Da dare bayan sallar Isha'i suna kan cin abinci Jakadiya tayi sallama ta shigo bayan tayi gaisuwa take sanar da sak'on Waziri da ya aiko cewar yana neman YARIMA nan ya amsa mata cewa yana nan tafe bayan sun gama ne ya mik'e yana fad'in "Ummi bari inje amsa kiran Daddy" ta amsa da to ai gaida su ya kalle su "Kuzo Ku rakani daga nan kwa gaeda Umma" Hafsat ta mik'e yace "ke Blacky ke fah?" ta d'an marairaice kasancewar tana kallon Best Korean film d'inta Boys Over Flowers na mutumin nata (Kim hyun Joong) yayi gaba a dole ta mik'e suka d'auko mayafi tare da bin bayan shi suna tafe bayi na risinawa suna gaidasu har xuwa 'bangaren mahaifin Xieey wanda ya kasance Waxirin garin nasu a Babban falon gidan suka tarar da Umma da fara'ar ta ta kar'besu tana mai farincikin ganin su "sannun ku da shigowa maraba YARIMA" suka durk'usa har k'asa suna gaidata ta amsa cike da fara'a
Bayan sun gama gaisawa ne YARIMA ya nufi 'bangaren Waxiri yana fad'in su jira shi kai tsaye yayi sallama falon domin baya buk'atar iso matsayin shi na YARIMA Daddy ya amsa yana fad'in "YARIMA kariso mana Ashe kana tafe" YARIMA ya zauna a k'asa bisa kafet d'in dake falon ya tank'washe kafafu tare da fad'in "Barka da dare Daddy fatan an wuni lafia" ya amsa da "lafia lau d'an albarka ya mahaifiyar taka?" "Lafia lau take, daman ance ne kana nema nah" ya washe baki "eh daman naji ka dawo ne ban ganka ba shiyasa" murmushi YARIMA yayi "to shikenan bari in shiga chan nasan ynx Abbah ma yana duba hanya ta banje mun gaisa ba" Daddy ya d'an ja numfashi yana me shakkar maganar da zaiyi sannan yace "YARIMA maganar k'anwar ka nake son muyi" ya kalle shi "wacce k'anwa ta fa Daddy? Ko Hafsat" baiji dad'i ba amman ya daure yace "YARIMA k'anwar ka Zainab nake nufi ta wajena"
"Ohh! Daddy wani abin ne kuma ya faru da ita?"ya fad'a in I don't care voice Girgiza kai yayi "ko d'aya kawai gani nayi tunda ka k'are karatu ynx kuma sai maganar aure shine na yanke shawarar aura maka ita idan tayi Candy" wani Abu yaji ya soke shi a zuciya wai me ake shirin maida shine ya tambyi zuciar shi babu amsa sbd haka ya d'ago ya dubi k'anin mahaifin nashi yayi k'ok'arin dai²ta yanayin shi "ai Daddy anyi latti zuwa ynx Kam Dan har Ummi ta had'ani da d'iyar Yayan ta kuma ma mun daidaita" ran shi ya 'baci gaskia Halima tana shiga mishi al'amura watou har auren ma ita zata za'barwa d'an nata yayi murmushi ai in tasan wata to bata san wata ba "to in banda abinka YARIMA ai namiji mijin mace hud'u ne musamman kai dake gidan sarauta kaga ai kafi k'arfin zama da mace d'aya sbd haka kaje ka shirya auren mata biyu" bai bashi damar cewa wani abin ba ya mik'e zuwa Bedroom d'in shi mik'ewa YARIMA yayi ya fara tafia kamar wanda baida laka har zuwa Babban falon gidan inda ya tarar da su Hafsat zaune suna hira da Umma yana shigowa ta mik'e ta nufi 'bangaren maigidan nata daidai lokacin Xieey ta fito daga d'akinta zuwa falon ai ko tana hangoshi ta kariso da sauri da nufin rungume shi da sauri yaja baya tare da daka mata tsawa su Kansu sun razana da yanayin shi musamman Hafsatou wacce saida ta mik'e tsaye tana rarraba idanu ya iso kusa dasu baiyi magana ba illa hannuwan su da ya kamo ya fara jansu har suka fice daga 'bangaren Xieey dake tsaye kamar gunki ta fashe da kuka tare da nufar falon mahaifin ta.........A dai2 kofar falon Ummi ya sake su tare da nufar 'bangaren Mai martaba suka tsaya suna kallon shi har ya shige ciki kafin kowacce ta sauke ajiyar zuciya suka shige falon kowacce da abinda take sak'awa cikin tata zuciyar
