Bayan sun isa Katsina, Ahmad ya aje su a GRA, kafin ya tafi saida yayita ma Badiyya magana amma bata amsa shi ba, kamar ma tsoronshi take, haka ya gaji ya wuce. Badiyya sai binsu da idanu take, wanda sukazo yima Gwaggo jaje da Allah ya kyauta, kowa sai ya mata gaisuwa amma ko nuna alamar ta gane batayi.
Gwaggo ta kawo mata abincin rana, kallon abincin tayi ta kauda kai "ke kici abinci, badan kinga na kawo maki ba, kinsan halina ai," tayi kwafa, tana kara tura mata plate din gabanta.
Badiyya kara turbune fuska tayi "ni Gwaggo banasan dry jollof rice," ta fada, tana kumburo baki.
"Kam bala'i! Kinci uwarki, ai ba uwarki ta siyo kayan abincin ba balle kice wani abu, maza kici ki bani kwano na ko kuma wallahi in maki bugun tsiya yanzu," fadar Gwaggo, sai kumfar baki take kanar tana fada da babban mutun.
Badiyya sanin halin Gwaggo da tayi, dan lokacin da Firdausi ke kawota weekends ba karamar wahala take shs ba, kullun saita kunsa mata tuwo da abincin da bata saba ci ba, kuma idan taki ci ta kamata tai mata bugun tsiya, wai bazata jamata sharri ba, ace bata bata abinci.
A haka wata kawar Gwaggo, wadda ake cewa Larai tazo, Badiyya sai wasa da shinkafar take, Larai kallonta tayi ta watsar, dan tun asali diyarta taso Ahmad ya aura amma yaki.
"Wai Binta wannan diyar bata iya gaisuwa bane? Ko dan uwarta ta rasu sai akace kuma bazata gaida mutane ba?" Fadar Larai, tana kallon Gwaggo.
"Tayani gani Larai, wannan shegiyar diyar, me hali kamar na uwarta. Wai yanzu ma cewa tayi bazata shinkafa ba," Gwaggo ta fada, tana kara zabga ma Badiyya hararar tsana.
"Inyeee! Lallai to ko uwarki ita taci ta girma, shegiya dangin bakin hali," fadar Larai egoistically.
Haka sukata kyararta, sai zagin uwarta sukeyi, wanda hakan ya saka Badiyya kuka, tana kuka tana tura shinkafar badan dadi ba, tunano lokacin da suke zuwa gidan Gwaggo da Momynta tayi.
Bayan ta gama cin abincin, taje da niyyar wanke kwanon, domin har yanzu bata manta da rules din Gwaggo ba, tsawar da aka doka mata ne yasa ta firgita hade da yarda plate din tangaran ya fadi, aikuwa cikin rashin sa'a ya fashe.
"Yau na shiga ukku ni Binta, wannan diya dangin asara da bakar kafa, daga zuwanki har kin fasa mani plate, to wallahi ubanki zanci kafin uban naki ya dawo ya biya ni," Gwaggo na fadin haka tayo kan Badiyya gadan gadan, wanda Badiyya har ta kusa sakin fitsari dan dama tasan Gwaggo bazata taba sparing dinta ba.
Aikuwa tana zuwa ta jawota ta cigaba da jibga, Badiyya sai ihu take, sai da Larai taga tayi likif sannan ta taso "Binta ya isa haka, kinsan yanzu mutane na shigowa kar ace wani mugun abu kike mata," Larai ke magana, tana wani kallon Badiyya, kallon kaskanci.
"Tashi ki wuce daki," Gwaggo ta fada, tana hankada ta.
Da gudu ta ruga dakin da take kwana idan tazo, kan gado ta fada, kuka ta cigaba dayi, sai yanzu ta yarda lallai Momynta ta rasu, kuma babu me iya rescuing dinta daga muguntar Gwaggo.
Wani baccin wahala ne ya sace ta, tana bacci taji an daka mata duka a baya "tashi kije ubanki na kira, kuma saura kice mashi na bigeki, ya tafi in kara maki. Minahika me kama da uwarta," Gwaggo ta fada hade da mata kwanya saman kai.
