BABI NA ARBA'IN DA BIYAR

3.6K 324 4
                                    

Fadin rudewar da Sultan yayi would be an understatement, jijjigata yake ta ko'ina, shi yama manta cewar shi doctor ne, duk wani ilimin kimiya a lokacin ya gushe ma kwakwalwarshi.

A hankali brain dinshi ke registering abunda ke faruwa, kafin ta fara karanto mashi 'Innalillahi, wa'inna ilaihir raji'un' sluggishly bakinshi ya fara furta kalmar, can kuma ya fara da karfi.

Shidai yasan yana rike da Badiyya, amma baiji lokacin da Abba, Baba baraka da Khadija suketa kwada sallama har suka shigo dakin ba. Hankali a tashe Baba baraka da Khadija sukayi kan Badiyya. Magana suke mashi amma kallonsu kawai yake, saidai Baba baraka ta dage ta kwada mashi mari kafin ya dawo hayyacinshi, a nan yake masu bayanin abunda ya faru, sai lokacin ya samu hawaye suka fara zubo mashi, jin jikin Badiyya yayi karara.

Zama Baba baraka tayi a bakin gadon hade da riko Badiyyar "Jeka debo min ruwa," ta fada da yar kara. Sultan a hankali kamar wanda kwai ya fashewa yaje ya dauko ruwan ya dawo ya kawo mata. Addu'a tayi cikin ruwan, a hankali ta fara shafa mata a fuska tana matsa jijiyar hannunta dadai abubuwansu irin na tsofaffi (😂 kunsan tsoffi an iya old time likitanci).

Ana haka Sultan da Khadija sun zura mata ido, Kamal kuwa ya fita domin ansa waya. Wata irin ajiyar zuciya Badiyya taja hade da squinting eyes dinta a hankali, ganinta jikin Baba baraka ba karamin razana ta yayi ba, yunkurowa tayi da niyyar tashi, hakan ya tabbatar ma Baba baraka yarinyar nan tsoronta takeji.

Sultan sauri yayi ya kamota hade da kwantar da ita gefe, Baba baraka ta mike hade da jan hannun Khadija tana fadin "Aliyu taimaka mata tayi wanka, ku sameni a falo, magana zamuyi,"tana fadin haka suka fita daga dakin.

Wani malalacin murmushi Sultan yayi flashing mata; kafin yace "Debbo am, sannu kinji. Muje kiyi wanka, Baba baraka na jiranmu a falo zamuyi magana," ya fada yana kokarin tayar da ita tsaye, batayi hesitating ba ta koma hannunshi a haka suka karasa toilet din.

Wani iri kallo ta bishi dashi ganin yayi tsaye cikin toilet din, bata fuska tayi gameda turo baki "Sultan am, ka fita ko? I'll be out in a jiffy," muryarta tayi dishi dishi saboda kuka.

Wani irin smirk ne yayi plastering on his lips, ga wani recalcitrant expression dayayi making, "Badiyya, don't be pugnacious mana, kinga Baba baraka na waje, kuma gardamar nan will take us long kafin mu fita. Ko so kike ta karajin haushi? Dan naga alamun ta hakura yanzu."

Daga jin haka Badiyya bata kara cewa komai ba, a tare sukayi wankan suka fita, doguwar riga kawai ta saka shi kuma ya zura jallabiya, da taimakonshi suka lallaba falon, dan har yanzu batajin karfin jikinta.

Badiyya zama tayi gefen Sultan a kasa, Khadija ita kuma ta koma dakin Badiyya dan ta basu wuri, shiru sukayi nadan lokaci kafin kamal ya fara magana "Badiyya naji duk abunda ya faru, sannan kuma ina mai baki hakurin rashin cika duties dina na uba da banyi ba. Ni ya kamata first kizo ki fada ma fear dinki a matsayina na mahaifinki. Amma yanzu dai duk abar maganar, Baba abunda tayi bamuji dadinshi ba, wanda ita kanta bataji dadi ba kuma taji kunya. Yanzu haka dalilin zuwanta gidannan domin ta baki hakuri ne, dan ta tausaya maki kwarai dajin labarinki, wanda shine silar jefaki cikin wasi wasi akan abunda zaki haifa," Abba ya fada yana mata kallon tausayi, santa da tausayinta na kara shigarshi, jinta yake kamar diyar daya haifa da cikinshi.

Badiyya kasa tayi da kanta, hannunta dake cikin na Sultan ta kara matsewa, wasu hawaye masu dumi na zubo mata. Kafin tayi magana Baba baraka ta fara magana, muryarta kadai ya isa nuni da yadda tayi dana sani da kuma tausayin Badiyya daya cika mata zuciya. "Yar nan kiyi hakuri dan Allah, nasan kwata kwata abunda na mike ban kyauta, hakan ya samo nasaba ne da rashin sanin labarinki da ban ba, a tunanina kawai sangarcewa yasa bakisan haihuwar, ashe wata irin rayuwa kika fuskanta mai wuyar fada. Maganar mahaifinki kuwa, bazan koma ba har sai mun tabbatar da hankalinshi ya dawo kanki, su kuma sauran da suka cuceki Allah zaiyi yadda yakeso dasu."

Nandai suka cigaba da tattaunawa, Baba baraka na nuna masu cewar asiri ne aka mashi aka rabata dashi, kasancewar ta mai bada irin magungunann nan a kauyen su. Nan ta fadama Sultan irin magungunan da takeso yaje ya siyo, kamar su habbatus sauda, zam zam, da sauransu.

