Babi Na Shida

1K 312 142
                                    

Kuka sosai take a cikin motar, ba ta samu ganin karamar 'yar ta ba duk da tana tunanin kila tana makaranta kasancewar watan Maris ake, "ba'a cike wata biyu ba kenan fa da zuwan su, kenan ko tarewa ba ta yi ba, toh auren ma duka wata nawa ne?" tace a bayyane hakan ya dawo da hankalin wanda ke kusa da ita zuwa gareta. 

"Haba barrister, da ilimin ki da komi kina neman zautar da kanki, gani nayi ma dai yarinya mai rasuwa ba sabawa kika yi da su ba, ina ce khul'i kika nema kika bar arziki, na tabbata da kina gidan kowa nan se ya dangwali arziki" cewan matar yayanta da tun fitowarsu hankalinta ke kan naman da ba'a ko sa musu a Leda ba, ga uban juice juice da ta gani ai yaci a ce an basu ko da na sha a hanya ne amma kudin mai kawai Justice ya ba direba.

"Haba debbo Hamma, ke dai kin ga haza da son abin duniya, Allah hoinu" cewan Sakina kanwar Batula tana mai harare harare. Nan dai motar ta cigaba da tafiya tsit, kowaccensu da abin da take saqawa a ranta. 

Gidan iyayensu su ka isa wato babban gidan su Batula da ke unguwar Bekaji a 

Jimeta da ke yola, gida ne babba mai sasa-sasa. Sashin Alhaji Aliyu modi su ka nufa nan su ka iske mahaifiyar su Batula Hajiya Hadiza zaune da sauran yadikkon su da ba'a yi tafiyar da su ba. 

Jikin mahaifiyar ta Batula ta isa, nan ta sa kuka mai tsuma zuciya. Duk wanda ke wajen sai da ya tausaya mata, babu wanda ya hana ta, sai da tayi mai isanta sannan mahaifiyar su ta miko mata hankicin ta ce

"Ya isa haka, maza share hawayen ki, abin er fari ɓoyewa ake" tace cikin raɗa, mutane se ganin Batula na murmushi, saboda tun da ta tashi in aka yi zancen kawaici ga ɗan fari se ta dara. 

"Adda Ummi Shike nan mun rasa Amma? Abu kamar mafarki, yayyafa min ruwa in farka kinji" tace tana kallon mahaifiyar ta da su ke kira Adda ummi. 

"Muma wata rana duk can zamu je, Allah ya kyautata namu bayan tasu" tace tana share kwalla, tasan 'yar ta na cikin wani hali, ta san ɗacin rasa abin da ka haifa, amma duk abin da hakuri bai baka ba rashin sa bazai baka ba. 

A nan gidan mutane su ka fara tururuwan zuwa ta'aziyya, yayin da Tsegumi.com ya fara aiki akan irin tarban da aka yi masu. Anan ne Adda ummi ta tsinci labarin kuma tun da ta tabbatar hakan ne ta nemi a bata lambar Hammad. 

"Assalamu Alaikum warahmatullah, sunana Hajiya Hadiza, mahaifiyar maman matarka, ya mu ka ji da Hakuri?" tace kai tsaye bayan ya ɗaga wayar.  Sauke wayar yayi yana saka ta a sifika 

"Adda Ummi ina yini" ya ce yana gaishe ta, bayan sun gama gaisawa ne tare da yi ma juna ta'aziyya sai ta ce. 

"Naji wani labari ne mara daɗin saurare, shin menene musababbin mutuwar Aisha" tace a kausashe. Sai da ya ɗaga kai ya kalli Justice Ubaidullah da ke tsaye a gefen sa yayi murmushi sannan ya ce "Bugun zuciya ne" yana kaiwa nan ya kashe wayar gaba ɗaya. 

"kayi yanda na ce ko na ba Yan jarida video din Amma tana bayyana abin da kake mata, amma se na fara da dangin mahaifiyar ta" yana faɗin haka ya shige motar sa yana mai barin wajen. Baki a sake Justice ya bi shi da kallo zuciyar sa na Dana sanin  kiran Hammad ɗin da yayi da fari. Yayin da itama Adda Ummi ta saki baki tana kallon wayar. Gode Allah tayi babu kowa a wajen don bata san irin bayanin da za ta masu ba.

