Da haka zancen komawar sa karo ilimi ya sha ruwa, sai dai ya karfafa sana'ar Ashiru, na safaran fatu daga Jihohin Taraba da Adamawa zuwa kasashen da su ka shahara a sarrafa fata. Sannu a hankali har shi ma ya fara zuba kudinsa a harkan, kafin ka ce menene a shekara ɗaya tsangayar sheikh Muaze ya ta tashi daga shahara akan malanta zuwa Hayin Alhaji Ashiru mai Fata. Hakan bai hana sauran yan uwa masu sha'awar malanta cigaba da yi ba, masu kiwo na yi masu kasuwanci ma duk su na yi.
A haka Ubaidullah ya samu gurbin karatu a jami'ar Bayero da ke Kano, in da ya samu a sashin Alkalanci (Faculty of Law). Da karfin sa ya fara karatun saboda ra'ayi, mafarki da burinsa kacokan na kan zama babban alkali. Yayyinsa ba su sa masa ido ba duk kuwa da cewa shekara ɗayan da yayi a gida ya tara dukiya mai yawa, haka nan su ka tsaya kai da fata su ka biya duk wani abin da ake biya, yayansa na talatin Muhammad Nura ya chanza masa akwati da kayan sawa, Yayyinsa mata ma ba daga baya ba, haka su ka aiko da sakonni, mai dambun zabi, wasu niya cike da tsoka haka dai ya harhaɗa ya isa jami'a kamar ɗan sarki.
Shekarar farko bai masa wahala ba saboda kusan gabatarwa ne da kuma tuni akan abin da ya sani a sakandire. Hakan bai sa yayi wasa ko ya rage kai min karatun sa ba. Ko da su ka kammala ajin farko shi ya zama zakaran ajin in da ya samu kashi tamanin da tara da ɗigo tara cikin ɗari. Hakan ya sanya sunansa ya koma Ubaidu OO1.
A hakan yayi farin jini don tarin abokai da yan mata, masu sonsa domin Allah, da masu sonsa domin su karu da baiwa na ilimin sa har da masu sonsa domin a ce suna da alaka ta sanayya ko abota da haziki Ubaidu 001. Shi dai ko a jikin sa in dai mutum zai raɓe shi ba tare da takura ba, kuma bai kasance mai cin naman wani ba toh tabbas ba zai hantare shi ba. Baya da kyashi ko hassada sannan abin hannunsa baya taɓa rufe masa ido.
A haka su shiga ajin karshe, lokacin ne ya maida rayuwar sa cikin ɗakin karatu, in har ba malami a ajin su ya gwammace ya shiga library yayi karatu saboda Tsabagen burinsa akan karatun law baya son abin da zai ja masa nakasu komi kankantar sa.
***
Yau ma kamar kullum ya shigo cikin library ɗin, gefen da ya ke neman maidawa alkibla ya kalla, ajiyar zuciyar sa na nan zaune ta maida hankali wajen karatu bata ma san yana yi ba.
Wani irin shockin ya ke ji jikinsa ga wani abu na fisgarsa kamar mayan karfe da karfe. Kamar yayi mata magana amma wani kwarjini haɗe da sonta ke kara lullube shi. Hakan bai zama bakon abu ba don tun da ta fara haduwa da ita yake jin haka. Kamar ko yaushe jan kujera yayi ya zauna a saitin da duk ya ɗaga kai toh da ita idanunsa za su fara gani.
Karatunsa ya cigaba a hankali shauqin ta na fisgarsa hakan bai hana karatun shiga ba kuma bai hana shi ganin motsinta ba. Kiran sallah ya mikar da shi, tana da ga zaune kamar yanda ya kula tun shigowan satin bata fita sallah kamar yanda da take yi ba, hakan ya sa ya ayyana ma ranshi tana hali na al'ada ne.
Fallen takarda ya cire yayi dan rubutu, ko da zai fita sai ya ajiye mata a Saman littafai ya fice don zuwa bada farali yana mai addu'a ubangiji Allah ya ɗaura shi a kanta.
***
Ko da ya ajiye mata takarda bata ko kalle shi ba, asali ma cigaba da karatunta tayi kamar bata san da wani halitta a wajen ba. Yana wucewa ta bi shi da kallo har sai da ya ɓace ma ganinta. Tun fara ganin sa tana aji ɗaya yana uku Allah ya ɗaura mata sonsa. Bata damu kanta ba haka bata bayyana ma kowa ba haka ta dinga shawara daga ita sai mahaliccinsa. Sau da yawa ta kan tashi cikin dare, tayi kuka cikin sujjada tana rokon Allah ya hankaɗo mata Ubaidullah, ya shi zai kasance mijinta na farko itama ta kasance matarsa ta farko.
YOU ARE READING
MAKANTAR ZUCI
Mystery / ThrillerRayuwa kan zo ma kowa da kalar qaddarar sa, walau khairan ko akasin hakan. A duk yanda ta zo maka da kamata yayi ka rungume shi cikin gode ma Allah akan sauran ni'imomin da ya maka ba tare da sanya damuwa ba. Zainab (Amra) da Fatima (Amma) suna cik...