita zata ruga, cikeda dariya da annashuwa suka gaba aikace aikacensu.
***
Bayan Sallar Isha'i Badiyya sunci dinner Sultan yana aiki a falo ita kuma ta shigo daki yin sallah, daga nan ta hige dayin game, saiga kiran Ikhlas ya shigo, inda take fada mata akan yau aka saka ranarsu iyayen Abdallah sukazo neman aure, sai ihu take tanajin dadi, ita ganin abun ma take kamar a mafarki.
Fita tayi falon dan ta fadawa Sultan, tana zama kusa dashi amma yaki kulata, buge kafadarshi tayi tana bata fuska "Kai Sultan am, nazo maka da gulmata shine ka wani shareni ko? Yayi."
"To yi hakuri kayan Sultan am, fada mani insha, hope dai gulmar me zafiiii ce🔥🔥🔥," ya karashe maganar yana dariya, Badiyya itama dariyar tayi "Kai Sultan am ka bani kamar wata mace wai."
"Ya bazan iya gulma ba ina tare da mace," dariya dukansu sukayi kafin ta bashi labari akan Abdallah ya turo, nandai har sun gama sai mood dinshi ya koma serious one. "Badiyya, dauko man slips din WEAC da JAMB dinki, an fiddo result din WEAC, JAMB kuma zamu diba admission status dinki," yana gama fadar haka cikin Badiyya ya kada, yanzu idan bataci bafa? Shikenan bazata zama lawyer ba? Bazata kwatar ma Momy da Anty hakkimsu ba?
Jiki ba lakka ta dauko, dama daga baya Ikhlas ta kwaso mata komai nata, mika mashi tayi ta zauna dabas kusa dashi, ta bashi dariya da kuma tausayi. Website din ya shiga ya duba WEAC din sai kuma ya dubo admission status dinta.
Ganin ya aje papers din gefe yasa Badiyya tunanin ko bataci bane, a dardare ta riko hannunshi, fuskarta ta nuna alamun kuka "banci ba ko Sultan am?" Ta tambaya, sai ga hawaye shar shar nabin kuncinta.
Dagowa yayi ya kalleta, "I'm sorry to say Badiyya, amma bakiyi passing ba," bai ida maganar ba ta rungumeshi sai hawaye shar shar ke zuba "Yanzu shikenan bazan neman ma Anty da Momy hakkinsu ba? An kashesu a banza kenan?" Sai kuma ta fashe da kuka.
Dariya ya farayi, hakan yasa ta dago ta kalleshi, "I'm very proud of you Badiyya, kinci plat B, kuma an baki admission Law a UMYUK," ya fada yana dariya.
YOU ARE READING
RAYUWAR BADIYYA ✅
Fiksi Umum"Tun ina yarinya kike zagin mahaifiyata, tun bansan menene maanar kalmomin wulakanci da muzgunawa ba nakejin kina fadarsu ga mahaifiyata, ina cikin wannan halin wani azzalumi yaje ya kashe min mahaifiya, a gaban idona kika hana a tafi dani inda zanj...