Dakyar likitoci suka samu numfashin Badiyya ya daidaita, cikin dare aka tafi da gawar Firdausi Kankia, amma anbar Ladi da kanwar Firdausi; Jamila a wajen.
Musaddiq yace shi sam bazai yadda a kashe mishi yar uwa a banza ba, domi daga gani kisan gilla ne, kisan was intentional. Saboda haka yayi alkawarin gano duk wanda ya aikata hakan.
Washe gari da safe aka ma Firdausi sutura, bayan an kaita an dawo, su Kausar sai kuka suke, sai yanzu suke realizing abubuwan da take fadi, sai yanzu suka yadda da maganarta. Ashe da gaske take idan tace na bankwana? Basu taba kawo ma ransu cewar da gasken mutuwar zatayi ba.
Musaddiq yan sanda ya dauka akaje gidan, Malam Tanko suka iske zaune kofar gida yayi jugum. "Sannu Malam," Inspector Sadat yayi magana, yana mika mashi hannu alamar sallama.
Malam Tanko mika mashi hannun yayi, "Yauwa yaro," ya fada, domin jikinshi yayi sanyi, yasan dole a nemeshi cikin case dinnan, tunda shine mai gadi.
"Tsoho so muke a fada mana wanda ya shigo gidannan last jiya," Inspector ya fada, yana scrutinizing face dinshi, domin yaga idan akwai alamun rashin gaskiya ko babu.
"To nidai jiya wajen karfe 9, wani yaro yazo yace ana sallama dani, nace yaje ya kira mutumin amma yaqi, dole na bishi domin inga waye, danaje kuma banga kowa ba, sai na dawo," Malam Tanko ya fada, zufa na keto mashi, domin yasan tabbas laifi ne barin wajen aikinshi dayayi cikin dare. Fatan shi daya Allah yasa suyi sparing dinshi.
"To daka dawo baka ga alamun an shiga gidan ba?" Inspector ya kara tambayarshi.
"Aa gaskiya ban gani ba, amma duk ranar Friday Baban Badiyya yana zuwa, to bansan ko yazo bani nan ba," Malam Tanko ya fada.
"To kai bakaiji wani sound ba haka alamun buga mutun jikin bango? Yarinyar kuma batayi ihu ba?"
"Gaskiya Yallabai banji ba," Malam Tanko ya fada yana goge zufar data keto mashi.
A haka akaita tambayarshi yana bada amsa, duk yabi ya rude, rayuwarshi bai taba arba da yan sanda suna mashi tambayarsu ta kure gaskiya ba. Ba kamar yan sandan Nigeria, tsoronsu zai saka ka amsa laifin da bakasan kayi ba, ga iya yima mutum rijiya ya fada koda mutum bai aikata hakan ba.
Da aka shiga aka ga abun ba alamun zaa gane wanda ya aikata hakan sai suka tambaya ina yarinyar, wata kila ita ta gani.
Gaba daya suka tafi asibitin domin suga Badiyya, bayan sunje likitoci suka fada masu akan ta shiga coma, baza'a iya cewa ga ranarda zata farfado ba, saidai a jira ikon ubangiji.
Ba yadda ba'a yiba domin a karbi camera hannunta kodan kila a samu wani evidence, amma abun ya gagara, da alama jikinta yayi frenzing tare da camera, kuma yadda ta rike camera kamar rayuwarta gaba daya ta dogara da camera ne.
Babu yadda suka iya saidai sukace a basu number Ahmad, domin shine last chance dinsu; kuma first suspect dinsu.
Saida tayi 2 missed calls sannan a kira na ukku ya daga. "Hello, wake magana?" Ya fada, alamun an takura shi.
"Inspector Sadat ne, mun kira ne domin muna suspecting dinka akan kashe tsohuwar matarka; Firdausi," Inspector ya fada, cikin kakkausar murya, domin daga jin muryar Ahmad yasan baida gaskiya.
"Firdausi kuma?" Ya tambaya, tsananin mamaki karara a muryarshi.
"Eh ita. Ance kaine kullun kake zuwa gidan duk ranar Friday, but jiya bakaje ba, that means kanada masaniya akan hakan."