Sallama yayi a falon Mai martaba aka bashi izinin shiga suna zaune da Mama (kishiyar Ummin shi) gaidasu yayi cike da girmamawa Abbah ya tambayeshi ya wajen service d'in nashi ya amsa da "Alhamdulillah komai yana tafiya dai2" sannan yayi shiru wayar Abbah CE tayi k'ara nan ya d'auka ganin k'anin shi ke kira nan sukayi magana take fara'arshi ta fad'ad'a ya sauke wayar yana murmushi "YARIMA ynx Daddyn Ku yake sanar dani maganar da kukayi ashe kuma mata biyu zakayi ne" gabanshi ya fad'i kar dai Abbah ya amince shima ko dayike yasan daman za'ayi hakan ai ya girgiza kai "a gaskia Abbah nawa nake da har za'ace nayi mata biyu lkc d'aya ai Sam bai dace ba" had'e fuska yayi "to to MUS'AB ka nuna min cewa bamu isa dakai ba kawai shikenan ina sane dakai cewar in har ba Halima bace tayi mgn Sam baka d'aukar ta da muhimmanci,to bari kaji baka isa kaja da maganar Dan uwana ba sbd haka umarni ne kasa a ranka auren mai sunan Hajiyarmu dole ne" tayi dariya cikin ranta yau dai ta had'o Dan gold da Abbahn shi (sunan da Matan gidan ke kiran Mus'ab kenan) "to in banda abin YARIMA ai gata akai maka....." Kallon da ya watsa mata ne yasa tayin shiru don yana da wani irin k'warjini "tashi ka bani wuri" cewar Abban nashi ya rusuna tare da fad'in "Allah ya huci zuciyar ka na barka lafia" ya fita duk yadda yaso danne damuwar shi ya kasa a dole ya nufi 'bangaren Ummi suna zaune da Hafsatou yayin da Hafsat tuni tashige bacci ya shigo direct wajen Ummi ya nufa ya zauna kusa da k'afar ta ya fara magana "Ummi meyasa ne ake min haka a gidan nan? tun tasowa ta kowa yake iko dani tamkar nine kad'ai 'Da ina ganin su Musa na gidan Daddy komi sukayi ba'a cewar komi sbd ni kad'ai ne ba'a so ko mi? Hatta karatu za'bar min Course d'in da akeso akayi kuma banyi musu ba haka nayi Amman har abin yakai cewar Matar aure ma sai an za'ba min? Shin an ta'ba tambaya ta ko akwae abinda nike so? Ko da wacce nake so?" Ya k'arishe maganar yana hawaye hak'ik'a ya bata tausayi amman ta daure tace "kenan YARIMA kana nufin don mun za'ba maka mata bamuyi dai² bane ko hakan yana nufin bamu sonka ne? Idan kuma kasan baka son Hafsat meysa ka amsa mana iye?" "Sam ni Ummi bazaki ta'ba bani wani Abu ink'i kar'ba ba koda banso balle ma ni ba Hafsat nake nufi ba Daddy ne ya kira ni wai sedai in auri Zainab kuma Abbah har ya amince" ya fad'a cikin d'acin zuciya
Ba Ummi ba hatta Hafsatou dake zaune nesa dasu tana kallon Playful Kiss sai da gaban ta ya fad'i tayi saurin kallon su akayi sa'a shima ya kallo inda take nan hankalin ta ya tashi ganin hawaye a idanun shi Ummi ta danne 'bacin ranta "to ynx ya kake son nayi iye? Ko inje ince su fasa ne sbd basu isa dakai ba, ni kaga ka tashi kaban guri mahaifin Kane duk abinda ya yanke a kanka ya zama lallai kabi" ta fad'a cikin daga murya tare da mik'ewa tana fad'in "sai da safe kuma kada ka sake tunani ya hana ka bacci kayi addu'a komai zaixo da sauke" ta shige d'akin baccin ta tana mai jin zafin abinda ake ma d'an nata.....
Sunkuyar da kai yayi k'asa ya rasa ma mai zaiyi ita da yake ganin zata share mishi hawaye amman Sam ashe ba haka bane itama tabi bayansu kenan to shi yanxu Yaya zaiyi kenan
Ganin k'afafunta yayi masu kyau a gabanshi ya d'ago har izuwa fuskar ta tana tsaye ta zuba mishi idanu ya janyo hanunta tare da zaunar da ita a gabanshi yana jin inama ace matar shi CE da ya rungumeta ya fad'a mata damuwar shi ya raya hakan a ranshi har ynx hanunta na cikin nashi yake kallon ta kallo irin na ido cikin ido suke wa juna tana hango wani irin rauni cikin idon shi....... Tashi tayi tana k'ok'arin zare hanunta dake cikin nashi ya rik'e gam a hankali tace "Yi hkr Yaya ynx zan xo" don ta lura yau Malamin nasu rikici yakeyi ya sake ta ruwa mai sanyi ta d'auko ta zuba a kofi ta mik'a mishi bai karba ba sai ya bude baki tayi murmushi ta saka mishi kofin yasha ruwan.....................
YOU ARE READING
YARIMA MUS'AB
Short StoryAminan juna ne Hafsat da Hafsat wadan da suka kasance kuma masoya ga mutum daya wato Yarima Mus'ab yayin da a gefe daya kuma ga Zainaba masoyiya ga Prince din Hafsatus (Lol) wacce take ikirarin aurenshi ko ta wacce hanya tare da kudurin rabashi da k...