Badiyya suna fitowa ta kamo hannun yan biyu sukayi wajen claimimg bags, suna daukar troleys dinsu, inda yan biyu keta rigama kowa saiya dauki nashi, wanda iri dayana kanana, saidai bambancin colour.
Barinsu tayi suka dauka, suna fita saiga Musaddiq shida matarshi Sa'adatu sunata murmushi, da gudu yaranshi sukaje suka rungume Badiyya, wadda ita jikinta har zillo yake dan ta ganta kusada uncle dinta.
"Uncle, nayi missing dinki," Badiyya ta fada, slightly hugging him. Murmushi yayi ya janyo hannunta suka karasa mota, ita kuma Aunty Saadatu ta janyo Yan biyu, dan tasan yanzu wadancan biyun basuda lokacin kowa.
A mota sai labari suke kamar wanda sukayi shekaru basu hadu ba, ita kuwa Aunty sa'adatu ta kama yan biyu sunata mata surutansu, mostly maganar duk ta Dad dinsu ce. A iyakar ganinta da dangin Musaddiq, zata iya cewa gaba dayansu kwallafa rai ga yan'uwa garesu, kuma suna matukar kaunar junansu.
A haka suka karsa Apapa, inda nan gidanshi yake. Suna shiga Badiyya sai yaba kyawun gidan takeyi, aka kaisu dakinsu, su kuma yan biyu suka wuce dakin yaransu suma. Badiyya wanka tayi, tana fitowa taga wayarta na ringing, da murmushi kan fuskarta ta dauki wayar "Sultan am, nayi missing dinka wallahi," ta fada tana wani shagwabe murya, dan kuwa ba karya tayi missing dinshi. A tsarin rayuwar hausawa, idan kunyi aure da yan shekaru, to nanfa zaku daina kula da juna, amma a bangaren rayuwarsu Sultan ba haka abun yake ba, dan kuwa kullum jin soyayyarsu suke sabuwa.
"Badiyya anya bazanzo gobe ba? A goben ma jirgin safe? Kinji yadda nakeji kuwa? God! Bazaki gane ba. Kamar in rasu," his voice was laced with sincerity and joke.
Dariya ta kwashe dashi, dan kuwa tasan ita yake koya, domin sarar ta ce cewa 'kamar in rasu', "Allah sarki Sultan am, twins ma tun dazu maganarka suke. Ba jibi friday ba? Sai ka biyo jirgin yamma ai, ka tsaya kayi aikinka kaji? Haba handsome doctor," yadda tayi maganar sai ya bashi dariya, dariya yayi sosai itama tana biye mashi.
"Tohm Maman twins, yanzu ina fighters dina? Basu naji, ke kin tsufa ai," da dariya cikeda tsokana yayi maganar, amma hakan bai hana Badiyya turbune fuska ba.
Ringis ta kwanta kan gadon, sanyi sanyin garin dana AC yana dukanta, hade da soothing duk wata gajiyar dake jikinta. "Kai Sultan am, nice tsohuwa? Yanzu ace zaka barni nayi shigar yan mata na ratsa titu, ho! Da kaga yadda zanyi kasuwa," cikeda rashin ji da neman ramawa tayi maganar, aikau ta hassala shi.
"Kinsan Allah Debbo am, zama kija in taho gobe, dama ga yarabawan nan ba kwakwalwar fahimtar matan aure da yan mata garesu ba, kuma ni dama Badiyyata bawai kama take da matan auren ba. Allah sarki Sultan dinsu," ya fada cikin sigar tausayin kanshi, Badiyya kuwa me zatayi inba dariya ba. Sosai take darawa, bawai dan abinda yace kadai ba, sai hada Sultan dinsu daya kira, sai ya tuna mata da Ikhlas.
"Kasan Sultan am, da kace Sultan dinsu sai ka tuno mani da Ikhlas, itace duk bala'i bata iya cewa Sultan am, wai ai nawane, saidai Sultan dinsu," ta fada tana kwashewa da dariya, tunowa da dramas dinsu ita da Ikhlas takeyi.
Saida yayi dariyar shima kafin yace "Allah sarki Ikhlas, tun last zuwan da sukayi raban da nakara ganinsu, koshi Abdallan yabar kirana, ai na gama mashi amfani."
"Kai Sultan am, kila hidimace ta rikesu, tama kusa haihuwa nakega. Though nima mun dade bamuyi magana ba, tunda tayi aure yarinyar nan ta rage kirana," Fadar Badiyya, idanuwanta har wani lumshewa suke saboda kauna da kuma bacci.
"Ahh kaiji Debbo am, Auren ne yake mata sugar," fadar Sultan yana kwashewa da dariya.
Dariya Badiyya tayi hade da girgiza kai "Kasan Allah Sultan am? Bakajin magana ko kadan."
YOU ARE READING
RAYUWAR BADIYYA ✅
General Fiction"Tun ina yarinya kike zagin mahaifiyata, tun bansan menene maanar kalmomin wulakanci da muzgunawa ba nakejin kina fadarsu ga mahaifiyata, ina cikin wannan halin wani azzalumi yaje ya kashe min mahaifiya, a gaban idona kika hana a tafi dani inda zanj...