Bayan an dawo daga sallar la'asar Abbu ya cigaba da lbr
"Gagarumin biki akayi na gani a fada a garin Bauchi yayinda hakan ya sake bakanta ran Bahira da Anoosha wacce a cewarta ko ita dake diyar sarki ai ba'ayi wannan bikin ba sai wata can diyar Fulani wadda ba 'yar kowa ba da dai sauran kananan maganganu na mata
Bayan auren mu da Su'ad matana biyu suka kafa mata kahon zuka sam bata da sake cikin gidan ta in kaga tana dariya to sedai tare da Muniba wacce suke kusan sa'anni domin fulanin su Su'ad basu irin auren wurin nan to akalla takai shekaru ashirin da daya naji dadi kwarai yadda take kula da Su'ad da nuna mata abubuwan da bata sani ba gameda al'amuran gidan haka dai suke zamansu lafia lau watan mu uku da aure Su'ad ta sami ciki munyi murna mara misaltuwa musamman Abba na tamkar ya zuba ruwa a kasa yasha sbd yana son yara amma ni kadai Allah ya bashi dan haka Extra kulawa ake bata a gidan yayinda su Anoosha ji suke ina wuta su jefa ta duk wani makirci sunyi dan su rabata da cikin amman abu ya faskara Allah bai basu iko ba a haka har ta haife diyarta mace ranar suna taci sunan mahaifiyata Halima gagarumin bikin suna akayi yarinya ta taso cikin gata da kulawa musamman wajen Muniba wacce take kira da Mama ta gefe daya kuma Anoosha (Umma) da Bahira (Yafendo) suke takura mata idan abin yafi karfin Muniba sai ta fada min na tsawatar amman a banxa ita kuwa mahaifiyarta bata ko daga idanu ta kallesu sbd kunya da kawaici irin na Fulani sai ranar da maganar takai kunnen Abba ya tsawatar musu domin ya nuna musu akan yarinyar zai iya korarsu a gidan abin ya bata musu rai matuka amman suka shanye suka daina kulata
Tun bayan haihuwarta ba'a sake haifar wani dan ba saida ta shekara goma Su'ad ta sake haifan danta namiji Abubakar Sadiq wannan haihuwa kam ya daga ma su Anoosha hankali musamman da mutane ke kiransa Magaji
Tun tasowar Sadiq ya nuna sam baya sha'awar sarauta don ko fada baison zuwa in an kaishi zaita kuka sai an maidashi gun mahaifiyarsa lkcn yana primary schl Sadiq yana da Shekara hudu Su'ad ta sami wani cikin wannan karon kam karara Bahira suka nuna bakin ciki a fili ita kam bata ko kulasu domin mace ce wacce bata son hayaniya sam kuma ma wannan Karon cikin yana bata wahala sosai kullum ba lfy ko abinci ba wani na kirki take ci ba wannan yasa bata cika ma fitowa daga daki baWatarana wanda yana daya daga cikin ranakun da bazan taba mantawa ba na shigo daga fada Muniba ta shigo bangare na hannun ta rike da na Sadiq da gudunsa ya karaso jikina na dagashi na daura kan cinya ina tmbyrsa ina Yayar shi yace tayi bacci a dakin Amma(Su'ad) Muniba ne ta gaisheni muna dan taba hira nake tmbyr ta ina Su'ad tace ta shiga dazu tana ga wanka take bata sake komawa ba kuma itama bata fito ba nace to dubota ko jikin ne naga bataxo ta gaisheni ba tun shigowata Muniba ta mike ta fita shiru² tafi minti talatin sai can ta dawo hankali tashe tace min bata ganta ba ta duba har bandaki bata nan kuma Sadiya ma yadda ta barta tana bacci kan kafet har ynx gurin take anya lfy kuwa na tashi da kaina muka fita nema abu kamar wasa an bincike kaf cikin fada babu ita na aika gidan abokina Mu'ayyad ko taje gidan shi tunda suna shiri da matarsa Zainab amma akace bataje ba hankali ya tashi domin bata taba fita ban sani ba sbd haka jikina ya bani babu lfy wasa² har washegari babu Su'ad muna ta faman nema wani dake kula da barga yaxo da Dan kwalin ta a hanunshi cewar a kofar baya ya samu nan muka tabbatar fita tayi aka bazama cikin daji amman har babu ko alamar ta cikin haka lbr ya iske Abba na take ya yanki jiki ya fadi domin yana matukar kaunar Su'ad tamkar diyar cikinsa aka kira likita yace ciwon zuciyansa ne ya tashi yayi mai allurai bai farfado ba aka nufi asibiti dashi nan fa tashin hankalin mu ya karu ga matana sai kuka suke haka ma Sadiya da yake da girmanta ga Sadiq shima kukan yake yana kiran Amma abubuwan duk da ba sauki