Babi Na Tara

1.2K 203 52
                                    

ALLAHU AKBAR
ALLAHU AKBAR
LAA ILAHA ILLA ALLAH
ALLAHU AKBAR
ALLAHU AKBAR
WA LILLAHI HAMD
ALLAHU AKBAR KABEERA
WALHAMDULILLAHI KATHEERA
LAA ILAHA ILLA ALLAH
ALLAHU AKBAR
ALLAHU AKBAR
WA LILLAHI HAMD

Tun bayan rasuwan Sheikh da sati, iyalansa su ka fara fuskantar hargitsi na rayuwa, wasu da ga cikin kwarkwarorin sun tattara kananun ya'yansu sun yi gaba saboda kishim kishim ɗin da ke yawo akan gwamnati zata kwace duk wani abin da sheikh ya mallaka.
Almajiran sheikh su ka duqufa da addu'a, ba su kaɗai ba har ya'yansa, sauka da yanka kuwa sun yi fiye da a kirga. Duk wani kalan addu'a mai inganci da akasin sa, ma daidai da na kuskure sun yi don kar a tozarta musu mahaifi ko bayan babu shi.
Ranar da sakon gwamnati ta iske su akan su tattara duk wani abin da sheikh ya mallaka su aika shi kafin su zo su aikata shi a wulakance. Don a cewar kanal ɗan fari filin da sheikh ma yayi gini mallakar sojin Nijeriya ne saboda haka wajen shakatawar manyan sojoji za'a yi a wajen. A daren duk wani masoyin Sheikh na hakika bai runtsa ba, ciki har da Aljanun da su kan taya shi wasu ayyuka a lokacin da ya ke raye.
Suratul yasin su ka sauke amma a juye, da harafin karshe na ayar karshe su ka fara karantawa. Duk wani lungu da sako na gidan an samu wanda ya ke zaune a wajen yana karantawa, haka su ka kwana su ka yini har zuwa lokacin da tawagar gwamnati ta isko su da motocin kwasan kaya da makaman rushed gidaje. Babu musu aka nuna musu  turkin shanayen gidan, sojoji ne da makamai su ka isa wajen, a zahiri sun ga shanayen amma suna shiga ciki duk su ka zama macizai da kunnamu. Ihun su ya tayar ma mata da yara da aka kulle a ɗakuna hankali, amma da yake umurnin da aka basu shine ko taga kada su leqa se dai su ka kudundune a ɗakunansu bakunan su na ambaton Allah.
A guje sojojin nan su ka fito daga turken wasu sun sha harbi wasu kuma sun tsira. Haka su bar gidan suna ta kamar ai in wancan sun koma  macizai ai gida ba zai tsira ba. Da yake inyamurai ne su ka cika sojojin, sai shugaban su ya ce ai in takamar su gidan malami ne ai akwai shugaban majami'a a cikin su, take ya umurci wani ya musu addu'a ya musu kalar ta su, kafin su ka shiga cikin motar rusau don rushe gidan malam.
Jama'a sun taru su na son ganin ikon Allah, yan murna na ta murna musamman ma su adawa da Shehi, yayin da masoya malam cikin mutane da Aljanu su ka tsaya a shirye don ganin ba'a wulakanta shi ba.
Duk wanda ya shiga motar sai ya dai na ganin gida sai katuwar bishiya mai fitar da wuta take tsoro da firgici ke sa su sauka da gudu suna kiran Jesus.
Ko da komandar ya ga haka sai ya hau kan motar da sunan zai yi, yana musu alkawarin query in aka kammala musamman reverend da ya ce shi bai san aikin sa ba.
Yana hawa ya gano abin da su ke gani, da yake shi ma a jike yake da tsafi sai yai murmushi ya tunkari bishiyar, yana kai wa, wanda yake daidai da gate din gidan ta waje, ya ji shi da motar a Saman gajimare su na yawo ga wuta na cin inda yake zaune. Ihu yake yi yana neman taimako amma. Babu mai jin sa sai ma kabbara da wa'inda ke wajen ke yi don su a karamin tunanin su, Allah ne ke kare malantan Shehi.
Shi dai Manjo Izaya tsintar kansa yayi a ɗakin matarsa jikin sa duk shatin bulala, yayin da cinyoyinsa su ka yi jawur sai radadi su ke masa. Su kuma sojojin da ke tsaye wajen sun ruɗe rashin ganin kwamandarsu. Basu san mai za su je su fadi ba, ganin awanni sun shude ya sa su ka yi tunanin komawa su ce ai ya ɓace a gidan sheikh.
Ko dasu ka koma sai labari ya sha bambam don sun iske matarsa a wajen tana faɗin bata san yaushe ya shigo ba amma in ban da kuka babu abin da yake, jikin sa kuma kamar an zane, cinyoyinsa kamar mai quna.
Kanal Danfari da yake jiran a kawo masa shanaye don ya zuba a gidan gonar da ya gida chan kudu da Mubi ne ya kasa hakuri. Kiran GOC in da ya ba umurni yayi don jin me ake jira, nan ne yaji labari da ko a mafarki bai yi tunanin zai yiwu ba.
"Kar ka faɗa min maganar banza, da Ace tsohon nan ya san tsafi kamar yanda kuka ambata, babu abin da zai hana shi dago ni tun ranar da na je" se fa ya furta sannan ya tuna ai cewa yayi da kuɗin fashi sheikh ya tara shanayen shi ya sa za'a kwace.
Shi dai GOC na jin sa ya ji sanda yayi shiru kuma nan ya sa ma abin ayar tambaya.
"ko za'a chanza wasu ne sir" ya ce cikin alamun neman izini.
"eh amma cikin dare za'a je, bana son yan jarida ko ɗaya a wajen don zan kasance a wajen yayin da ake yi" ya fadi cike da isa da izza. Yana gama faɗi ya kashe waya. Amininsa ya kira wanda tare su ka tsara komi.
"Ka ji wai shanayen nan sun zama macizai kuma gidan ya zama bishiya mai wuta, in dagaske mutumin na asiri mai ya hana shi gane mu, ya gane dukiyar sa mu ke nema ba wai abin da muka shirya masa ba" yace yana tsaki don shi a ganin sa rainin wayau ne kawai  GOC ke neman kawo masa ba wai hakan ya faru da gaske bane.
"toh kada mu tono ma kanmu dai  inaga mu hakura da rusa gidan mu Kwaso shanayen kawai. Ka riko Layun ka yanda muma za mu isa cikin shiri ko ya kace"  da haka ya amince don ya san Layun sa ba abin da baya kare shi. Dariya yayi yayin da ya tuna arzikin da zai samu.
"siyar da shanayen zan yi na sa na kasashen Turai ma su bada madara" ya fadi a bayyane yana mai juyi a bisa kujera yayin da ya fara Mafarkin ido biyu.
***
A can Tunga kuwa mutane sun cika da abin mamaki, da yawa su ka fara Waliyantar da sheikh su na masu isa ga makwancinsa suna sujjada. Wasu kuma in ce ai  aikin Aljanu ne don babu yanda za'a yi babban malami ace baya aiki da Aljanu. Zantuttuka dai kala kala ake, yayin da a cikin gida mata su ka ci gaba da harkokin su.
Dakin taron sheikh yaransa maza ashirin ne a ciki kowannwnsu da iyalin sa ciki kuma babu mai kasa da shekaru arba'in. Zaune su ke suna jiran rahoton aljanun da ya bi sojojin nan ne don su san shirin da za su yi.
"Ni fa bana son wannan don kamar shirka mu ke, in shi Shehi yayi sai mu nema masa gafara, ku duba fa duk shekara ɗaya ga muharrama shi ke faɗin me zai faru a shekara amma ya kasa ganin ga abin da zai faru da shi ya kare kansa, ku ma Aljanun kuna ina aka kai shi kurkuku, aka kashe mana shi duk ba ku yi komi ba, ni dai na dawo daga rakiyar ku" ɗaya daga cikin su ya fadi.
"Ashiru! Ashiru!! Ashiru!!! Da ba Danejo ce ta haife ka ba da wallahi zan rantse ince ba ɗan Shehi kake ba. Amma mata ce ta haife ka ba saɗaka ba. Tashi ka fita tun kafin in sauke hannu na akanka, duk wani maqiyin Shehi mai irin tunanin Ashiru ya fice mana ba mu bukatar ganin sa anan" Auwalu ya fadi, yana hura hanci, da ma ya fi kowa ilimin surkulle a cikin ya'yan Shehi, wani aikin ma in Shehi ya kasa wajen Auwalu yake turawa, kuma shi ne wanda ya fara ganin duhun gidan su har ya shaida wa Shehi.
Ashiru bai kai ga fita ba Aljani ya dawo ya feshe musu abin da su ka shirya.
"Hauka za mu ɗaura ma sa, tun da zalunci ne nashi" Salisu ya ce yana dukan sandar hanunsa a kasa.
"ina za ku kai zunuban sa na rashin ibada a duk lokacin da  ya ke cikin hauka" Ashiru ya sa ke katse su. "ina laifi a firgita shi da Shehi, a bar su shiga wajen shanayen se duk wanda ya san Shehi cikin su ya gan shi a gaban sa. Inaga wannan mai sauki ne da  Ace mun lahana su, kun ga umurni aka ba su ba wai gaban kansu bane su sojojin" ya karasa ganin duk sun tsare shi da ido cike da zargi.
"kace wani abu kuma, ai ni shegen gwamnar nake so a haukatar amma gara firgicin. Mun bar komi a hannunku Arɗo." Ya karasa maganar zuwa ga kujerar da ke wajen na sarkin Aljanun yankin.
"Ba damuwa, Allah ya bamu nasara" ya faɗi yana mai mikewa, iska ya tashi daga kujerar wanda hakan ya tabbatar musu da tafiyar sa.
***
Sai dare wajen karfe goma sannan sojoji su ka iso tare da gwamna. Ba gardama aka buɗe musu kofa su shiga har baya wajen shanaye. A hankali su ke kaɗa shanayen, zuwa bayan motocin da su ka kawo don kwasansu.
Karfe goma sha biyu da rabi su ka kammala shanaye kusan ɗari biyar da yan kai. Tada motar ke da wuya su Kanal ɗan fari da ke wajen su ka lura da babu komi acikin motar yayin da shanaye ke zaune a shingen su, wasu a tsaye wasu a kwance. Take cikin sa ya ɗuri ruwa, hakan ya taɓo abokin sa da GOC a tare yana nuna musu ikon Allah. Basu kai ga samun natsuwa ba su ka ga Shehi ya fito gaban su yana dariya.
"Shanayen nan kaf dinsu babu haram, bana cin haram komi kankantar sa, saboda haka baka isa ka maida halaliyata haramiyarka ba, tun muna shaida juna bi nan" ya nuna musu hanyar fita da kyar su ka iya ɗaga kafufuwan su don tsoro ya sandarar da su a wajen.
Tafiya su ke ba ko waige haka duk wani soja da ke wajen ya bi bayan su ba tare da ya san dalilin yin hakan ba.
***
Washegari jaridu sun fitar da labari akan cin zarafin da Gwamnatin Gongola su ka yi ma babban malami saboda suna son cin gajiyan arzikinsa. Su kansu yan jarida ba su san da labarin ba, ba za su ce ga yanda aka yi labarin ya fita ba bayan su kokarin yaki da fashi da makami su ka so sawa. Take kasa ya ɗauka saboda duk wani jarida da ke fita a Nijeriya sai da aka samu wannan labarin, take kungiyoyin kare hakkin bil adama su ka fara aika wasika zuwa ga shugaban Kasa, sannan su ka kai ziyara ga iyalin marigayi Sheik Hamze, wasu da kyauttutuka wasu kuma haka kawai su ka je.

Gwamnatin tarayya kuwa a kokarin toshe wata kafa da za'a ce ta gaza ne ta sanya ya'yan Sheik da su ke kasa da shekaru ashirin a tsarin ta na tallafin karatu, bata bar su hakan ba har sai da ta sanya tallafin ta cigaba ko da an samu juyin mulki. Hakan ya sanya Ubaidullah ya samu gatan ilimin boko, yayin da ya samu sauran gata kama da ilimin Muhammadiyya har zuwa gatan ci, sha da sutura daga wajen yan uwanshi, don ba su da buri sama da na tallafawa Ubaidullah da duk wani abin da zuciyar sa ke so ko sa dace da tubarrakin Mahaifin su.

Bayan ya kammala firamare a shekara goma sha biyu, nan su ka sama masa gurbin karatu a kwalejin Barewa da ke zaria, nan din ma sai da su ka cika masa akwatunan garwa biyu da kaya, duk da kuwa sanin da su ka yi gwamnati ma samar musu abinci lafiyayya da  za su ci. Ana sauran sati ya koma cimarsa gaba ɗaya ta koma na neman tsari da kwarjini saboda labarin da ke isko su na muguntar da ake a makarantun kwana.

Ya shiga makaranta cikin nasara da kariyan ubangiji, ya kasance mai kwazo da hazaqa don bai taɓa tsallake na biyu a ajin su ba.  ko da ya kammala ajin uku an so ya je gurbin kimiyya amma tunawa da wasiccin da mahaifinsu ya bari don tsabagen faɗi masa da yayyinsa ke yi ya sa ya haddace tare da alwashin kulle Kanal Danfari duk kuwa da ritaya da aka masa akan maganar.

