Kwance take lifelessly a saman gadon asibitin, sai mutum ya lura sosai zai iya gane fitar hawaye daga gefen idanunta, wanda eyes din were halfy closed.
Jin kamar muryar Larai yasa ta juyo da kanta cikeda tsananin azaba, dan ji take kamar ana daka dukkan wata gaba ta jikinta. "Inna, ina kwana? Har kin shigo? Wallahi dama yunwa nakeji," Adama ta fada cikin wata murya taban tausayi, me cike da jin jiki.
Tsakin da Larai tayi ne yasa a hankali ta dago da idanta tana mata wani flummoxed look. Kafin tayi magana Larai ta fara magana cikeda da masifa da kosawa "Nifa wallahi nagaji, na rasa gane wace irin cutace ke damunki haka. Gaba daya yan kudina dana kullo sun kare, ke gashi nama kasa gane kan gadon cutarki. Allah idan nagaji saidai ki nemeni ki rasa."
Binta da kallon mamaki Adama tayi, dama Uwa tana kosawa da yar ta? Dama uwa tana kin jurar duk wani abu daya shafi ya'yanta? Dama uwa kan iya furta irin wadannan kalaman ga diyarta me tsananin bukatarta?. Can wata zuciyar tace "Ki fara masa ma kanki wannan tambayar." Tunowa da diyarta Nana tayi, wadda itama yanzu batasan halin da take ciki ba.
Dakyar ta bude baki ta fara magana "Inna ni kaina ba'asan raina nake zama wajennan ba, inda so samu ne yanzu ina gida cikin ya'yana, saidai kaddara ta riga fata. Kuma maganar kudi, ina duk kudaden Ahmad danake turo maki, Inna? Ina tunanin ai basu isa ace sun kare ba, dama rana irin ta yau ake gudu, tunda ga amfaninsu yazo ai sai ayi ko?" Yadda take furta kalma daya kan daya, me saurare bazai iya bata awa biyar ba nan gaba.
Tun bayan shigowarsu garin Niger state ta kama hayar wani daki a wani gida, bawai dan tana da tabbacin zata samu kudin dazata biya ba. A haka wata rana cikin dare ciwo ya turnuke ta, da safe matar dake kusa da dakinta, ganin har hantsi bata fitoba yasa ita ta shiga. Ganinta sukayi a sume tsakar daki, nan suka daukota suka kai General hospital Minna. Ganin bills din cutar dake damunta yasa sukayi inquiring danginta, nan aka kira Larai tazo ta cigaba da zama da ita. Ba wasu cutuka bane illa HIV da ciwon zuciya!
Maganar da Larai tayi da karfi ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin data lula. "Lallai Adama wallahi kanki yayi tauri, wato tambayata kike ina kudin da kike turowa ko? To kamar yarda kike amshesu da karfi da yaji wajen maisu, haka ni kuma hankali kwance ya fizgesu a hannunki. Kinga tafiyata, ga kudi nan idan kinada bukatar komawa gida," Larai ta fada fuskarta babu alamun imani, tana ajiye mata kudi Naira dubu goma a gefen gadon hade dayin gaba.
Cikin muryar marasa lafiya Adama ke kiranta kukanta na tsananta, amma kwata kwata Larai batada alamar zata juyo. Tana fita Adama ta rufe ido hade da fashewa da wani matsiyacin kuka. Kukane na sheer sadness and remorse.
***
Badiyya bata farka ba sai can wajen azuhar, dishi dishi ta fara ganin fuskokin wadanda ke dakin suna jifanta da kallo mai cikeda so da kauna, idanunta basu sauka akan kowa ba sai Uncle dinta; Musaddiq, wanda fuskarshi ke ciked da murmushi.
Ai batasan lokacin data wartsake ba, wani ihun jin dadi ta saki hade da mikewa zauna, yarinya yar shekara goma ta koma. Yunkurowa tayi da niyyar saukowa daga kan gadon, zafin dataji ne yasa ta koma ta zauna tana kura mishi ido hade da tabe baki "Uncle manaaa," ta fada cikeda shagwa tana bude hannayenta alanar hugging dinshi.
Duk mutanen wajen dariya ta basu, a haka yana dariya ya karaso wajenta, engulfing dinta into a tight hug yayi, ai sai kuma ta fashe da kuka. "Nayi kewar Uncle dina mai siya min sweet kullum," ta fada cikin kuka hade da fashewa da dariya.
Dariya yai shima kafin ya janyo kujera ya zauna kusa da ita, hannunshi kem cikin nata. "Nima nayi kewar Badiyyar Sultan dinta," ya fada cikeda kewa.
Kafin Badiyya ta kara maganar Aunty Kausar tace "Lallai ma yarinyar nan, wato duk mu baki ganmu ba sai Musaddiq ko? To ku su Jamila kuzo mu koma, Musaddiq akesan gani," Ta fada cikeda da gatse, tana tattara gyalenta alamun da gaske tafiyar zatayi.
YOU ARE READING
RAYUWAR BADIYYA ✅
Genel Kurgu"Tun ina yarinya kike zagin mahaifiyata, tun bansan menene maanar kalmomin wulakanci da muzgunawa ba nakejin kina fadarsu ga mahaifiyata, ina cikin wannan halin wani azzalumi yaje ya kashe min mahaifiya, a gaban idona kika hana a tafi dani inda zanj...