kullum cikin neman Su'ad muke amman babu ko lbr ga jikin Abba kara tsanani yake gaba daya banda kwanciyar hankali harkokin fada ma sai Waxiri Mu'ayyad ne yake gabatar dasu iyayen Su'ad kullum cikin bani baki suke kan inyi hakuri indai tna raye za'a ganta amman ina har bayan shekaru biyar babu Su'ad ga Sadiq har ya gama Primary Schl amman kullum sai ya tambayi Muniba ina Amman su hakan yasa na tattara na kaishi England ya sami wanshi Mubin wato Babban dan Waxiri wanda ke Uni a chan tun daga nan bai dawo Nigeria ba saida ya gama Sec Schl nakan kai masa ziyara dai tare da yarshi Sadiya kuma dawowanshi yayi dai² da lkcn bikin Sadiya da Mubin sun nuna suna son junansu kuma munyi farin ciki babu bata lkc tana gama karatun ta aka sa auren su anyi bikin da sati daya ciwo ya kama Anoosha anyi jinyan asibiti amman ina basu gano ba ana ta faman na gida amma babu cigaba
Wataran da dare ciwon ya tashi sosai da kyar take numfashi ta aika aka kirawo ni nan take fada min maganganun da suka daga min hankali a cewarta sune sanadiyyar barin Su'ad gida aljanu suka tura mata sukai mata barazanar zasu kasheta in bata fita ba amman in yafe ta tayi hakan ne sbd kishi da kuma bakin cikin bata haifi wanda zai gajeni sarauta ba shima Sadiq taso kassara shi amman Allah bai nufa ba tayi ta rokon in yafe mata har Abba da yaxo dubata yaji maganar nan ya yanki jiki sai gawanshi aka daga daga gurin yayinda itama Anoosha a daren tace ga garinsu rai yayi halinsa
Washegari da safe akayi jana'izar su aka kaisu makwancinsu nayi kuka sosai sbd abinda ya faru ya daga min hnkl jin cewar sbd sarauta abin banxa an rabani da masoyiyata da abinda ke cikinta gashi kuma sanadiyyar hakan na rasa mahaifina take na yanke shawara cikin zuciyata kuma banyi kasa a guiwa ba bayan anyi kwanaki bakwai da rasuwan na tara mutanen fada na sanar dasu cewar nayi murabus
Kowa yayi mamaki tunaninsu ai Sadiq bai kai wanda zaiyi sarauta ba na fahimce su sai nayi murmushi nake sanar dasu ai Sadiq sam baya sha'awar sarauta don haka na daura Waxiri daga yau Mulkin garin nan ya koma gidan kanin Abba tunda daman ai duk mune amma ga mamaki na sai Mu'ayyad ya mike shima yace kafata kafarsa indai babu ni bazai iya mulki ba don haka sedai Mubin yayi to wannan shina asalin dalilin da ya maida mulki gidan Waxiri kuma Dan uwana Mu'ayyad nayi hakan ne kuma sbd hukunta matata Bahira domin Anoosha ta sanar min cewa da sa hannun ta a lamarin batan Su'ad wanda ita a tunanin ta har yau ban sani ba to kunji abinda ya faru kuma a ynx Mubin shi ke mulkin garin nan kuma mahaifin Mus'ab wanda yaje neman jikata a Gombe"
Abbu ya karasa lbrn kowa sanda ya tausaya masa ita kuwa Yafendo banda kuka babu abinda take ta shiga neman gafaran su Abbu yace ya yafe mata daman Allah ya kaddara rabuwarsu da Su'ad a lkcn koda batai sanadi ba amman ta nemi gafaran 'ya'yan da ta rabasu da mahaifiyarsu musamman ma Ammi da ko ganinta bata taba yi ba suma sukace sun yafe mata
Malam yaso su koma Gombe ranan amman fir Abbu ya hana yace dole su kwana biyu a gaisa da 'yan uwa Ummy tace zasu tafi da Ammi gidanta amma Mama wato Muniba ta hana cewarta sai gobe itama tanaso suyi hira da diyarta a dole ta hakura ta kwashi su Mami ta tafi dasu Sadiq kuwa yace kwana zaiyi da kakan shi Abbu susha hira to shima Yarima hakan yace duk da yaso yau su kwashi soyayya da Mamin shi amman baison rabuwa da dan uwa kuma amininsa Sadiq don haka ya zauna
Ammi kuwa sai goma tabar sashen mahaifinsu yana bata lbrn mahaifiyarta wanda ya fahimci kaf halayyarta tayo itama dai Mama hirar Su'ad tayi ta mata har suka raba dare kafin sukayi bacci
#Smart
YOU ARE READING
YARIMA MUS'AB
Short StoryAminan juna ne Hafsat da Hafsat wadan da suka kasance kuma masoya ga mutum daya wato Yarima Mus'ab yayin da a gefe daya kuma ga Zainaba masoyiya ga Prince din Hafsatus (Lol) wacce take ikirarin aurenshi ko ta wacce hanya tare da kudurin rabashi da k...