08

162 17 5
                                    

Shiryawa sukayi Lamido cikin atamfa riga da skirt ita kuma Hafsatou cikin doguwar Riga tayi rolling mayafin shi suka fito nan suka iskeshi har ya shirya cikin manyan kaya har da hula
     Wannan ne karonta na farko da ganin shi cikin shigar manyan kaya sai ta tsaya kawai tana kallon shi ba karamin kyau yayi mata ba shima idanu ya zuba mata duk da cewa ba wani kwalliya tayi ba amman tayi kyau sosae, Murmushi Hafsa tayi ganin irin kallon da suke yiwa Junan su sun manta a inda suke dan gyaran murya Ummi tayi da sauri Hafsat ta kauda kai yayin da shi kuma Mus'ab ya sauke ajiyar zucia tare da juyawa cike da kunya ganin Ummi ta kamashi yana kallon H³ ya nufi kofa yana fadin "Ummi sai mun dawo" tayi murmushi ganin yaki kallon ta "to Auta ku gaidasu Allah ya tsare" nan suma suka mata sallama tare da bin bayan shi.

Parking lot na bangaren Ummi suka nufa inda yake tsaye yana jiransu ya zuba hannuwa a aljihu yana kallon su duka biyun Allah kadai yasan abinda yake kissimawa cikin ranshi
  Driver ne ya matso kusa dashi tare da rusunawa cike da girmamawa domin ya hanasu durkusa masa yana fadin "Yallabai zamu fita ne?" Mus'ab ya murmusa "Eh Mlm Sule amman kayi zaman ka ba nisa zamuyi ba" gyada kai yayi tare da komawa wajen zamanshi yana fadin a dawo lafia
Wata Bakar mota ya nufa yana budewa H³ ta shige baya yayin da Lamido ta shiga gidan gaba ya tada motar suka fice daga fada suka nufi Gida Dubu gidan Aunty Maryama Wacce Mus'ab ke bi.
Sosai tsarin gidan ya burge H³ musamman yadda taga falon babu wasu tarkace very classic bayan sun zauna Mai aikinta Zubaida ta kawo musu ruwa tare da gaidasu Mus'ab yana tsokanar ta da cewa "a'a wai nikam Zuby har ynx kina nan to yaushe zamuje L/K musha bikin ne? Tayi dariya Aunty Maryama dake fitowa daga dakin ta ta furta "ai basai kunje LK ba da Dan gida za'ayi" ta karisa tana zama gefen H³ wacce ke kallon Yarima dake ta dariya ta lura yana da matukar saukin Kai fiye da tunanin ta sai Kara burgeta yake.
Gira ya daga wa Aunty yana jiran karin bayani tace "eh ai Mlm Sule direban Ummi ke sonta ai har yaje gida anyi magana" jinjina Kai yyi yana fadin "a gaskia na tayaki murna don Akwai shi da nutsuwa Allah yasa ayi damu" da gudu Zuby ta shige Kitchen suna mata dariya

Nan suka gaidata ta dafa kafadun H³ "Kawar  Little Kakus yau kinxo mana ziyara kenan" murmushi Hafsat tayi tana wasa da Kafar Yaron Aunty dake hannun ta Ajmal dake ta leqen fuskar ta yana  wangale baki ta mika masa hanu ya kuwa zo

Lamido ta ce "wai lallai Besty kin ciri tuta domin Ajmali ko ni bai yarda dani"

Maman shi tace "fadi gaskia dai Kakus kodai kina mishi mugunta ne" suka yi dariya nan suka cigaba da hiran su

Hafsat gwanar son yara tuni ta goya Ajmal suka shiga Kitchen taya Zuby aiki sai tsiya lamido take mata tana bada Lbrn lkcn da aka kawo Zuby bata iya komi ba sai kauyanci Hafsat sai dariya take..

Basu bar gidan Aunty ba sai wajen la'asar nan ma ba gida ya kaisu ba saida suka zaga gari sosai kafin suka iso gidan..

  Yau Ummi ce a bangaren Abbu  sbd haka ganin bata bangaren suka nufi site dinsa domin su gaidashi nan suka dan jima yana jansu da hirar makarantar su kafin da zaici abinci suka masa sallama suka koma bangaren Ummi duka su ukun nan suka fara kallo suna dan taba hira a tsakar falon yau Akayi serving abinci suka ci H³ kam ko cokali 5 batayi ba ta koma gefe sam ya lura bata son cin abinci da yawa

"Ke Blacky ance baki juriyar yunwa amman bakison cin abinci sam"

Tayi narai² da fuska "Yallabai ni ka daina cemin Blacky gaskia ko in fada ma Ammi na"

Zaro idanu yayi kamar Mai tsoro "yi hkr Baby abin bekai nan ba so kike Ammi ta hukunta ni"

"eh dai a daina kuma ai duk bakinmu daya naga"

Dariya suka yi ita dai Lamido kallon diramar su take suna sakata nishadi tana kuma kissimawa a ranta cewa rayuwa dasu shine cikar farin cikin ta

Ranar Saturday da safe suna bacci aka taada su wai su shirya su fito Yarima na jiransu a mota  babu musu sukayi yadda aka sanar dasu

YARIMA MUS'ABWhere stories live. Discover now