Babi Na Goma Sha Daya

618 114 17
                                    

Wannan shafin sadaukarwa ne ga yayata abokiyar shawarata Anty Fatima (Ummu Hanan AKA maman fikra) Allah yakara tsawon rai mai albarka.

Da labari fal a bakin ta ko da ta isa Jimeta, ta samu tarbo daga iyayenta da yayyinta maza. Bayan sun gama cin abincin rana mahaifin su ya fita zuwa Asibiti daga Adda Ummi sai yayyinta sun zauna suna hira, Batula dai tayi jigum labarin Ubaidullah na ta mintsilin ta, sai mui mui take da baki har dai Adda ummi ta ankare da ita ta ce "Batula bakin nan da labari kenan" tace tana murmushi. Rufe fuska Batula tayi cike da jin kunya hakan ya sa yayyin nata fara dariya.

"ba kyau gulma fa" tace tana kara zumburo baki, tsokanar ta su ka shi ga yi har ta yi fushi ta bar wajen.

"kun ga ku bar min yar fari, aka ce ina yin ku ne, itace qawa aminiya" Adda Ummi ta ce tana mai mikewa. Dariya su ka saka har qannenta. 

A daki ta iske ta zaune gefen gado, zama ta tayi kusa da ita kana ta riko hannayenta duk biyu. 

"Faɗa min Batula mun yi babban kamu ne" ta ce tana dariya cike da farin ciki, shike nan wa'inda ke nuna ta a gidan biki da suna ko duk wani taron mata akan yar ta na jami'a babu wanda zai zo ya aureta. Wani sa'in har shaguɓe ake mata akan in bata bi a sannu ba zata goya yan gaba da Fatiha. 

Daga kan da Batula tayi alamun eh ya sa Adda Ummi sakin wani kabbara, hakan ya sa Batula sakin baki tana kallonta cike da mamakin farin cikin  mahaifiyar su, sai gani tayi kwatakwata shekarunta ashirin da ɗaya ballantana a ce ta tsufa ba aure ko a ce an cire rai za ta sami mijin aure.

"Ɗan ina ne?" Ta tambaya cikin zakuwa. Hakan ya sa Batula kwashe duk abin da ta sani ta faɗi mata a kansa. Shiru Adda Ummi tayi don ta hango rikicin da ke cikin wannan al'amari kasancewar sa ba ɗan yola ko wani sashi na yola ba, gani su ke Fulanin sauran wajajen na da nakasu bi ma'ana ba su zama cikakkun Fulani ba.

"shi ke nan boddo'am, mu yi addu'a Allah ya tabbatar da khairan" tace zuciyar ta cike da tunanin madafa. Har ga Allah ta fi so yarta ta auri wanda ta ke so, kuma daga bayanin Batula ya fito gidan ilimi, mai ya fi wannan garɗi ka auri maabocin ilimi boko da addini. 

"Kinga tashi mu je wajen su kar su cigaba da miki dariya" Adda ummi tace tana mai jan hannun Batula.

Suna fita kannen ta na shigowa daga makarantar boko inda su ke tsayawa su yi extra lesson. "Adda manga! Adda manga!!" suke fadi suna masu rungumar Batula.

Nan ta zauna su ka cigaba da hira, tana tambayar su suna bata amsa, kiran sallah la'asar ya tayar da su duka. 

***

Ko da Dr. Aliyu ya dawo daga harkokinsa, ya gabatar da salolin magariba da isha'i da ya kan yi kafin ya shigo gida, sannan ya ci abincin sa na dare tare da matarsa wanda hakan ya zame masu farali gare su duka. Sai bayan ya samu natsuwa ta ke faɗa masa labarin Ubaidullah, har ga zuciyar sa bai laminta ba kuma fuskar sa bata ɓoye ba. Shiru su ka yi na wasu lokutta kana yace 

"Ban so ta wuce Adamawa, jalingo ta yi nisa Ummi" yace yana mai share baki da hankici. 

"Hamma'am ba zan so ka kasance cikin masu kyamatar wasu al'umma kawai don bai kasance cikin taka Al'umman ba, ka zame mata gata matukar ba ka same shi da gurɓataccen ɗabia ba" ta fadi ciki sanyin jiki, amma kallon da ya ke hurga mata ya sanya ta yin shiru. 

"Ai ban san sanar da ni kike ba bayan kin gama yanke hukunci. Allah ya Baku nasara" ya ce yana mai mikewa, shi abin da ya tuna labarin Sheikh Hamze da ya kasa mantawa, ya san ance da yawa cikin yaransa sun saki aikin malantar sun kama Sanaa amma duk da haka ana zuwa tsangayar don neman taimako. Yanzu a ce yar da yake son ta zama mutum, al'umma ta amfana da ita ce zai dauka ya kai tsangaya Sheikh Hamze. Girgiza kai kawai ya ke yi tun da ya fita don bai san ta ina zai fara ba, ga matarsa ta juya masa zancen zuwa wani abin.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Mar 26, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

MAKANTAR ZUCI Where stories live. Discover now