***

A shekaransa na goma sha takwas a rayuwa ya kammala sakandire Don a lokacin form five ake yi a kammala. Kuma a lokacin sun zama yan jihar Taraba saboda raba Gongola da aka yi zuwa jahohin Adamawa da Taraba. Shekarunsa yayi daidai da shekarun rasuwan sheikh, kana da yawa daga cikin iyalin na shi babu su don a lokacin babu ko matar Shehi ɗaya da ta yi saura, sannan ya'yan sa fiye da talatin babu su. 

"Ubaidullah zaka fadada karatun ka, ilimin addinin gidan nan da ɗan nakasu, akwai gurɓacewar tauhidi a ciki, karatun lawya in ba wanda ke da tauhidi mai kwari ba mutum sai yayi ta aikata aikin da zai kai shi wuta" Ashiru ya ce da shi kasancewar shine babba da gidan a wannan lokacin. 

"toh Shike nan ina zan je karo karatun ne?"

"zan rubuta maka wasika ka kaima sheikh Jibrilla, na yarda da karatun sa ka gyara aqeedar ka ko da ma wata shida ne, daga nan sai a nema maka gurbin karatu a jami'a" ya ce yana mika masa kwaryan fura damammiya da aka kawo masu.

Suna sha sun hira, Ashiru na bashi labarin rayuwar su a baya, da rayuwar Mahaifin su, yanda ya kaunaci Ubaidullah a Yan kwanakin da su ka yi tare. Zuciyar Ubaidullah ya kara buɗewa da soyayyar mahaifinsu tare da tausayin sa da kara ɗaukan alwashin bi masa hakkin sa.

"Shehi mutum ne mai hakuri, da juriya, bashi da riko, sannan bai yarda ya ci haram ba ko kaɗan ne. Yana da ilimin Alkurani sosai da sosai sannan ya san sirrin Alkurani. Kowace aya zai iya faɗi maka amfaninta, sannan dukkan damuwar sa da Kur'ani yake magancewa sai dai wani lokuttan har tauhidin sa yake tabawa" yace yana share kwalla da ya zubo masa yayin da yake faɗi. 

"wai tauhidin nan da ka ke faɗi ba LAA ILAHA ILLA ALLAH bane, kuma ai duk mun yarda da hakan ko" ubaidullah ya ce yana kallon sa cike da alamun rashin fahimta. 

"kwarai shine ginshiqin Tauhidi, amma faɗi kaɗai ba zai kai ka Aljanna ba, se mutum ya bi hakan da ayyuka na gari da ibadu. Misali kullum mutum ya kasance yana ambaton LAA ILAHA ILLA ALLAH amma yana neman kwarjini, soyayya, farin ciki daga wani abin da ba Allah ba. Misali in dauki Goron nan, Kaga ba komi a jikin sa ko, sai in ci don ya sa matata ta so ni ko ya sa in dinga juya ta, wannan wani nau'i ne na shirka da in ban tuba ba zan mutu ne a mushriki " yace yana mai fito da goro da kwatanta masa. 

" kai wannan fatawa naka da zafafawa a ciki, ai wannan neman taimako ne, kuma Allah ya ce tashi in taimake ka, in dai wannan ne ra'ayin da za'a sa min ka barni kawai a turban mahaifi na"

"Allah da yace tashi in taimake ka da ka faɗi, cewa yayi wanda ya kusance ni yana tafiya zan kusance shi cikin sauri, wanda yazo yana sauri zan matso gareshi cikin gudu, sannan wanda ya tuna da shi lokacin da yake cikin yalwa Allah zai tuna da shi lokacin kunci. Ka gane fatawan yanzu ko" ya ce cikin murmushi.

"Ni dai Baba ba zan je ba, zan taimaka maka a naka sana'a kafin in samu gurbin karatun" yace yana gyara zama, Alhaji Ashiru bai musa masa ba don baya so ya ɓata rai, saboda fahimtar su ɗaya faranta ma Ubaidullah rai daidai yake da faranta ran Mahaifin su in da ace yana Raye. 

Barka da sallah in advance 💞💕😘😍
In na samu sukuni in baku Goron sallah in ban samu ba mu haɗu rana ita yau Insha'Allah.
Love u ol irin ba kaɗan dinnan ba.

MAKANTAR ZUCI Where stories live. Discover now