***

A ɓangaren su Ubaidullah kuwa tun bayan tafiyan mutan Yola yaji duk ya tsargu, ace an zo ta'aziyya babu mijin marigayiya alhali duk an san cewa bata tare ba, kuma ya bayyanawa duniya irin son da ya ke ms surikin na shi. Hakan ya sa ya ɗaga waya ya kira shi

"Hammad wai ka shirya tozarta ni ne ko menene niyyar ka da jiya baka zauna gidan makoki ba yau ma babu kai balle mu yi tunanin ganin dangin ka" ya ce a fusace ba tare da ya amsa gaisuwan Hammad ba, shiru ya ziyarci tsakanin su har se da ya sake cewa "hello! Hello!!" Sannan Hammad din yayi ajiyar zuciya, ranshi na quna ya ce

"Baffa muna amsar gaisuwa anan ne shi ya sa, kuma ban jin daɗin jiki na" ya ce a sanyaye yana kokarin danne abin da ke taso masa kasancewar zaune yake gaban Mamma.

"Amma ka san nan ɗin za'a fi bukatar ka ko, ka bar su mahaifiyar taka anan su amsa a madadin ka, kayi maza ka zo nan, ɗazu na ce da yan jarida ka je ka dawo, yi maza Allah ya maka albarka" bai jira amsar sa ba yana gama faɗi ya ajiye wayar, sannan ya koma mazaunin sa. 

Ba'a fi minti goma ba Hammad da Mamma ta taso ya iso, don tun da ya mata bayani ta gaskata zancen justice ta sa shi fitowa ba shiri. 

Sabuwar ta'aziyya aka sake masa, yana ta amsa ma mutane kafin ya samu wata rumfa a gefe ya zauna. Haka su ka cigaba da karɓan gaisuwa har yan jarida su ka zo don su ɗauki rahoto amma bai iya faɗin komi ba sai kuka sosai da yake yi, mutane da dama sun tausaya masa don wa'inda su ke da alaka da shi ko justice na kusa sun shaida irin son juna da su ke yi. 

"ko zaka faɗi adadin kwanakin aurenku?" wata yar jarida mai nacin tambaya ta ce da shi. 

"toh zan iya cewa kwanaki masu tarin albarka, da Rahman ubangiji, zan so ku kyale ni haka, mu haɗu mu yi mata addu'a ko zasu zama mata abokan hira a yanzu da bata da kowa sai halin ta" yace yana mai barin wajen. Gaba ɗaya wa'inda ke wajen sun samu sanyin jiki tare da tausaya masa. Addu'a su ka mata kamar yanda ya bukata, kafin duk suka watse kasancewar an fara kiraye kirayen Sallah. 

Se bayan sallan isha'i ya yi sallama da su Justice zai koma, anan ne justice ya tako in da yake don masa rakiya. Tafiya su ke ba uhm ba um um har su ka kai motar Hammad. 

"Hammad ka yi hakuri, rai baya wuce ajalinsa" ya ce yana dafe marfin motar, fitowa Hammad yayi ya tsaya gaban sa kamar zai bankaje shi, sai ya tsaya yace 

"kuma ko wane rai da SILAR AJALINSA, me kayi ma matata zuciyarta ta buga" yace yana kallon sa, daburcewa Justice yayi don tsoro yaji kar Hammad ya make shi a wajen. Bai kai ga tattaro Natsuwa ba wayar Hammad din yayi kara, nuna masa sunan yayi take cikin Justice ya ɗuri ruwa ganin Adda Ummi ce mai kiran. Matar da ta sa karfin ikon ta na matantaka ta tsinka masa igiyar aurensa da wacce ya fi so a duniya.

***

Zaman daɓas yayi a wajen bayan wucewan Hammad, ta ina zai fara, 

"kayi yanda na ce ko na ba Yan jarida video din Amma tana bayyana abin da kake mata..." Ya maimaita kalaman Hammad, tunani ya shiga yi shin menene wannan abin da zai sa shi yi.

"kila kuɗi zai bukata" ya faɗi a bayyane, take yana murmushi don ya san wannan ba zai taɓa zama musu matsala ba, amma kuma tunawa da yayi adda Ummi ta kira ne take zuciyarsa ta fara rawa yana mai cike da tsoro. Cikin gida ya shiga da sauri, don son sanin abin da ya auku lokacin da su Batula su ka iso gaisuwa.

"ai kuwa basu  wani daɗe ba su ka fito kari wani abin akai masu" ya fadi yana karasawa cikin gida. Anan ya karasa bai ɓata lokaci ba ya nemi labarin. Bai bata lokaci aka faɗa masa abin da ya faru, ji yayi Ransa duk ya ɓaci, rashin sanin hukuncin da zai yi yayi. 

Ehem. A tattaro mutunci. Ayi voting, commenting, recommending har ma da sharing.

Ina sonku sosai da sosai.

MAKANTAR ZUCI Where stories live. Discover now