12

156 20 4
                                    

A daddafe Sadiq yayi kwana biyu domin a koyaushe yaga Hafsa sonta karuwa yake cikin zuciyarsa a haka dai ya daure har Schl ya rakasu da zasu koma ya kuma jaddada masu cewar suyi kokari yanason ganin result mai kyau ya musu sallama ya koma Gombe

Haka su Mami ke ta faman rubuta Exam Hafsa dai bata sake tada maganar Yarima ba sbd gudun fushin Bestyn ta har suka gama Jarrabawar Mami bata koma Gombe ba sbd kwana biyu aka saka Speech nd Prize giving day ranar kuwa har Ammi Sadiq ya dauko suka zo su Mami sunsha kwalliya taji dadi sosai ganin Ammin ta nan Ummy suka hadu da Ammi kowaccen su taji kaunar 'yar uwanta cikin ranta tashi daya wani abinda Sadiq ya lura dashi shine Ammi da Ummy da suka zauna waje daya yaga haka nan sun masa kama but bai kawo komai a ransa ba a haka aka gudanar da abubuwan a nutse ba hayaniya yayinda Hafsa da Mami suka karbi kyaututtuka da dama musamman ma ita Mamin domin ita ce Best student a shekarar

Bayan an tashi ne Ummy ta matsa wa Ammi cewar sedai su kwana gobe su wuce duk da cewar taso su koma a ranar amman haka dai ta hakura babu yadda zatayi a ranta tace Ina laifin me sonka

Sun sha hira sosai kamar wadan da suka san juna haka washegari aka rabu cikin kewa itama Ummy tayi alkawarin zata kai musu ziyara Gomben soon

Bayan sati biyu da yin Candyn su Mami Daddy wato Waxiri ya kira Yarima kan cewar sun gama magana da Abbansa nan da wata biyu za'ayi bikinsu shidai ya amsa da to sbd ynx baida matsala da auren Xee tunda zai sami muradin ranshi har yayi magana da Abba Sadiq ya tabbatar masa nan da Sati daya in sunyi magana da Mai martaba za'aje tambayo masa auren ta wajen Baffa Auwalu

Ya tashi zai fita a hanya suka hadu da Zee ta tsaya baiyi niyyar kulata ba yaji tace "sannu Yaya ina wuni?"

Dan dakatawa yayi ya juyo "lafia ya hutu"
"Alhamdulillah" ta amsa tare da shigewa falon Dad dinta
Bayanta yabi da kallo yana mamaki sbd tun lkcn da suke Exams ya lura da canzawa da tayi ko Staffs ma suna maganar ynx an daina yawan kai karanta duk da ba duka ta daina ba kuma ta daina yawan shigemai da takeyi gashi yau harda gaisuwa ya dan tabe baki yayi tafiyar sa zuwa wajen Ummy

Actually ita Zainab bawai wani halin banza ne da ita ba daman dai sangarta ce irin ta yaran masu kudi sai kuma rashin wayo wanda hakan yasa haduwarta da Sauda ya kara bata ta da rashin ganin girman na gaba

A kullum burin Umman ta shine ta kasance 'ya ta gari ko yaushe takan mata misali da Hafsa wanda hakan shi ya jawo tsanar Hafsan cikin zuciyarta kuma kawarta Sauda take zugata suke takura rayuwar ita Hafsan kasancewar ta shiru² bata kuma son hayaniya to sai bayan zuwan Mami lkcn suna JSS 3 kafin suka sarara mata don Mami akwai zafin rai da masifa wannan yasa suke tsoronta
Umma dai bata fasa yiwa Zainab fada ba akan hakan har sabani suke samu da Waxiri domin ko cikin Yayyenta Maza babu wanda ya isa ya tsawatar mata to a haka da Umma ta lura Zainab tana matukar son Yarima sai tayi amfani da hakan wajen nutsar da ita kullum tana nuna mata yadda yake kula da su Mami sbd suna da nutsuwa ba irinta ba da kuma cewar ta daina yawan shige masa tunda ya amsa cewar zai auretan to Alhamdulillah da alamu dai ta fara daukn maganar Umman

Mus'ab yayi waya da Sadiq cewar ya sanar da Ammi akwai me son Mami daga Bauchi kuma yana son ya turo a nemar masa auren ta amman sun kulla kada ya fada mata shine har sai yaxo din to itama bata wani ja ba tunda Bappa Auwalu ya takura tun dawowar Mami cewar sedai ta fidda miji ko ya aurar wa duk wanda yaga dama mutane sun dameshi ita ta gode wa Allah ma da ya basu dama baiyi radin kansa ba don haka da amince da batun Sadiq don ya tabbatar mata cewa sanda yayi bincike kuma ya amince da tarbiyyar yaron

YARIMA MUS'ABWhere stories live. Discover now