"Yallabai, ni banma san ta rasu ba, yanzu ya Badiyyar? Lafiyarta kalau kuwa? Ni ina Lagos naje aiki, amma yanzu zanbi next flight Insha Allahu," Ahmad ya fada, fatanshi Allah yasa Badiyya lafiyarta kalau.
"Badiyya tana asibiti, kuma daka dawo kayi reporting a police station, inba haka bazaka wanke kanka ba," Inspector ya fada, yana kashe waya.
Nan ya sanarda Musaddiq yadda sukayi, shi kanshi ya daure, to wa ya aikata ma Adda Fiddi wannan ta'addancin?
Wajen karfe 4 na marece Ahmad ya diro Dutsinma, looking worried, a haka yaje police station din, ya rokesu da su barshi yaje yaga Badiyya, yana zuwa ya ganta kwance lifeless, wasu hawaye masu zafi suka sulalo mashi.
Haka ya zauna yanata kallonta, saida mahgrib ta gabato, sannan ya tashi ya tafi, duk zaman da yayi kannen Firdausi ba wanda yace mashi sannu, haka yasha zamanshi ya tashi ya tafi.
***
Badiyya bata tashi ba sai bayan kwana uku, a lokacin data tashi bata cewa kowa komai ba, camerata ta kara rungumewa. Kowa tsoron yi mata magana yake, kuma sunga bata nema Momynta ba, tunani suke ko batasan ta rasu ba. Amma lura da sumar datayi ya nuna tabbas may be har wanda yayi kisan ta gani. But nobody dare to utter a single word about her Momy.
Musaddiq zuwa yanzu ya hakura, abun yaci tura, babu iota of possibility cewar Ahmad yayi kisan, kuma basu da wani suspect inba shi ba. Haka ya hakura yabar case din, kuma saboda sisters dinshi sun nuna mashi akan ya hakura, ko an gane wanda yayi kisarnan ba dawo masu da Adda Fiddi zaiyi ba.
Bayan an sallami Badiyya, kausar tace zata tafi da ita Kano, tunda acan take aure, amma fir Ahmad yaki, a cewarshi bamai raba shi da yarinyarshi. Akai akai yace bai yarda ba, haka Gwaggo tazo taita zuba ruwan bala'i akan sun jama kaninta sharrin kisa, kuma yanzu sunasan rabashi da diyarshi, salan su cunkusa mata tsanar mahaifinta.
Da sukaga bala'in Gwaggo bana karewa bane, kuma dama sudin ba yan bala'i bane, balle ga abunda yake damunsu. Sai suka hakura akan zasu barta ta tafi wajen Gwaggo, amma akan sharadin duk hutu zata rika zuwa wajensu. Budar bakin Gwaggo sai tace wannan kuma sai taga dama, tunda yanzu diya dai ta uba ce. Ganin Gwaggo na neman saida masu hali cikin asibiti yasanya suka hakura.
Har akazo za'a tafi Badiyya batayi kuka ba, wanda hakan ba karamin daga ma yan uwan Firdausi hankali yayi ba, domin yarinya kamarta yaci ace tayi kuka. Sai mutum ya kalle ta deep into her eyes sannan zaiga kukan zucin da take, zaiga plea din da take akan karsu barta wajen Gwaggo, amma ba yanda suka iya, Gwaggo tafi karfinsu.
A haka Gwaggo ta rike hannunta suka nufi motar Ahmad, Badiyya ta juya tana kallon yan uwar Mamarta, ko kwalla daya ya kasa zuba daga idonta. Babu abunda ta dauko na daga kaya daga wancan gidan, camera hannunta kawai ta tsira da ita. Ahmad yayi igniting motar, suka dauki hanyar KATSINA TA DIKKO DAKIN KARA. Sai a lokacin wasu hawaye masu tsananin zafi suka zubo daga idonta, memories dinta da mahaifiyarta suna mata ebbing cikin kwakwalwarta.
Dan Allah ku rika voting da comment, hakan zai karaman karfin guiwa. Nagode.
YOU ARE READING
RAYUWAR BADIYYA ✅
Ficción General"Tun ina yarinya kike zagin mahaifiyata, tun bansan menene maanar kalmomin wulakanci da muzgunawa ba nakejin kina fadarsu ga mahaifiyata, ina cikin wannan halin wani azzalumi yaje ya kashe min mahaifiya, a gaban idona kika hana a tafi dani inda zanj...