"ka san abin ka da yaran yanzu, duk da wahalar da nake a kanta ba ta gani, tana aji biyar a sakandire yarinya ta zo min wai aure take so, auren ma tsohon mutum bara gabas kamar mai gadin gidana take so" yace yana ciccijewa. Take tausayin Khadi ya shiga zuciyar Hammad yana mai tir da halin ɗan yau.
"Da ka tura ta makarantar kwana inaga zai fi kyau ka nesanta su ka san sharrin zuciya" yace cikin halin tausayawa.
"Hmmmn ina ga duk faɗin jalingo za ka kirga masu biyan kuɗin da na ke biya ma ta na makarantar kwanan da take, Queens science na wudil din jihar Kano take. Bari naje likita na bar Mammansu cikin damuwa" yace yan mi juyawa don fita daga ofishin likitan.
"Queens Science!" ya ce cikin mamaki, girgiza kai yayi cikin takaici kamar ya samu daurina ya zane ta tas, kila abin da ta rasa kenan.
Aikinsa ya dukufa da yi ba tare da ya bari tunani ya hana masa sakat ba, duk da tausayin justice Ubaidullah kan ratso zuciyar sa amma bai bari hakan ya ci galaba a kansa ba.
***
Washe gari wajen shidan safe malamar jinya da ke wajen ta sanar da farkawan yar Justice, hakan yayi daidai da zuwan Ahlin justice, fuskokinsu babu wani walwala tun ba yar budurwar da a shekaru ba zata wuce sha huɗu ba. Kamannin ta da mai jinyar har ta ɓaci amma ita tafi mai jinyar haske.
"Adda kar ki tafi ki barni" tace cikin fillanci tana kamo hannun mara lafiyar da ta ke murmushin karfin hali.
"in lokacin ta yayi ai dole tafi ko? Ciwon Allah ma mutum ya tafi ballantana ciwon da kai ka siya ma kanka. Allah hoinu" ta karasa tana mai kallon mai ciwo tare da juyawa zuwa wajen ɗakin.
Da ido Amma ta bi ta, zuciyar ta fal da mamakin mammansu, matar da bata taba bambanta su da su Almustapha ba yaran da ta haifa don in ba tayi karya ba zata tafi son su da yaran.
ESTÁS LEYENDO
MAKANTAR ZUCI
Misterio / SuspensoRayuwa kan zo ma kowa da kalar qaddarar sa, walau khairan ko akasin hakan. A duk yanda ta zo maka da kamata yayi ka rungume shi cikin gode ma Allah akan sauran ni'imomin da ya maka ba tare da sanya damuwa ba. Zainab (Amra) da Fatima (Amma) suna cik...