13

162 19 2
                                    

Ammi tayi mamakin jin cewar zasuyi tafiya da Malam amman batayi musu ba ta shirya kayanta a jaka kala biyu dan ba'a sanar da ita ko tafiyar ta kwana bace hakama Mami da Inna sun shirya nasu kayan

"Wai Mlm ya kukayi ne da maneman auren diyar waccan matar" cewar matar Bappa Auwalu

Bai amsata ba tunda ya shigo yake ta tunani shi da farko yaji mamakin jin cewar dan sarki keson Mami yaso ace 'yarsa suka zo nema to amman gabadaya ynx kwakwalwarsa a dame take da maganganun Malam wanda bai fahimci komi ba sedai yaji dadin cewa da akyi dashi za'a tafi Bauchin gobe

A Bauchi kuwa bayan isowan su direct Fada suka wuce Abba Sadiq ya isa wurin 'yar uwanshi suka tattauna sunyi akan goben ta taho gidan mahaifinsu tare da Hafsa da kuma Yarima nan shima Mus'ab yake jin yadda sukayi a Gombe yaso ya daga hankali amma Ummy ta nuna mishi yy hkr zuwa goben suga abinda Allah zaiyi domin haka kawai mutumin bazai nemi ganin Kakansa kawai don zai bashi aure ba dole akwai lauje cikin nadi

Daga fada Abbah Sadiq direct New GRA ya wuce gidan mahaifinsu  bayan gaisawa da matan su biyu ya wuce bangaren Abbu kwance ya tardashi yana jan carbi Dattijo ne kyakkyawa wanda kallo daya zai tabbatar maka da cewar shi cikakken bafillace ne da kuma tsananin kamar da sukayi da dan nashi da kuma Yarima don babu abinda Prince ya bari daga kamannin tsohon in banda bambancin shekaru da ya raba su

Murmushi dauke a fuskar sa ganin dan nasa kwaya daya tal namiji a hankali ya mike ya zauna sukayi musabaha bayan sun gama gaisuwa yace "Abbu yadai yau na ganka kamar baka jin dadi"

"Lafia lau nake Abubakar kawai yanayin jikin tsufa sai kuma kwanaki biyun nan mafarkin Hafsatu dake yawan zuwar min na rasa dalili sedai in ban kwanta bacci ba sai na ganta"

Share hawayen da ya zubo mai yayi duk da cewar yana karami amman har yau ya kasa cire rashin mahaifiyar tashi a ransa sbd yadda suka shaku da ita sosai nan ya sanar da Abbu abinda ya faru yau a Gombe baiji komai a ransa ba yace "to Allah ya kawo su lafia in ka fita ka sanar dasu muna da baki a shirya abin tarbansu"

Amsawa yayi da to suka dan taba hira kafin ya mike ya masa sallama sai zuwa goben

Washegari

Karfe sha daya tayi wa su Ammi a Bauchi fada suka wuce daman Yarima na jiransu kasancewar Sadiq baisan gidan Abbu ba shi ya musu jagora daman su kawai ake jira Ummy da Abba Sadiq sun dade a can bayan an gaisa suka nufi falon Abbu yanayin abubuwan gidan tamkar dai gidan Sarauta ga kuma ma'aikata birjik suna hidimomin su

Zaune yake bisa kujera sukayi sallama Abba Sadiq ke gaba Malam da Bappa suna biye dashi sai su Ammi da sauran yaran a bayan su gaba daya a kan kafet suka zazzauna banda Malam da ya samu waje gefen Abbu bayan sunyi musabaha kowannen su dauke da murmushi kamar dai sun san juna gaggaisawa akayi sannan Malam yayi gyaran murya "amm..wato ranka shi dade maganace ke tafe dani mai muhimman ci sbd haka nake son duk wani dake cikin ahalinka y kasance a nan"

Duban Yarima Abbu yayi "Mus'abu kira su Yafendo duk kace ina son ganinsu ynx"

Cike da girmamawa ya amsa ya fita jim kadan suka dawo tare da mata guda biyu ganin taron ya basu mamaki suka kalli juna Abbu yyi musu nuni da wajen zama suka zauna tare da gaida Malam dasu Inna bayan kowa ya nutsu Mlm ya bude jakan da ya shigo dashi ya ciro wasu hotuna guda biyu da zani ya mika wa Abbu yace ko kasan wannan

Tun ganin zanin jikinsa ya fara rawa da hanzari ya karbi hoton yana kallo hawaye ne suka fara zuba a idanun shi ko da a mafarki ne bazai taba manta wannan fuskar ba babu wanda yayi magana sai da Abbu ya share hawayen sa ya dubi Malam yace "ina ka sami wannan bawan Allah tabbas nasan su ba shakka a kwanakin nan Allah ya nuna min bayyanar su a mafarki na suna Ina"

Yafendo da tunda taga zanin itama take zufa ta gyara zama don bazata taba manta ranar ba wanda yy sanadiyyar yayewan farin ciki a rayuwar su bayan a tunanin su hakan ne maslaha garesu amma sabanin hakan ne ya kasance domin daga ranan basu sake gane kan Mai gidan ba in fact abinda sukayi domin shin ma a lkcn suka rasa shi Malam ne ya katse mata tunani da ya fara magana

YARIMA MUS'ABTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang