09

129 14 2
                                    

Tabbas tasan wannan fuskar haka take rayawa cikin ranta amman ta kasa tuna a ina ne nan dai ta koma a sanyaye ta zauna shima Yarima zama yayi a tsakar dakin suka gaisa tamkar sun san juna take tambayar shi mutan gida da aiyuka tare da masa godia.

Haka nan matar ta burgeshi yaji farat daya yana kaunarta sannan ynx ya gano inda Hafsat ta dauko Kyau sedai Ammi ta fita Haske itama tana da dimples kamar su daya da da Hafsat din

Kunun shima ya zuba yana sha domin duk basu karya ba suka taho suna dan taba hira bayan sun gama ne tace "Mami ki tashi ke da Hafsa ku shiga gidan Baffan ki Ku gaidasu

Hade fuska tayi domin sam ta tsani shiga gidan sbd abinda suke mata amman babu halin taki don babu musu tsakanin ta da Ammi wannan shine tarbiyyar da tayi musu

Yana lura da yadda take famar bata rai sai yabi bayansu yana fadin "Ammi bari nima in zaga Unguwar taku sbd nan gaba kar in manta hanya"

"To a dawo lafia" itama ta mike ta shiga kitchen don daura musu abincin rana

Jikin mota ya tsaya yana kallon su suka shiga wani gida nan kusa da nasu gidan

Da sallama dauke abakinsu suka shiga "Assalamu Alaikum" sun fada yakai sau uku kafin wata mace ta leqo daga daki tana fadin "wai waye ne da hantsin nan yake cika mana gida da kuwwa" ganin su Hafsa yasa ta wani cune fuska gata daman ba wani fasali ne da ita ba tamkar dai kawata Minauwal (Lol)

"Maman Fati ina kwana" Hafsat ta fada a dan dakile
 
"Eh lallai dole wato rashin kunyar da kika koyo kenan?"

Ita kam Hafsa ikon Allah take kallo daga shigowa taga an fara masifa ko sallamar su ba'a amsa ba

"Wai Lami kedawa kike ta hayaniya ne da safen nan" sukaji muryar namiji yana fada daga daki

"Yo nida 'yar wajen wancan tsintacciyar magen mana tazo tana min halin fitsarar da ta saba mana"
Da hanzari yaran gidan suka fito suna kallon su cike da wulakanci shima Baffan fitowa yayi

Da sauri suka durkusa suna gaidashi amman bai bi takan gaisuwar ba ya yamutse fuska "ke mai ya kawo ki gida naga ba hutu ake ba ko wani abin maganar kika jawo mana"

Ta girgiza Kai "a'a Baffa hutun Midterm ake kuma ma yau zamu koma"

"Oho sbd ga mai kudin banxa in banda rashin hnkali ki taso tun daga Bauchi zuwa nan kuma ki koma yau yaushe ma aka fara hakan naga baki taba zuwa hutun midterm ba" ya cigaba da masifa babuji ba gani

"A'a fa Baffa Malamin mu ne Yayan wannan ya kawo mu" tana nuna Hafsa

Gyada Kai yake kamar kadangare "Oh lallai iskanci kika koma da Malamai kenan ko?"

Tuni ta fara hawaye tana girgiza kai

"to tashi ki fice min a gida tambadaddiya ina dab da cireki cikin zuri'a ta"

Da sauri tayi hanyar waje tana zubar da hawaye tasan halin Baffa Auwalu amman batasan har zai fara mata zaton bin maza ba Hafsa sai bata hkr take domin ita abin ya daure mata Kai duk da cewa ba yau ta saba ganin kiyayya irin wannan ba don gidan Kakannin su haka suke musu

Yana hango fitowar su lkcn yana zaune cikin mota kafarshi a waje suna dab da karasowa kusa dashi sukaci karo da wani saurayi kana ganinsa kaga kalar 'yan kalare gashin nan babu kyan gani har sun gota shi ya dawo yasha gabansu

"Ke Mami Dan uwarki baki iya gaisuwa bane?" Ya fada yana wani ciccijewa

Murguda baki tayi "to ni yaushe na ganka"

Wani ashar ya maka "ke ni sa'an ubanki ne kk min rashin kunya" ya daga hannu da niyar Kai mata Mari sai yaji an rike hanunsa ta baya

"Haba Malam da girmanka dukan mace" Yarima ya fada yana kokarin danne bacin ransa

Abunka da kwarjinin Sarauta sai Kamalu ya kasa musa masa ya sauke hanu yayi tafiyar shi ganin kukan da takeyi ya janyo hanunta zuwa mota suka shiga Hafsa na biye dasu itama hawayen take
Hankali tashe yake tmbyr ta me ya faru  nan taci gaba da kukan da kyar ya lallashe ta suka shiga  gida daman Ammi tasan za'a rina bata ko tambayi dalili ba ta zuba musu jallop din taliya sukaci kafin yaje yayi sallar azahar

Kwanciya Hafsa tayi sai bacci suna ta hira Yayan ta ya dawo daga Shago da tsalle ta suka rungume juna tana fadin "I miss u Yaya Sadiq dina"

Murmushi yayi yana Jan hancin ta cike da farin ciki sosai hannu ya mika ma Yarima suka gaisa zasu kai sa'anni dashi yana cin abinci suna hira da ya gama yayi wanka Hafsat sai binshi take duk inda yasa kafa

Yarima yace "Blacky ki barshi mana ya huta"

Tace "yauwa Ammi ai kinga kullum haka yake cemin Blacky"

Tayi daria "ai kunfi kusa ke dashi"

Ya mata gwalo yana jan hanun Sadiq "Aboki na muje ka nuna min garin naku please"

Itama ta rike dayan hannun Sadiq tace "lallai ji wani wayau ka kwace min Ammi shima Yayan kwace min shi zakayi?"

"Kai habibty ai babu mai rabamu kawai yawo zan kaishi me kikeso in kawo miki"

Ta gane wayo yake son mata amman tayi shiru alaman tunani kafin tayi tsalle "Yaya Ice cream din Havila please ni da Besty"

"Au tare kuka zo?"

"Eh Yaya tana bacci a dakin Ammi na"

"Okay sai mun dawo maa gaisa da ita" inji Sadiq suka fita

Itama kwanciya tayi domin baccin..

#Ina ga kawai zamu koma amfani da Mami a madadinita kuma Lamido mu kira ta da Hafsa

#Smart ce.

YARIMA MUS'ABWhere stories live. Discover now