01

854 66 3
                                    

Follow me on Wattpad @ Sadieey_Smart

Tsaye suke ko wacce sanye da uniform mai launin ruwan madara (Milk colour) da kuma kore wanda bai turu sosai ba (Army green) riga da wando sai kuma hijab wanda kadan ya wuce kirjin su(ga musulmai kenan yayin da sauran kabilun zaka bambance su ta hanyar rashin hijab din)...... Dalibai kenan a makarantar ta GIWO SCIENCE ACADEMY dake hanyar barin gari in ka nufi Ningi (wato Kano Road) cikin garin na Bauchin Yakubu.....

Tsaye a layin Assembly suna sauraren bayanin Principal din nasu cikin harshen turanci ko wacce ta kasa kunne tana sauraran shi in ka dauke dalibai guda biyu dake ta tadin su babu abinda ya dame su tsawa ya daka musu "Zainab nd Saudah! stop this nonsense" turo baki dayar tayi cike da rashin tarbiyya take 'yan harare hararen ta....

Gama assembly keda wuya ko wacce ta shige ajinsu domin daukan darussa. Mafi yawancin daliban sun hada group ne as usual suna tattaunawa kan abinda Principal yace wato na zuwan d'an sarkin garin makarantar tasu domin Bautar kasan shi (National Youth Service Corps. NYSC) wanda ya zabi yayi a wannan makarantar. Kowa cike yake da zumudi da kuma son ganin shi in ka dauke dalibai guda biyu dake zaune da littafi a gabansu suna dubawa hankali kwance yayin da daga kofar ajin kuma aka shigo yarinyar dai ta dazu ce wacce akaiwa fada lkcn assembly tana taku d'aid'ai har zuwa gaban board din gaba dayansu suka maida hankali gareta tana murmushi take duban kowacce cikinsu kana ta bude baki cikin harshen turanci dai har ila yau (wanda doka ce hakan magana da turanci during classes idan kuka koma hostels sai kuyi yarenku kasancewar makarantar ta boarding ce) ta fara magana "Albishirinku students" daliban da mafi yawansu 'yan korenta ne suka fara "sai Xieey tamu muna sauraren ki" ta sake murmusawa "shin kuwa kunsan waye zai zo yau?" bata jira cewarsu ba taci gaba "to ba kowa bane face YARIMA MUS'AB dake shirin zama mijina da zarar nayi candy" suka dau tafi da ihu "yeeeey sai Xieey Allah dai ya nuna mana prince dinki" daga musu hannu tayi tare da fadin "saboda haka kowacce cikinku ta kiyaye kar ta sake in kamata da laifin cin amanata in ba haka ba....." ta jinjina kai tare da wucewa wajen zamanta

Daya daga cikin 'yan Matan nan ne masu karatu naga tayi murmushi tare da girgiza kai taci gaba da sauraren Kawar ta wacce ke yi mata bayanin wani Topic da bata gane ba......

K'amshin turaren shi ne ya fara aiko musu da bayanin isowar shi wajen kafin ya sako kafa cikin takun shi na jaruman mazaje cike da kuzari bakin shi kuma dauke da sallama gabaki dayansu suka mike tsaye "Gud morning Sir!" suka furta a tare daya bayan daya yake kallonsu kafin ya furta "Morning u can seat down" kowa ya nemi waje ya zauna "Maa Sha Allah" shine abinda naji daya daga cikin 'yan matan ta furta a hankali nan ya fara gabatar musu da kanshi tare da sanar dasu cewar zai dauke su darasin Chemistry nan take naga wannan yarinyar ta fadada fara'ar ta da alamu wani abun ne yayi mata dadi.
Tambayoyi ya fara jifansu dashi nan take ajin akayi tsit ko motsi baka ji sai chan naga ta daga hannu (na kasa gano muku sunan ta fa readers) ta mike yace "can I know ur name first?(zan iya sanin sunan ki?" ta gyada kai "My name is Hafsat Hasheem Hussain" sannan ta fara mishi bayani dalla2 har zuwa karshe kafin ta koma ta zauna "give her a round of applause class (Ku tafa mata)" raf! raf! raf! Suka tafa don sunsan itace kawai zata iya bada amsa yadda ya dace a cikin su nan ya cigaba da tambayoyi itama ta gefenta ta daga hannu ya daga ta tare da tambayar sunan ta "My name is Hafsat Abubakar Lamido" Nuno ta yayi da yatsa tare da furta "Abbah Sadeeq?" ta gyada mishi kai tana murmushi shima murmushin yayi daga bisani ta bada amsa ta zauna duk wasu tambayoyi shi bayan Hafsat wacce 'yan ajin ke kira Lamido to fa kaf yarinyar da ya kira da 3ple H a zuciar shi itace ta amsa sosai ta burge shi sedai abinda ya bashi mamaki fuskar ta daure tamau take amsa tambayoyin babu ko 'yar fara'ar nan..... (Kuji min bako da shisshigi ko miye matsalar shi da dariarta oho).

Idan aka koma 'bangaren Xieey wato Zainab Ahmad Waxiri kuwa ran ta a dagule yake duk a sanadin murmushin da yayi wa Lamido (to pha).

A kankaro mutunci please follow, vote,comment nd share.

#Oneluv guys!

YARIMA MUS'ABWhere stories live. Discover now