BABI NA TALATIN

4.3K 400 13
                                    

Badiyya wanka tayi ta shirya sannan tazo ta gyara wajen, kaya ta saka sannan tayi hanyar fita. Tana fita ta jiyo kamshi na tashi daga kitchen, murmushine ya bayyana kan fuskarta kafin ta karasa kitchen dan taga abunda ke faruwa. Tana shiga taga Sultan sanye da apron yana soya plantain.

Batasan lokacin da dariya ta subuce mata ba, dariyarta ta tsorota shi har saida ya juyo "Debbo am, kin bani tsoro wlh, I though bacci fa kike," ya fada yana dafe kirji, alamun da gaske yaji tsoron.

Dariya ta kara kwashewa da ita "Sultan am, kamar ba namiji ba? Karka bani kunya mana dan Allah, sorry kaji Sultan am," ta fada tana fluttering eyelashes dinta ostentatiously. "But wait... miye Debbo am ma? Na manta Allah," pouting lips dinta tayi, alamar tana san ta tuno abunda Debbo yake nufi.

Gwalo ya mata sannan ya girgiza kanshi alamar Aa "Bazan fada ba, lokacin da aka koya mana ba har dariya kike mani bana pronouncing daidai ba? To banzan fada ba nima. Da yanzu Ammi nanan sai muje ta koya maki," fadin haka ya tuna mashi da mahaifiyarshi, take expression din fuskarshi ya chanza. Ganin haka Badiyya yasa tayi saurin chanza akalar maganar, dan in har suka kara magana kan haka to baza'a samu me rarrashin wani ba.

"Sultan am, nidai ka fada mani, inba haka ba Allah babu ruwana dakai," tana dan bubbuga kafa a kasa alamun shagwaba.

Riko hannunta yayi ya zaunar da ita akan dan karamin table me dauke da two chairs a gefen kitchen din yayi, murmushinshi mai kyau yayi mata hade da zama gefenta. "Debbo am na nufin matata," ya bata amsa yana mata murmushi. Itama murmushin tayi mashi, me cikeda alamun ta tuno lokacin da aka koya masu "Ohh hakane fah. A wali jam, Gorko am?" Ta fada cike da zolaya.

Pouting lips dinshi yayi kamar baby "Ah noo.. banasan gorko am dinnan, ai kowa zai iya zama mijinki, kuma kinga ina iya maki kishiya, so Sultan am din yafi dadi, that's for sure I'm your Sultan," ya fada yana mata wink cikeda zolaya. Badiyya hade fuska tayi ba alamun wasa, ta juya kanta gaba daya daga kallonshi. Dan fadar maganar zai kara aure ma ba karamin bata mata rai tayi ba, dukda tasan wasa yake, amma tsananin kishinta bazai barta ta yarda wasa kadai bane.

"Me nayi kuma Debbo am?" Ya tambaya innocently, yana kokarin suppressing dariyar datazo mashi.

Magana yayi tayi amma Badiyya tayi banza dashi, ganin plantain din dayasa zata kone yasa yaje ya juye hade da dawowa. "Debbo am, wasa nake maki wallahi, ni na isa na miki kishiya? Ke infact ma ko admiring wata macen ban tabayi ba sai ke, trust me," ya fada pleadingly, hade da daukar hannunta cikin nashi.

"To nidai Sultan am banasan irin wannan wasan, inada kishi fa Allah," muryarta har ta fara karaya kamar zatayi kuka.

Dariyar da ya daure tun dazu ce ta kufce mashi, yi yake har yayi mai isarshi, ita kuma Badiyya kallonshi take admiringly. "Sultan am dariya ma na baka ko?" Ta tambaya tana turbune fuska, bayan taga ya tsagaita dariyar.

"I was just happy ne, ashe dai ana kishina?" Wink yayi mata wanda yaja dole ta kauda face dinta dole tana blushing. Saurin mikewa tsaye tayi tana hade kayan dan suje suyi breakfast. Data gama hadawa sai ta fara mika mashi yana kaiwa dining table din dake falon, idansu na haduwa zai sakar mata da murmushi ita kuma ta kauda kai tana blushing.

Breakfast sukaje sukayi cikin nutsuwa babu wanda yayi magana cikinsu, sai sakon da Sultan yake emoting mata through his eyes, ita kuma ta daina kallonshi dan yanzu wani nauyinshi takeji.

Suna gamawa suka nufi falon dan suyi kallo kafin ya fita, zama yayi kan three sitter sannan yayi mata alamu da hannu akan tazo ta zauna. Kasancewar tana da tambayoyin da takeso ta mishi yasa withoust hesitation taje ta zauna. Hannun yakai ya janyota kan jikinshi, wanda batayi kokarin janye jikinta ba saima kwantar da kanta da tayi akan broad chest dinshi.

RAYUWAR BADIYYA ✅ Where stories live. Discover now