Babi Na Hudu

1K 171 118
                                    

"kai dinnan karamin alhaki ne, ko Yusuf bai iya kare kansa ba na kora shi nayi ya qara gaba" ya maimaita yafi so a qirga. Kenan da yake tunanin da taimakon asiri mahaifinsu ya tsallake su yayi gaba ba tare da ya ko tuna da zaman su a duniya ba. Shin yana da rai? Kila ma ya yi aure ya hayayyafa amma duk da kalaman yayan baban nasu bai sa ya ji sauyi daga kiyayyarsa da ya ke ji ba. 

 "mstwww" ya ja tsaki da karfi yana mai jan motarsa daga haraban gidan. In bacin ya kira shi akan lallai yana son ganin sa bai ga abin da zai kai shi gidan mutumin ba duk kuwa da sanin da yayi basu da wani saura a cikin dangin Mahaifin su da yake makwafin uba sama da shi. 

 Sannu a hankali ya tuka zuwa gida, ya iske gidan makil da mutane makota ne da abokan arziki sai wasu daga cikin dangin mahaifiyarsu

Nan kakanni da abokan wasa su ka sa shi a gaba, tsiya su ke masa akan auren da yayi shi kuma yana washe baki. Ɗaki ya samu ya shige don yin wanka da shirin zuwa sallan magrib don an fara kira. 

***

Sannu a hankali sai da aka kwana uku da ɗaura masu aure ya isa gidan justice don ganin masoyiyar sa a da kuma matarsa a yanzu. Ya samu tarba mai kyau daga Mamma, inda ta dinga masa nasiha yayin da  fakaice kuma tana rokon arziki ne kan ya ɗaga ma yar ta kafa. 

"kai din ai sashin da ka fi wayau ne, ka san kugun Amma bai yi kwarin ɗaukan ciki ba a yanzu" ta faɗi tana  dakewa. Hakan ya sa justice jin faduwar gaba, kamar zai juya don yana daga bakin qofa ya jiyo ta amma ya dake ya karaso jiki a sanyaye. 

"kar ka sake tsuguna min, ban ga bambanci tsakanin ka da Almustapha ba, kai ɗin ɗa ne ba suruki ba" yace yana dago Hammad da ya tsuguna don ya gaida shi. 

"ka karasa ɗakinta ai babu wani hijabi yanzu tsakani" yace yana mai kwatanta masa dakin. Ba Hammad ba hatta Hajiya Jamila bata so haka ba, in ya lalube mata 'ya fa a bar su da rainon ciki kafin tariya. Bai bata fuskan da zata kawo korafi ba, hakan ya sa kallo ɗaya ta masa ta hadiye duk wani korafi da ke ranta. 

MAKANTAR ZUCI Where stories live. Discover now