06

287 24 1
                                    

Kallon shi tayi a nutse bayan ya gama shan ruwan ta ajiye kofin a hankali ya fara magana "kina kallon abinda Ummi ta min ko Hafsatou, shin was take son in sanarwa damuwa ta bayan tun tasowa ta bata bani damar yin aboki ba da ita na saba sharing duk wata damuwa ta to ynx was take ganin zan nufa iye?" haka kawai yaji zuciyar shi ta aminta da ya fad'a mata matsalar shi ya lura tana da kaifin hankali duk da k'arancin shekarun ta da basu gaza 17 ba zuwa 18 ta runtse hanunshi dake cikin nata har saida ya d'anyi k'ara yana fad'in "Gaskia Blacky ke muguwa CE" gwalo ta mishi kafin ta had'e fuska ta fara magana "Yaya shin kana tunanin cewa Ummi bata damu da halin da kake ciki bane? Sam ba haka bane ita uwa da kk gani akwae wata k'aunar dake tsakanin ta da abinda ta haifa wanda ko yaya ya shiga damuwa takan shiga fiye da tashi,Ummi tayi hakane badon komi ba sai dan kasancewar duk yadda takai da son ka babu yadda za'ayi ta raba ka da Dangin mahaifin ka sbd idan aka wayi gari babu Abbah dole sune matsayin shi kuma kai kanka kasani cewa DA UBA AKE ADO wannan kalmar na dad'e ina jinta wajen Ammi nah tun tasowa ta kasan dai duk yadda Ummi ke son ka bazata je Masallaci da sunan kar'ba maka aure ba ko? So kuma ma ina laifin wanda ya d'auki d'iyar shi ya baka ai k'auna CE tasa hakan ko?"

Tun da ta fara magana ya zuba mata idanu tamkar talabijin yake kallon yadda bakin ta Ke motsawa tabbas yarinyar ta shayar dashi mamaki jin kalaman dake fitowa daga bakin ta tamkar shirya mata su akayi "Hakane hakika yau naci gyaran Malama bahaushe dake cewa Abinda Babba ya hango yaro baya hangowa tabbas ba kowane Babban bane domin ni sam banyi tunanin hakan ba gani nake kawai kowa ya tsane ni? daria tayi jin abinda ya fad'a " to amman Hafsatou kinsan fa halin harinyar nan sam batta da tarbiyya a 'yan kwanakin da nayi da dawowa na fahimci hakan tartare da ita kuma ina yawan jin Malamai suna k'orafi kanta a Schl" ita tasan hakan amman domin ta k'arfafa mashi guiwa tace "haba Sir Xieey fa mace ce sannan kuma yarinya k'arama kuma tana Son ka na tabbata bazaka sami matsala ba wajen tank'wara ta zuwa kalar da kk so ba" ta karisa maganar tana kallon cikin idon shi gyad'a kai yayi "shikenan Hafsatou ina yaro k'arami an maidani mai mata da yawa" ya fad'a yana dariya tashi tayi tana kallon agogon falon ta zaro ido "Sir har karfe goma fa tayi muna zaune oya a tashi dare yayi"

Hararan ta yayi ya tashi "to ai kene kika tsayar damu yarinya sai surutu kamar aku" ta murguda bakin ta "oho dai jeka daman ba'a muku kai da waccan matar taka mai bacci kamar kaasa" ta fad'a tana kashe kayan kallon
Yana fara tafiya "eh anji dai Blacky Parrot" ta watsa mai sauran ruwan da ta dauko a Kofi ta nufi Fridge dake dinning room ta aje ya fita da d'an gudun shi yana mata dariya......

Komai na wuta saida ta tabbatar ta kashe sannan ta rufe k'ofar falon ta nufi d'akin baccin su tana murmushi ita kad'ai

Ajiyar zuciya Ummi ta sauke wanda tun fara maganar su take tsaye tana kallon su kasancewar ta fito bayan shigarta d'aki domin yiwa Hafsatou magana ta kulle falo sosai yarinyar ta burgeta tana da kaifin hankali sosai da sanin ya kamata kuma taji dad'in yadda ta kwantar wa da Autan nata hankali nan ta juya ta koma d'aki hankali kwance......

YARIMA bayan shigar shi d'aki ya gama komai na al'adarshi kamar wanka,alwala ya sanya Pyjamas tare da fesa turare sannan ya kwanta yana mai jin farin ciki a zuciyar shi yayin da wani bangaren na zuciyar tashi tana d'aci in ya tuna wai shi zai auri mata biyu kuma duka babu za'bin shi? Tunawa da gargad'in Ummi na cewar yayi bacci yasa yayi addu'a tare da Jan bargo yana rayawa a ranshi cewar a wannan karon babu mai hana zuciyar shi abinda take so ko ya za'ayi kuwa........

Tana shiga d'akin tayi kwanciyar ta tana mai tunanin yanayin rayuwar YARIMA da ya kasance iri d'aya da tata duk kuwa da k'arancin shekarun ta amman ta experiencing abubuwa da dama a tun bayan rasuwar mahaifin ta lkcn tana k'arama amman ta kasance yarinya mai wayo sbd haka bata manta wasu abubuwan da suka faru da ita a haka bacci 'barawo yayi awun gaba da ita.........

Xieey tana shiga d'akin Mahaifin nata da hawaye ta fad'a jikin shi "Abbah ni wlh bazan iya ba sam YARIMA baya k'aunar ko gani na" ya shafa kanta "yi hkr Umman mu da yaddar Allah komai ya kusa zuwa k'arshe" nan ya sanar da ita yadda sukayi da YARIMAn duk da ta tsorita da jin cewar da Hafsat zai had'asu amman jin cewar ba sonta yake ba bashi ita akayi tad'an ji sanyi a gabanta kuma ya kira Mai martaba ya shaida mishi maganar kuma ya amince da haka ta mik'e ta nufi d'akin ta tad'au waya ta kira k'awar ta Saudah ta shaida mata yadda ake ciki nan ta kurma wani uban zagi tana fad'in "amman wannan uwar tashi akwae munafuka kar ki damu k'awata Indai Lamido ce zamu San yadda zamuyi da ita don bata da wani wayo daman 3ple H Ke kar'ba mata a Schl ammah in aka gama ai shikenan ko". Nan dai suka gama k'ulle²n su kafin sukayi sallama kowacce ta nufi makwancin ta.

To asuba ta gari mutan Masarautar Bauchi.............

#Team Mushaff
#Team Xieeysab
#Oneluv

Vote,Comments nd share mutane na ana kyawun tare.

YARIMA MUS'ABWhere stories live. Discover now