Babi Na Takwas

983 178 60
                                    


August 1975

 Jihar Gongola na arewa maso gabashin Nigeria. Jiha ce da ta amince da yaren fullanci a matsayin yaren amfani. A tsakanin yola da jalingo akwai wani Alkarya da ake kira da  Tunga, Fulani ne kaɗai a wannan Alkarya, an ce asalin su daga Chadi ne wasu na cewa Fulani ne daga gabashin Faransa.

Yammacin Tunga akwai tsangayar Sheikh Hamze. Duk wanda ke Tunga da kewaye ya san girman malanta  da dattako na Shehi. Hakan ya sanya shugabancin Tunga ya koma hannun Sheikh Hamze. 

Gidan sheikh Hamze gari guda ce don girma, akwai bukkoki huɗu a tsakiya, sannan akwai wasu falle ɗaya-ɗaya a gefen dama daga bukkoki Wa'innan za su kai dakuna talatin, daga gefen hagu kuma gidan sama ne, mai ɗakin a kusan goma. Ta gaba kuma akwai ɗakuna da wasu bukkoki, ta baya kuma su kicin ne da banɗaki. Daga nan in mutum yayi gaba  kaɗan zai iske turken shanu da shanaye fiye da dubu. Duk ginin an yi su ne da laka da ya ji wuta sai wasu wajajen an sanya duwatsu. 

 Yana da mata huɗu kowaccensu ta mallaki bukka ɗaya da ɗaki ɗaya a Saman bene. Sannan yana da kwarkwarori goma sha uku da su ke zaune a falle ɗai-ɗai dinnan. Sauran ɗakunan kuma Yaransu ne da su ka tasa kafin a aurar da su ko su yi aure. Ɗakunan farko kuma na surukan gidan ne walau matan ya'ya ko matan almajiran malam. 

 Duk da kasancewarsa ɗan shekara tamanin a duniya ba'a fasa yi masa haihuwa ba don ko a cikin kwarkwarori akwai yan shekara goma sha.

Ana cikin ruwan sama a ranar Talata 12 ga Agusta shekara 1975, a ranar amaryar da ya aura shekaru biyu da su ka wuce ta haifi ɗa namiji. Duk da ta koma gidan su wanka a cikin mubi hakan bai hana Shehi yanka shanu don bada sadaka, ba wai don ya rasa Magaji ba sai don soyayyar da yake ma mahaifiyar yaron.

Ko da bakwai ya zagayo raguna biyar ya yanka banda shanu ya kuma sanya ma yaron suna UBAIDULLAH. 

Anyi taron suna anyi shagali an watse, ranar sunan da dare sai ga  sako wai Shehi ya yi baƙi alhali dokan gidan ne matukar Shehi ya shiga ɗaki toh baya fita, saboda in su ka idar da isha'i ya kan zauna ya ji bukatun mutane, masu neman addu'a, taimako, shawara, tubarraki da sauransu.

"kar dai bakin da nake gani wajen lissafi ne ya qarato da wuri" ya faɗi yana mai mikewa. Sai da ya shiga turaka ya kimtso kafin ya fita wajen da aka je yayi baki.

Motoci ya gani kirar volks wagen da pijo 504. Murmushi yayi sannan ya isa gare su. Fitowa sojojin su ka yi, su ka buɗe kofar motar don fitowar wanda ya ke cikin motar, Sara masa su ka yi kafin su ba shi hanya.

"Allah gafarta malam ko zamu shiga daga ciki ne" yace yana gurfanar da kansa alamun biyayya. Shehi bai yi tunani biyu ba ya juya su ka biyo shi. Gaf da za su shiga gidan na gaban ya tsaida masu take masa baya. Sai su biyu kawai su ka shigo ciki, nan su ka yi gaisuwa sannan Shehi ya sa musu ido ma'ana yana saurarensu.

"Wannan shine Gwamnar jihar nan, ni kuma amininsa ne, aiki mu ke so na gaggawa na san babu wanda zai iya mana wannan aikin se kai, ka taimaka mana daga kobo ɗaya zuwa naira dubu zamu biya ka" yace ya ɗan dakata. Yana son Shehi ya maganta. Jin yayi shiru ne ya cigaba da faɗin. 

"wasu kuɗaɗe ne su ka ɓace a gidan gwamnati, yanzu shugaban Kasa Ya bukaci da a fito da su. Kasan soja yanzu sai a kai shi gidan maza, taimaka mana s rufe bakin kowa daga cikin al'amarin nan" ya kammala yana rusunawa.

