Kuka sosai ta ke yi bayan ta sauke wayar. "Shike nan Aisha kin tafi kin barni, shike nan na rasa sadaqatul jariya daga gare ki a lokacin da babu ni a doron kasa, Ya Rabbi ka amshi bakoncin ta, na san ta wuce sashin farko na tambayoyi ubangiji ka zama mata gata a sauran" tace tana ɓarkewa da sabon kuka.
"Subhanallah, Batula mai ke faruwa" me gidanta ya shigo yana fadi, don tun daga bakin kofa ya jiyo kukan ta.
"Aisha babu ita" tace tana kwanciya a kirjinsa, bayan ta yake shafawa
"wace Aisha kuma" har ga Allah ya shiga ruɗu, zuciyar sa Sam ta kasa tuna masa wata Amma.
"Amma, yanzu Hammad ya kira yake ce min an kaita, shike nan fa babu ita, anya na sauke hakki na a matsayin uwa? Na tsallake su, tana da shekara uku, sai da tayi wayau ta nemo ni a karan kanta fa" tace tana dara sabon kuka.
"shhhhhhhhhh! Insha'Allah tana cikin halin kwarai, tashi mu yi Raka'a biyu mu nema mata Rahma" yace yana kamo hannunta, bayin da ke haɗe da ɗakin ya ja ta, shi ya mata alwala yana yi yana bata baki, kana ya ja su sallah. Sun mata addu'a sosai, sun roka mata afuwa, sun roka mata Rahma sun tausaya mata kasancewar mutuwar quruciya.
Bayan sun idar ne take ce ma mijin
"ka san jikina na bani ba mutuwar Allah sa annabi Amma tayi ba, anya ba dodo aka ba rayuwar Amma ba" tace tana kallonsa. Duk da akwai ɓoyayyen sirrin da mijin ta bai sani ba saboda aukuwan sa kafin auren su, amma tun bayan da ta zama matarsa ba ta sake ɓoye masa komi ba. Kafin ta faɗi ma wani damuwar ta ko da akansa ne, shi take tunkara da zancen.
"wani abu ne ya faru?" ya tambaya
"a'a, gani nayi dai zuwan da su ka yi karshe kalaman ta na tuhuma da tayi min" tace tana share hawaye.
***
Alhamis ashirin da shida ga watan Janairu shekara ta dubu biyu da goma sha bakwai...
Hammad ke tuka motar, gaban motar Amma ce ta hakince tana kumbure-kumbure yayin da Hammad da zainab ke antaya mata dariya. Tun da ta ga ana soya doya cikin kwai bakin titi ta sa rigima sai sun tsaya sun siya, shi kuma Hammad ya ce ba zai siya germs ba. Tun lokacin ta dauke wuta.
Wakar Maheer Zain ke tashi a motar, yayin da zukatansu ke cike da kaunar wanda ya ke bege. Har su ka shiga gate din da zai sada su da gidan mahaifiyarsu da ke zaune a kwatas din Modibbo Adama university of technology. Da kwatance su ka isa gidan.
"Oyoyo Oyoyo Adda Amma, Adda zee" cewa kanen su biyu Sharhabil da Suhail. Da murna suka dauke su sama, sai a sannan su ka lura da wani da ba su sani ba. Suhail da ya kasance mai son mutane ne ya je yana mika masa hannu da sunan sallama. Take Hammad ya ji son yaron ya shige shi tare da mamakin wayonsa kasancewa ba za su wuce shekaru takwas ba.
KAMU SEDANG MEMBACA
MAKANTAR ZUCI
Misteri / ThrillerRayuwa kan zo ma kowa da kalar qaddarar sa, walau khairan ko akasin hakan. A duk yanda ta zo maka da kamata yayi ka rungume shi cikin gode ma Allah akan sauran ni'imomin da ya maka ba tare da sanya damuwa ba. Zainab (Amra) da Fatima (Amma) suna cik...