Janyo Badiyya tayi tana lallashinta, murya can kasa Badiyya ta fara magana "Bansan da wane irin baki zan gode maku ba, hakika na zama butulu da ace na zubar da cikin nan. Na taso cikin tsananin gatan rayuwa da farin ciki wanda ban taba tunanin zai dakile ba balle har yamin nisa. Nayi rayuwar da ban taba kawo ma raina ba, rayuwa ce cikin kunci da bakin ciki, rayuwa ce wadda babu digon farin ciki ko daya a cikinta, mutane ukkun da suke bani farin ciki duk sunyi nisa dani. Rayuwa batamin dadi ba, hakan yasa nakejin tsoron kawo wata halittar cikin duniya, kuma na tafi na barshi ya maimata irin rayuwar da nayi, wadda babu dandanon dadi a tattare da ita. Banason abunda zai haifa yayi maraicin uwa, kamar yadda nayi. Har yanzu I can vividly see my mom, sparwled on the floor, as her body was soaked in blood, the wall was stained with blood. Her blood," zuwa yanzu zuciyarta ta kafe, idanunta sun daina fidda ruwa, kirjinta takejin yana mata wani irin zafi.

Ruwa Sultan ya dauko ya mika mata, ba musu ta karba tayi gulping down, babu wanda yace mata kala, sai can Baba baraka ta fara bata baki, tana tausar mata da zuciya. Sultan kuwa kasa magana yayi, mahaifiyarshi na mishi gizo cikin kwakwalwa, fuskarta yakesan gani, dariyar yakeson ji, dumin jakinta yakeson yayi engulping dinshi. Shin wai waye wannan daya rabasu da mahaifansu ababen kaunarsu? Dan kusa a iya cewa kisan gilla daya aka masu.

***

Gwaggo ce keta lahainiya a bakin titi, dan kuwa zuwa yanzu dan gidan ma data siya ta saida shi, duk sana'ar data kama sai jarin ya mutu, gabadaya suturarta masu tsada takai yar kutungu ta siyar, amma still kamar ana kona kara haka duk abunda ta samu yake karewa.

Ganin ana rabama wadanda suke bara kusa dasu a bakin titin steel rolling, yasa tayi azamar tasowa daga inuwar data shiga domin hutawa da zafin rana.

Wata kawar bararta ta dafo a gajiye, saboda rabonda taci abinci mai sunan abinci har ta manta, gaba daya jikinta ya yankwane, fatarta tayi wasu scales saboda rashin wanka, kibarta kuwa duk ta zabge, sai tsabar azabar bakin da tayi.

"Kande, ki tashi mu tafi, ga wannan Alhajin me zuwa duk friday yazo, kuma kinsan gara muje da wuri kafin a fara turereniyar nan, sai a karya mutum in baiyi wasa ba," Gwaggo ta fada tana karkade kasar data kama mata kodadden zaninta.

"Keni wallahi kin cika azabar san kudin bala'i, kibar mutum yaji da bakar yunwar dake damunshi, ga azabar zafi, amma zakije kikai kanki cikin wancan garadan mazan, sai kin kare a banza ai. Kwadayayya, Alhajin ma da bai wuce naira dari yake badawa ba," Kande ta fada enragedly, wata irin muguwar harara take zabga ma Gwaggo.

Wani irin murmushin takaici Gwaggo ta saki, wai yau ita ake cema kwadayayya. "Kande kenan, bari kiji in fada maki, in da kin sanni a baya, aka cemaki nice yanzu wallahi sai kin kwasawa wanda ya fada maki haka mari. Dan kuwa karshen gata na sameshi a rayuwata, kaddara ce ta rabani da wanda yake kula dani, amma karki damu, very soon. Ko dan naki da kike ganin yana kawo maki garin kwaki kullun, to wallahi a lokacin ko kallon almajiri na bazan iya mashi ba, aikin banza kawai," tana fadin haka ta wuce ta tsallaka titi, zuciyarta na wani irin kuna kamar ta fiddota waje ko taji sauki.

Tana zuwa wajen ya cika makil, ga Alhajin ta cikin window din motarshi yake bada kudin. Kutsawa tayi har Allah yakaita ga zuwa gab da motar, baki ta bude a hankali tana "Alhaji Allah ya saka maka da alheri, Allah ya taimakeka kamar yadda ka taimake mu," Alhajin ya miko mata kudin, kafin ta karba wani kirteten saurayi ya wuwure kudin hade da hankadata bakin titi, wanda yayi daidai da zuwan wata bakar jeep tayi gaba da ita.

A gigice mutanen wurin sukayi kan Gwaggo, wadda jini ya gama wanke mata jikinta. A gigice saurayin dabai wuce 35years ba ya fito daga cikin motar, da ganin kudi sun zauna mashi, iyakar rudewa ya rude, ganin Gwaggo bata kwakwaran motsi.

"Ku taimaka min na sakata a mota muje asibiti," he whimpered, yana flashing dinsu a pleading look.

Matan wurin suka kamata aka sakata ciki, Kande ce ta shiga suka tafi asibiti, likitoci ne sukayi kanta ganin ceto ranta na neman zaman musu barazana.


RAYUWAR BADIYYA ✅ Where stories live. Discover now