"sai dai ku yi aikin da kanku, matukar ba haka ba toh ku yi hakuri" ya ce yana gyara zama akan buzun da ke shimfide a tsakiyar ɗakin yayin da su ke zaune Saman kujeru. 

"Alright, sai in yi, Baba kada a samu kuskure fa don ba zan iya risking life ɗina ba, kwata kwata shekaru na arba'in, ba zan yarda in bar yara kanana ba in dawo yayin da su ka girma" ya karasa yana kallon Shehi da ke murmushi.

"wala ya'uduhu zaka rubuta ka shimfide abin sallah akai ka yi rakaa hamsin ba tare da sallama tsakanin su ba. Yanda gawa baya magana haka shugaban kasa zai yi shiru akan wannan lamari." Shehi ya fadi yana mai mikewa, su ɗin ma su ka Mike ya taka musu, duk yanda su ka so ya amshi wani abin hannun su ya ki yace in komi ya lafa su bada sadaka. Godiya su ka dinga yi har su ka rabu a bakin motarsu ya koma cikin gida.

***

A haka rayuwa ta cigaba da tafiya a gidan Shehi har Ubaidullah ya cika wata tara, sai a lokacin mahaifiyar sa ta dawo ɗakinta daga wanka da taje gidan su. Sosai Shehi ke jin soyayyar Ubaidullah a zuciyar sa, yayi masa kyaututtuka na kin karawa, yayi alkawura akan bashi ingantaccen rayuwa, ya tara ya'yan sa kaf su tamanin ya bar musu amanar ubaidullah har wa'inda ba su san menene alkawari ba.

"ina so yayi karatun boko, ya zama soja ko alkali" ya faɗi a karshe wanda hakan ya girgiza duk wanda ke zaune don kowa ya san sheikh Hamze da kin boko kiyayya ba ko kaɗan ba. 

Sati biyu bayan taron sai ga yan sanda da sojoji fiye da talatin, su ka zagaye gidan Sheik Hamze kafin su taso keyar sa daga cikin almajiransa da yake koyar da su littafin Ashafa.

Yan boko cikin ɗaliban ne su ka yunkura don hana tafiya da sheikh amma zancen da ya fito bakin su ya firgita su inda su ka ce

"ya taimakawa yan fashi shiga gidan gwamnati da yin fashi" haka su ka ja jiki su ka bari aka tafi da shi kowa da abin da ya ke ayyanawa. Har zai shiga motar ya wai go ya kalli babban ɗan sa ya ce

"Ubaidullah!!!" ya juya ya shiga. Hankula sun tashi saboda ganin yan Tunga babban bango aka ɗauke musu. Da yawa sun san duk malantar sheikh baya taimakawa ɓarna amma kuma an ce ka ga mutum. 

***

Sai da aka yi Satu huɗu sannan aka gano in da aka kai Shehi, dalili kuwa shi ne rashin lafiya mai tsanani da Shehi ya fara. Yaransa manya biyu da wasu ɗaliban sa suka isa makurdi, zuwan su babban asibitin su ka iske shi kwance ya yarame, ga yan sanda shida da gadinsa. Kuka sosai su ka sa shi ne mai kokarin magana 

"ku yi hakuri, na daɗe da ganin baƙin nan, ban san zai zo da kusa ba. Amma kanal Dan fari ya ci amana," nan ya kwashe yanda su ka yi da gwamna ya faɗi musu. 

"Basu samu nasara ba sai suka cire kansu su ka ɗaura ni. Babu komi in ubaidullah ya tashi ya zama Alkali, sannan ya bi min hakki na ko min tsufansu" yace yana gyara zama. 

Gyara zaman ke da wuya ya yi miqa, shike nan rai bakon duniya. Nan yaran su ka sa kuka, shike nan mahaifinsu babu shi. Sun nemi a basu gawar amma su ka hana har sai da yan sanda su ka zo sannan aka samu aka basu. Gida su ka koma inda aka masa wanka aka shirya duban  mutane su ka halarci jana'iza ciki har da kanal.

Filin shakatawa a Wani sashe na Tunga.

Kaɗan daga shanayen Sheikh Hamze

Sheik Hamze

Sheik da yaransa

Babu yawa ku yi maleji. Kar ku damu da typos I typed directly here without editing.
Don't forget a yawaita faɗin LAA ILAHA ILLA ALLAH
ALLAHU AKBAR
SUBHANALLAH
ALHAMDULILLAH
a kwanakin nan mai albarka. Ku bada sadaqa ko da ta murmushi ne, a yi tilawa sosai
Duk don mu dace da Wa'innan kwanaki masu albarka.

MAKANTAR ZUCI Donde viven las historias. Descúbrelo ahora