BABI NA SHIDA

4.5K 378 2
                                    

A haka a rungume suna kuka har Badiyya tayi barci, bayan Firdausi ta tabbatar baccin yayi nisa, sai ta dauketa ta ajiye kan gado.

Ta dawo ta cigaba da hada kayan Badiyya, tana yi tana kuka. Ita yanzu in tace ta koma Kankia ya zata yi? Aikin ta fa? Wanda tasan shi zai rufa masu asiri, dukda Allah nanan.

Lokacin data gama hadan kayan Badiyya tsaf, har daya na dare tayi. Batabar ko tsinke a wajen ba, saboda bata da niyyar dawowa gidan, koda taso hakan; bataga alamun hakan a idon Ahmad ba.

A haka ta tashi ta wuce dakinta, ta janyo troleys dinta ta shiga hada nata kayan, bata gama ba har saida ukku na dare tayi. Tana gamawa taje dakin Badiyya.

Data shiga dakin, ta hango Badiyya ta makure, daga gani baccin bana kwanciyar hankali bane. Zama tayi gefen gadon ta kurama Badiyya ido, domin tana tausayin yarinyar, ita yanzu ta fara rayuwa. Ita tayi yarintarta cikin aminci da kulawar iyaye, amma Badiyya bata samu hakan ba, tun tana yar kankanuwarta damuwa ta fara samun mazauni a cikin zuciyarta.

Da taga zaman bazai amfaneta da komai ba, saita tashi ta dauro alwalla, tazo ta tada sallah, tanayi tana kuka. Ita yanzu ya zata yi? Ba Baba, ba Mama, kannenta duk matane, kuma kowacce na gidan mijinta, kaninta daya; Musaddiq, shima yarone.

Tana nan zaune tana karatun Al-Qurani, in abun ya tunkuro mata sai ta tsaya tayi kuka iya yinta, sai ta gaji dan kanta sai ta cigaba. A haka har aka fara kiraye-kirayen Sallah.

Ta tashi daga zaunen da take, ta tada Badiyya domin ta gabatar da Sallar Asuba su tafi; bataso gari ya waye masu cikin wannan bakin gidan, wanda ba komai cikinshi sai bakin ciki ta takaici.

Badiyya na farkawa, ta tsaya tana kallon mahaifiyarta; wadda a yanzu har idanunta sun fada. "Momy zamu tafi din?" Ta fada, daga yanayin da maganar ta fito za'a gane da abun ta kwana cikin ranta.

"Badiyya na fada maki tun jiya ai ko?" Firdausi ta fada tana mai mikewa tsaye, domin batason yarta taga weak side dinta. Not in this kind of situation. "Ki tashi kiyi Alwalla, kizo muyi sallah." Ta fada, tana komawa saman dardumar; hade da cigaba dayin lazuminta.

Badiyya batace komai ba, domin yanzu yawan damuwa yasa ta fara gane yanayin mutane, a lokacin da mutane kesan magana da lokacin da basu so.

A hankali ta turo kafar bayin, tana fitowa ta hango kayanta hade da hijab dinta; daga gani su Momynta ke nufi zata saka yau.

Daukar hijab din tayi hade da fadin. "Momy mu fara." Firdausi bata ce kala ba, ta mike suka tada sallah.

Suna gamawa Firdausi ta kalleta cikin kulawa. "Badiyya, kije kiyi wanka, yanzu zamu tafi." Ta fada, tana kallonta cikin sigar damuwa.

Badiyya ta turbune fuska, "Momy, mu bari sai gari yayi haske." Ta fada, idanunta na kawo ruwa. "Kuma bazanje makaranta ba?" Ta tambaya, alamun rashin jin dadi a maganarta.

"Zakije Badiyya, yanzu so nike inje in nemi transfer." Ta fada mata, domin ta kwantar mata da hankali. "Ki tashi, kinga Dady yace karmu kai karfe tara. Kuma kinga kema karki makara school." Ta fadi tana yin hanyar waje.

Badiyya ta mike zata cire kayanta. "Momy ke ina zaki?" Ta tambaya. "Zanje na hada maki breakfast, kafin ya dawo." Ta fadi tana rufo kofar dakin.

A haka Badiyya ta shiga shiga wanka, tana fitowa taga ba uniform dinta, data duba inda ta saba ajiyesu sai tagani. Ta tabbatar Firdausi mantawa dasu tayi da tasakasu cikin akwati.

Firdausi tana fita ta kira Malama Rukayya ta fada mata, domin mijinta a ministry of education yake aiki, taji ko zata samar mata da transfer. Aikuwa cikin sa'a aka samu, tace dama ana neman teachers a Dutsin-ma sai dai nan gaskiya. Wanda ita Firdausi ba haka taso ba, taso ace ta samu Kankia. A haka dai ta mata godiya, wanda ita Malama Rukayya ta shaida mata zuwa gobe transfer zata fito.

RAYUWAR BADIYYA ✅ Where stories live. Discover now