Babi Na Bakwai

972 241 121
                                    
Dedicated to MudassirDanArewa ga mai wakar biki ko suna ko na siyasa ko na kasuwanci ya same shi. Insha'Allah a next chapter zan sa muku YouTube ɗin wakar da yayi ma Kungiyar fikra mu haɗu mu yi rawa da disco ga wa'inda ke son audio kuma mu haɗu a WhatsApp 😍💞💕. Ubangiji Allah ya faranta maka kamar yanda ka yi mana ya biya maka bukatu na duniya da lahira. Ciyaladi na godiya a madadin yan fikra.
#anatare
#sonso
#fikrawriters

Nauyi yaji kansa yayi kamar an ɗaura dutsen mambila akai, dafe kan yayi sai kuma yaji kirjinsa ya ɗauka take ya fara safa da marwa a tsakar falonsa yana canki cankin kama kai da dafe kirjinsa. Samun kansa yayi a kofar ɗakin hajiya Jamila, bai san lokacin da ya isa ba don ba cikin hayyacinsa yake ba, sautin tafiyar sa kawai zai tabbatar maka da ransa a ɓace yake. Bai iya yin sallama ba don bai son abin da zuciyar sa ta gama haddacewa ya ɓata. Kamar yanda bai sa ma ransa tayi barci ba don agogon GMT na nuna karfe takwas sa minti ashirin ne wanda yake daidai da karfe tara da mintuna ashirin a Jalingo na Kasar Najeriya.

Zaune ya iske ta kan gado hankalinta kacokan na ga shirin series din da take kallo na Kasar Koriya mai taken 'Falsely' zama yayi a kusa da ita ya kamo hannunta sannan ya furta

"me kika yi ma 'yan ta'aziyya da su ka zo da ga Yola?" bai jira amsar ta ba ya ɗaura da faɗin 

"kin san ita ce ruhin gidan nan, ba don ta juya min baya ba babu abin da zai sa kaddaran ki ya biyo da ke hanyar gidan nan a sunan mata balle har ki samu daman fiffika da ganin kin isa ki wulakanta wasu" duk da faɗi yake yana wasa da hannunta hakan bai hana ta jin wani irin azaba a zuciyar ta ba wanda babu yanda za'a yi ta kira shi sa kishi sai sai ta danganta shi da ciwon da ke neman rayuwar ta. Duk yanda ta so ta basar ta nuna ba komi ba kamar yanda ta saba a duk sanda makamancin hakan ya faru, nauyin da zancen ya mata a maƙoshi ya sa ta amayar da faɗin. 

"sai naga ruhin ita ce zuciyar wani gida don in ido na ba karya ya min ba ciki na gano lafe a jikinta. Duk wanda ta haifa bai ishe ta ba amma nan biyu ta haifa kiyayya ya sa ta kasa zama..." marin da ya kwashe ta da shi ne ya katse mata magana. Cikin fushi ya ce

" ranar da zaki kara tunatar da ni Batula mallakin wani na ne a ranar zan ɓatar miki da rayuwar ki, alkawari ne wannan kuma kin san bana wasa da alkawura" yace yana mai ficewa daga ɗakin zuciyar sa cike da bakin ciki ita Kuma ya barta cikin tsoro da firgice.

 ***

Investment quarters ya nufa, ɗakin Royal suits da ya Kama na shekara biyar a shield hotel ne ya Shiga, watsa ruwan sanyi yayi a jikin sa, ya dan samu natsuwa sannan ya ɗauki waya ya latso lambar Hammad.

Nauyi yaji kansa yayi kamar an ɗaura dutsen mambila akai, dafe kan yayi sai kuma yaji kirjinsa ya ɗauka take ya fara safa da marwa a tsakar falonsa yana canki cankin kama kai da dafe kirjinsa. Samun kansa yayi a kofar ɗakin hajiya Jamila, bai san lokacin da ya isa ba don ba cikin hayyacinsa yake ba, sautin tafiyar sa kawai zai tabbatar maka da ransa a ɓace yake. Bai iya yin sallama ba don bai son abin da zuciyar sa ta gama haddacewa ya ɓata. Kamar yanda bai sa ma ransa tayi barci ba don agogon GMT na nuna karfe takwas sa minti ashirin ne wanda yake daidai da karfe tara da mintuna ashirin a Jalingo na Kasar Najeriya.

Zaune ya iske ta kan gado hankalinta kacokan na ga shirin series din da take kallo na Kasar Koriya mai taken 'Falsely' zama yayi a kusa da ita ya kamo hannunta sannan ya furta

"me kika yi ma 'yan ta'aziyya da su ka zo da ga Yola?" bai jira amsar ta ba ya ɗaura da faɗin 

"kin san ita ce ruhin gidan nan, ba don ta juya min baya ba babu abin da zai sa kaddaran ki ya biyo da ke hanyar gidan nan a sunan mata balle har ki samu daman fiffika da ganin kin isa ki wulakanta wasu" duk da faɗi yake yana wasa da hannunta hakan bai hana ta jin wani irin azaba a zuciyar ta ba wanda babu yanda za'a yi ta kira shi sa kishi sai sai ta danganta shi da ciwon da ke neman rayuwar ta. Duk yanda ta so ta basar ta nuna ba komi ba kamar yanda ta saba a duk sanda makamancin hakan ya faru, nauyin da zancen ya mata a maƙoshi ya sa ta amayar da faɗin. 

MAKANTAR ZUCI Where stories live. Discover now