Zaune su ke sun zagaya mahaifiyarsu, tun bayan da ta kira su ta shaida masu auren qanensu hankalin su ya tashi, su tun da su ke ba su taɓa jin anyi aure irin haka ba, sai auren qanensu da su ka gama kwallafa rai akan irin shagalin da za su yi ne kawai za'a kira su Ace an ɗaura aure. Da kyar su ka bari aka wayi kafin mazajensu su sauke su a kofar gidansu da ke unguwar gadi a cikin birnin jalingo.
"Toh wai da kuka sa ni a gaba me kuke nufi, warware auren za'a yi ko duka na za'a yi" tace tana kallon yanda su ke cika su na batsewa.
"A'a Mamma, shin auren ma ya inganta? Babu fa waliyin shi a wajen sannan a yanda ya ce mutanen wajen da shi takwas ne, ni fa kar a halasta zaman zina nake gudu" babban su Aisha ta faɗi tana mai addu'an haka ya zama hujjan da zai sa a warware komai.
"shin in an tura ki islamiyya wani gun kike zuwa? Karatun fiqhu da kike gadara kin samu ya tashi a banza kenan. Shaidu nawa ake bukata kafin aure ya zama ingantacce?" mahaifiyarsu ta tambaya taba kallon su ɗaya bayan daya. Ganin sun yi shiru ne ya sa ta cigaba
" mace sai da waliyyi wanda zai kasance namiji musulmi mai hankali daga cikin ubanninta, shi kuma namiji zai iya neman ma kanshi aure ko wakilin sa ya nema masa. Sannan dole sai an samu shaidu balagaggu, masu hankali kuma musulmi maza biyu ko namiji ɗaya da mata biyu.
Tun da an samu wannan, an biya sadaki, yana son ta kuma da amincewar yarinya aka yi me zai hana auren yiwuwa, ban son mugun tunani, mu yi zaton alkhairi kullum don Allah " tace tana kallon su, a hankali su ka fara sakin fuskokin su, har dai su ka fara hira.
" toh ni wai Mamma yaushe ya haɗu da yarinyar da har ya fara sonta, ko dai huce Haushi ya ke son yi don an hana masa Bingel" Sumayya yayar sa ta biyu ta ce tana dariya. Don ita kaɗai ta yi adawa lokacin da yake neman auren Bingel a cewan ta ba za su bashi ba ita ba. Yan uwan su ka yi mata caa wai ba ta son yarinyar ne kawai.
ESTÁS LEYENDO
MAKANTAR ZUCI
Misterio / SuspensoRayuwa kan zo ma kowa da kalar qaddarar sa, walau khairan ko akasin hakan. A duk yanda ta zo maka da kamata yayi ka rungume shi cikin gode ma Allah akan sauran ni'imomin da ya maka ba tare da sanya damuwa ba. Zainab (Amra) da Fatima (Amma) suna cik...