Shimfida

1.9K 205 48
                                    

  Cunkushewan da hanyoyin da zai sada mutum zuwa da stadium din birnin Jalingo tun da daga presidential lodge na sabuwar GRA  da ke garin. Motoci ne masu tsada wasu akan mashina kirar ladies {wayyo kuɗina}, wasu na tafe cikin jimami wasu na hirar duniya yayin da ke tofin Allah tsine.

"Kirkin grand khadi ya sa ni halartan jana'izan nan, in ba haka ba mai ake da mai saɓa ma iyayensa" cewan wani da ke zaune a Saman babur. 

"Ai Yushaau ni ko don kuɗin makaranta da ya biya min bara dole na masa wannan halacin. Gashi an ce duk cikin zuri'ar sa babu Wanda ya ke so sama da ita, amma don ta cika tsinanniya a ce har gidan radiyo da je tana mai aibata Mahaifin ta"  haka su ka isa stadium in da za'a sallaci gawan.

Bayan an sauko da gawar daga cikin motar asibiti (ambulance) yayi daidai ta haɗa sahu da aka yi. Babban limami Jalingo ya jagoranci sallan yana mai karanto addu'ar samun Rahma ga marigayiya haɗe da sauran al'umma wa'inda su ka riga mu gidan gaskiya da wa'inda su ke Raye. Bayan an idar aka dangantata da makabarta in da aka saka ta a gidan ta na gaskiya.  

Liman yayi wa'azi akan zaman duniya da shirya ma isko lahira, tare da nuni da qiyaman ɗan adam na farawa ne daga san da mala'ikan mutuwa ya ziyarci mutum. Anan gaɓan ne Justice Ubaidullah ya fara kuka mai tsima zuciya, rungume matashin da ke tsaye yayi yana kuka, duk in da kiyayya ya kai matashin nan na jiyo shi tun daga tafin kafa, ji yake kamar ya ya tunkuɗe Justice ya haɗa da shi cikin Ramin ya birne.

 "Allah ya jikan ki Amma, na yafe miki Ubangiji Allah ya sada ki da Aljanna" yace cikin kuka, kalaman da ya sanya matashin nan zare jikin sa, ya juya ya shige mutane ba tare da ya ce uffan ba. 

'Ni da Zainab aka yi ma rashi ba kai ba, wakilin Shaiɗan a doron kasa' ya ce a rashin yana kaucewa masu masa gaisuwa na ainihi da na gulma.

***

Daga maqabarta gidan Justice cike yake fal, masu kuka na yi wasu sun kafa dandalin hira wanda mafi akasari akan alakar marigayiya da mahaifinta ne. 

"Ai ban taɓa ganin tsinanniya kamar Amma ba, kun san  cewa don ta kalli idonsa ta zage shi ba komai bane, ni kam ba ta min ko don ba ta ga fuska bane" cewar matar baban tana mai cin farfesun cinyar sa da aka kawo mata. 

"Ai Adda Jamila ina tunanin da kin sakar mata fuska wata rana sai kun dambata" cewar Hajiya shamsiyya, kanwar Justice

"Ai kuwa dai, an rage mugun iri, shi kuma ɗan iskan mijin da bai san daɗin ta ba ance kasa zama makabarta yayi, naji su Almustapha suna Allah sa kar ya taɓa shi. Hajiya Jamila tace tana mai kara jan tsaki. Nan su ka saki shewa su duka tare da cigaba da cin abincin su.

***

"Hakuri za ka yi, sannan ka iya bakinka, babu wanda zai ji maganar nan ya yarda Hammad, Allah ya jikan ta ya sa chan ya fi nan"  faɗin dattijuwan da kallo ɗaya za ka mata ka san mahaifiyar sa ce.

"Momma Amma ba ta san daɗin uba ba, ba ta san daɗin uwa ba, bata san wani abu soyayya ba, daga ni sai zainab ne masu sonta, kafin ta dandani soyayyar kuma rai yayi halinsa" ya ce cikin shessheka

"saboda soyayyar duniya ba ta dindindin bace, shi ne Allah ya sada ta da soyayyar asali, addu'a za ka mata Hammad, kuma ina mai kara jan maka kunne,  bakinka kanen kafarka" tace tana mai mikewa. Sai da ya sha kukansa ma'ishi kafin ya tashi ya yi alwala tare da gabatar da nafila kafin a kira sallan la'asar. 

MAKANTAR ZUCI Where stories live. Discover now