Babi Na Biyu

1.1K 273 75
                                    

Iska ake kamar zai ɗaga bishiyoyi tun daga jijiyoyinsu, hadari ne a garin, ya haɗu yayi baki qirin duk kuwa da cewa watan Oktoba ake hakan bai hana ruwa saukowa kamar da bakin ƙwarya ba.

Amma ce zaune tana cin abincin da aka kawo mata, ba zata ce bata jin dandanon girkin ba amma kuma chusawa take don tsare ta da Dr Hammad yayi.

" Na qoshi" ta ce tana mai kallon shi cike da shakka, ba wai don ba ya mata dariya bane ya sa take shakkansa, Tsabagen kwarjinin da Allah ya bashi a shekarunsa na ashirin da shida a duniya.

"cinye shi fa zaki yi, gara ma tun wuri ki cinye" yace a dake. 

"Hamma" ta faɗi cikin sigar tausayi

"ni ba hamman ki bane gara ki je can ki nema, bana wasa da wanda bai daraja iyayemsa" yace yana haɗa rai. 

" ka dena hukunci da labarin da ka ji daga gefe daya in ba haka ba zaka wayi gari babu azzalumi mara adalci sama da kai. Ina son Baffa fiye da tunanin ka Kafin ya kona min future, da Ace kisan kai mai sauki ne, kuma ba zunubi bane inaga da tuni Baffa ya daɗe a lahira, an ce baa ɓata ɓarna da ɓarna, shine kawai" tace tana wani yake da ya kasa gane abin da yake nufi.

"yanzu me kike shirin yi da auren tsoho, ina za ki kai shi? Ki natsu ki yi karatun ki ta yanda za ki rike kanki da ya'yan ki" ya samu kansa da mata magana cikin sigar lallashi a karo Na farko tun bayan sati ɗayan da tayi kwance tana jinya

"ya'ya? Ai shi yasa na ce sai baba mai gadi ka ga ya tsufa ba haihuwa zai yi ba, in aure shi babu mai min gori ko Ya ma ya'ya na gori. Ko da yake wa zai iya aure na in ba Baba mai gadi ba" tace tana dariya, dariya mai cike da tururin kona zuciya amma inaa bata fasa ba sai da ta yi mai isanta. Ko da ta tsaya da dariya, Dr Hammad ta gani tsugune da hannu sama kamar ya na rokon ta. Hakan ya sa ta saki baki tana kallon shi.

MAKANTAR ZUCI Where stories live. Discover now