Marayu Ma Ya'ya Ne

1K 102 12
                                    

Assalamu alaikum.

Bako da yaushe rayuwa kan baka zabi ba, kamar yanda ka diro cikinta batare da shawara ba, haka kake barin ta ko da baka shirya ba. Sai dai cikin hakan a kullum ba zaka rasa abin godiya ga Ubangiji ba.

Akwai hikima da tarin dalilai a cikin tsari da rubutun kaddara da samuwar shi ta kasance tun kamun taku, ta gefenka inka duba ba zaka rasa ganin kana nan yara marayu ba. Da yawan lokutta ka kan kauda kai daga halin kunci da rashin gatan da suke ciki badan zuciyarka bata son taimaka musu ba, sai dan taka dawainiyar tana da yawa.

Sai dan abinda zaka iya taimakawa dashi din kana ganin kamar yayi kadan. Tare da NAJ CHARITY FOUNDATION zaka samu damar taba rayuwakan marayu daga biyu abinda yai sama. Rayuwar bata da yawa. Karka jira lokacin da baka da tabbas akai, karka jira lokacin da bakasan zuwan shi ba.

Da #500 zaka iya kawo canji a rayuwar yaran da suka yanke rai da samun wani sauki cikin rayuwar da bata da yawa. Ba mai yawan kudi a banki bane mai wadata ko arziqi, mai wadata shine mai bayarwa batare da tunanin rasawa ba. Kaman yanda suka zama marayu batare da zabi ba, naka yaran zasu iya zama batare da zabi ba.

Kaman yanda zaka so a Allah ya nada mai kula dasu in kasa ta rufe maka ido, hakan zaisa ka taimaka wajen kawo canji a rayuwar su batare da son zuciya ba. Kadan din daka raina na nufin komai a wajen su.

Tare da NAJ CHARITY FOUNDATION #200 ma batai kadan ba, karka duba yawan kudin, ka duba girman niyyar.

Saka a asusun NISAAU AHLIL JANNAH CHARITY FOUNDATION

0334993079
NISAAU AHLIL JANNAH CHA. FDN
GTBANK

JAZAKUMULLAHU KHAIRAN

MAKANTAR ZUCI Where stories live. Discover now