Sumu sumu ta tashi, tana fita falon Ahmad an zubo mashi lafiyaryar shinkafa da miya yana ci. Rabewa tayi daga jikin wata kujera,tana wasa da yatsunta.
"Badiyya zoki zauna kusa dani," Ahmad ya fada, mouth full.
Karkada kai tayi hade da gyara zamanta, ko dagowa ta kalli inda yake batayi ba. "Badiyya tsoron Dady kike yanzu? Taso kinji," cewar Ahmad yana daga hannunta alamar mikar da ita. Aikuwa tanajin hannunshi akan nata ta firgita, a take ta fara ja da baya, tana wani lumfashi kamar zata shide. Ganin haka yasa yayi saurin releasing hannunta, yama mata kallon rashin fahimta. Yanzu kuma tsoronshi takeji?.
Be kara tanka ta ba, saida ya gama cin abincinshi sannan ya kalleta "Badiyya zomuje a siyo maki kaya," ya fada a raunane, yadda ta firgita ba karamin taba mashi zuciya yayi ba.
Kin ko motsi tayi, saida Gwaggo tazo tayi mata magana sannan ta mike jiki babu lakka ta tafi.
Koda suka shiga mota ko kallon inda yake batayi ba, sai rawar sanyi take tsabar tsoro, shi abun mamaki yake bashi bashi, ko me tagani? Kome yake bata tsoro haka.
A kasuwar haka yaita daukar kayan ko kallon inda yake bata yi, kuma ko hannu bata saka ta dauka ba, ya gama jidar kayanshi yakai mota ta shiga suka tafi.
Bayan sun isa ta dauki kayan ta tafi dasu dakinta, tabar Ahmad da Gwaggo na magana akan god knows what.
Tana shiga dakin ta kwanta, kaf sai yanzu rasuwar Firdausi ke damunta, ba kamar dazu da taji Gwaggo da Larai suna zaginta, sai taji kamar taje ta shakesu suma su mutu.
Tana nan zaune akayi sallar maghrib, fita tayi taje tayo alwalla, wajen dawowa taji an fisgota "Dan uwarki meyasa idan Ahmad yana maki magana baki amsawa? Kuma meyasa idan ya tabaki kike wani kamar zaki shide? Koda yake bazanga laifinki ba, dangin tsiya da bakin hali ne suka haiheki, shegiya uban yan jan sharri, yanzu da wani ya gani sai ace wani abu ai," Gwaggo ta fada, tana mata kwanya saman kai, itadai Badiyya ko kezau, bakuma ta dago ta kalleta ba. Har ta gama ta turata sannan ta wuce dakinta.
Bayan tayi sallah, tana zaune Gwaggo ta kwala mata kira taje ta amshi tuwon dare taci tayi sallar Isha'i. Ta kwanta sai kuma ta tuno da camera ta, ai ta saka video ranar, bari ta dauko tagani, kila taga wanda ya buga Momynta.
Taje ta lalubo camera ta, wanda ta zamar ma wata treasure, bayan ta zauna kan gadon, hannunta na rawa ta kunna hade da shiga ciki.
Ta tsaya tana kallon video, wata zuciyar na ce mata ta kunna wata nacewa Aa, can dai tayi karfin halin kunnawa.
Zaune taga Firdausi tana kallo abunta, amma ta lura da yadda take ajiyar zuciya, can sai taga Firdausi tayi hanyar kofa tare da saka hijab, alamun anyi knocking kuma namiji ne...........
Votes and comments dinku su zasu karamin kwarin guiwa. Nagode.
YOU ARE READING
RAYUWAR BADIYYA ✅
Fiksi Umum"Tun ina yarinya kike zagin mahaifiyata, tun bansan menene maanar kalmomin wulakanci da muzgunawa ba nakejin kina fadarsu ga mahaifiyata, ina cikin wannan halin wani azzalumi yaje ya kashe min mahaifiya, a gaban idona kika hana a tafi dani inda zanj...